DALILIN KUDIN HAYA...
Ana qoqarin rufe gidanshi saboda bai samu kudin haya ya biya ba...Sai ya nemi bashin kudi a hannun manajan kamfanin da yake aiki bai samu ba... Ya tuntubi attajirin unguwarsu nan ma bai samu ba... Sannan ya kira yan uwanshi a waya nan din ma bai dace ba...
Sai yayi post a facebook wall dinshi yana neman taimako, amma iyaka abin da ya samu shine: 2likes da kuma 0 comments ...
Sai ya tura messages guda 120 zuwa ga abokanshi da suke contact list dinshi yana neman su rantamar dubu 50... Abin haushi mutane 10 ne kawai suka yi reply na message din... 6 daga cikin 10 suma suka ce basu da abin da zasu bashi.. Mutum daya daga cikin 4 ne kawai ya bashi dubu 5 amma sauran sai uzuri suke badawa qarshe ma suka daina daukar wayarshi...
A hankali har lokaci yayi maigidan haya ya kulle gidan, Ya bar iyalinshi a kofar gidan tare da tarkacen kayansu... Ya shiga lungu da sako bai samu tallafi ba har dare yayi... Yana tafiya a cikin duhu yana neman mafita sai ga babbar mota ta bi ta kanshi nan take ya mutu...
Washegari sai labarin ya cika gari da labarin mutuwar shi... Facebook friends dinshi mutane dubu 2220 su kayi posting a wall dinshi suna jimamin mutuwar shi tare da fadin kyawawan halayenshi...
Maigidan hanyar da ya samu labari da gudu ya zo ya budewa iyalinshi gidan yace su shiga ciki domin amsar ta'aziyya...
Attajirin unguwarsu wanda ya hanashi bashin kudi Shima ya kwaso kayan abinci da kudin cefene ya ba iyalin mamacin yace a dafa domin baqi masu zuwa...
Daga bisani sai aka fara shirye-shiryen binneshi... Inda anan take kwamiti na abokanshi suka tara kudi har N1,200,000 ta hanyar karo-karo... Domin ciyar da bakin da zasu zo daga wajaje daban-daban...
'Yan uwanshi na nesa da na kusa wadanda ya bugawa waya lokacin da yake neman taimako suma suka zo da nasu gudunmuwar ta kudi mai yawa...
Abokan wajen aikinshi suma suka tara kudi har N300,000 domin kar6ar rumfuna da kujeru da kuma sauran abubuwa...
TO WAI DUK MENENE WANNAN DIN? Me yasa ba zaku taimaki mutum a lokacin da yake tsananin buqatar taimako ba har sai mai kasancewa ta kasance? Me yasa ba zaku taimaki mutum dan lada ba sai dan mutane su fito su yabeku??
Me yasa kuke son yabon mutane akan yabon Allah da mala'ikun rahma? Me yasa ba zaku yi maganin matsala ba tun kafin ta girma?
Haka musulunci yace ko haka 'yan uwantaka da zaman tare suka ce?
Saboda irin wannan mugun halin namu mutane har nawa suka rasa ransu? Mata nawa suka zama zawarawa...' Ya'ya nawa ne suka zama marayu? 'Yan mata nawa suka zama karuwai? Mutanen kirki nawa suka fada ga halaka?
Matasa nawa suka zama barayi da masu fashi da makami? Mutane nawa suka zama mabarata?
WALLAHI IDAN ZAMU CENZA TO MU CENZA TUN KAFIN ALLAH YA YI FUSHI DA MU....
YA ALLAH KA TAIMAKI BAYINKA WADANDA SUKE CIKIN IRIN WANNAN HALIN 🙏😢🙏