HUKUNCI MURNAR SABUWAR SHEKARA

HUKUNCI MURNAR SABUWAR SHEKARA


 *Shehin Malami Abdul Aziz Ibn Abdullah ibn Baz Allah ya jikansa da rahma yana cewa:*

Baya halatta ga Musulmi ko Musulma suyi tarayya da Kiristoci ko Yahudawa cikin bukukuwan su, hakan wajibi ne su bar shi baki daya domin duk Wanda yayi kamanceceniya da wasu mutane to yana daga cikin su (ranar kiyama za'a tashe su tare). Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata agareshi yayi mana gargadi wajen kama dasu da kuma dabi'antuwa da halayen su.

Wajibi ne akan Mumini da Mumina su gargadu daga aikata haka, kada kuma su taimaka da wani abu wajen aiwatar da haka saboda bukukuwa ne da suka sa6awa shari'ar Allah masu kuma aikata su maqiya Allah ne, dan haka baya hallata tarayya dasu wajen gudanar da irin wadannan bukukuwa, ko taimakon wasu yi ko taimaka musu da wani abu na shan Shayi ko lemo ko kuma wani abu na kyaututtaka ko abinda yayi kama da haka, Allah ta'ala yana cewa cikin Qur'ani mai girma: 

" *Ku taimaka wajen yiwa Allah da'a da jin tsoron sa kada Ku taimaka wajen sa6on Allah da Ta'adanci"* 

Saboda haka tarayya da wadanda ba musulmai ba cikin bukukuwan su yana daga cikin taimako akan sa6on Allah da Ta'addanci.

Daga cikin Fatawowi da Maqaloli: 6/405.

Fassarar Dan uwanku a Musulunci: 
 Shuaib Nura Adam
24-4-1440/1-1-2019
Post a Comment (0)