UKU-BALA'I 11

UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
​​WÉ› ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucÉ‘tÉ›, MѳtiѵɑtÉ› ɑɳɗ ɛɳtɛʀtÉ‘iɳ ѳuÊ€ ʀɛɑɗɛʀร​.
BABI NA GOMA SHA DAYA.
Sosai yake kaiwa da komowa cikin dakinsa, hannayensa sarke a kirjinsa, lokaci-lokaci ya kan ja tsaki kamar harshensa zai tsine. duk sanyin da A-C din dake dakin take bayarwa hakan bai hana gumi samon mazauni saman goshin sa ba.
Sosai ya cigaba da zarya a dakin cikin rashin mafita akan abin da ya addabi zuciyarsa sosai yake jin zafi da raÉ—aÉ—i a zuciyarsa da ruhinsa sosai ya ji komai da ya faru dashi kwanakin baya sun hanashi sukuni ya naji a ransa bai taba ganin 'ya mace da ta raina masa hankali ta ci masa mutunci kamar wannan kankanuwar Æ´arinyar wanda ko a zaben mata aka saka ta ba in da zata kai labari kwaila ma irin ta wacce sam bata san Darajar da mace ke da ita a wannan duniyar rayuwar ba ta yanzu ba amma har ta dubi tsabar idon sa ta gaya masa haka.
"Noo Impossible".
Abinda ya fadi kenan cikin daga murya mai sauti yana faman kai wa kirjinsa naushi kamar a nan mai laifin take.
Kamar wanda aka tsikara haka ya zari Key din Motarsa ya fara tafiya cikin sassarfa kamar zai tashi sama a haka har yafice daga cikin dakin sosai yake taka benen da zai kai shi zuwa kasa sashin babban falon cikin gidan kallo daya zaka yi fuskarsa ka fahimci halin da yake ciki na kunar rai sosai yake zakar wani abu a ransa wanda yake da tabbacin shi kadaine mafita gareshi dole ya dauki mataki dole ya dan hukuncin da zai dauka dole ya nuna mata tayi kadan ba kowan kowa bace a cikin jerin mata ba ta kai Level din da zata raina shi ba ba ta kai matakin 'ya mace da zai kalla har ya yaba ta raina masa hankali ba da wannan sakar zucci har ya fice daga sashin cikin gida ya doshi Mota Parkig ya fara kokarin fiddo da motarsa komai yake yin sa a hanzarce haka ya figi motar mai gadi na ganinsa ya doso shi da sauri ya mike ya nufi Get din ya bude sosai yake kallon fuskar Huzaif yanayin da ya ganta sai da gabanda ya fadi sosai.
"Allah Yakyauta".
Abin da ya fadi kenan yana margaya kai ya mai da Get ya rufe bayan Huzaif ya fice.
Sosai yake gudu kan titi zuciyarsa na faman wassafo masa abubuwa ma bambanta sosai yake jin komai na zuwa masa a bazata wanda ya hakikance ba wanda ya assasa hakan sai wacce kwailar yarinÆ´ar wacce ko kyautarta aka bashi ba abin da za tayi masa a rayuwarsa illah wahala.
Cikin mintin nan da ba su haura talatin ba ya isa Kofar Asbitin baban alis sosai yake kallon asibitin bayan yayi parking ya fito yana mai wasa da Key din motartashi gaban motar ya usa ya yi tsalle ya hau gabanta ya zauna gami da harɗe hannayensa duk biyu a kirji ya kure kofar asibitin da kallo yana tunanin abin yi domin shi dai zuciyarsa ce ta kawo sa amma bai san takamaiman abin da zai gudanar ba abubuwa biyu suke masa sukuwa da tunanin sa haushin Mariya da kuma son ganinta wanda duk ya ajje a hurumi daya wanda sam ba su da alaƙa da juna numfasawa yayi gami da zaro wayarsa daga aljihu yana shuga dandannawa kamar mai kokarin kira kamar wanda ya ga takaici sai kuma ya ja tsaki gami da maida wayar aljihunsa yana faman sakin numfashi.
*****
"na rasa me zan yi komai ya kwance mani".
Abinda ta fadi kenan tana tura laɓɓanta cikin bakinta tana faman ya mutsa fuska kamar wacce aka sanya shan magani.
Sosai yake kallonta da yanayin da take ciki na yanayin rashin kwanciyar hankali komai ya bayyana a fuskarsa na tsananin damuwa har zurmawa tayi kamar wacce ta tashi daga gudawa.
"na rasa ta ina zan miki bayani ki fahimta, na rasa mai zance miki wanda zai ganar dake komai da komai kin kasa daukar abin da nake fada miki, ya zan yi dake Mariya?".
gyaÉ—a kai kawai take yi tana faman dauke kwallar da taji suna kawo mata farmaki.
"Hakuri Dr.Aqeel. bani da komai da zai taimaka min domin samun natsuwa ta ka tuna yau kwanansa Biyar ban gan sa ba, yau kwanan sa biyar ban san a wani hali yake ba, dole dole ne na damu sosai da sosai zuciyata taki hakuri taki natsuwa".
Ta karashe cikin karfin hali kamar mai som fashewa da kuka kai ta cigaba da gyaÉ—awa.
"ban san abin da yasa yaki jin magana ta ba, ban san abin da yasa bai yi amfani da abin da nace ba komai da komai Dr.Karami yace zai amma yaki yarda da hakan".
Ya fadi yana kallon Mariya wacce gabadaya hankalin ta na wajan Habeeba wacce take sharar barcin ta hankali kwance kamar bata da wata matsala a duniyarta mai da kai tayi wajan Mu'azzam wanda shi barci yake yi. sosai take jin tausayin sa na damunta a rai sosai take tausayawa rayuwarsa.
Mikewa tayi ba tare da ta dubi Dr.Aqeel ba ta fara tafiya sannu hankali sai ka rantse rashin jini ne ke damunta.
"Uhmm nace ba".
Ya fadi yana mai kallonta cak! tsaya ba tare da ta juyo ba.
"ina zaki kuma?".
"waje zan fita".
ta bashi amsa tare da kara saurin tafiyarta don ba ta so ta sake furta ko da kalma daya ne gareshi
So take ta je waje ko za ta samu sa'ida a zuciyara ba wai ta yarda dari bisa dari bane a,a kawai dai zaman dakin ne ya fara gunduranta dalilin Dr.Aqeel ba ta son a daidai wannan lokacin ace maganar wani na ratsa mata kunnuwa tana bukatar natsuwa ko yaya ne amma ta lura Dr.Aqeel ba zai bata wannan damar ba sam! Ba ta san me yake nufi da ita ba ta rasa ina zata sa kanka ko yaya ne ta samu hutun rai da ruhi.
"MACE ƘYANƘYAWA".
Sautin muryaar da taji ne ya sanya ta katse tunanin da ta afka sosai gabanta taji ya bugu har sai da ta sanya hannu ta dafe tana ambaton 'innalillahi wa'inna ilaihir raji'un'
Sosai ta fiddo da idanuwanta waje tana mai sauke so akan sa sosai taji komai yana kwance mata cikin kwakwalwarta.
Gabadaya idanuwansu suka sarƙe sosai suke ƙallon junansu an rasa mai dauke kallonsa daga dan'uwansa fuskar Huzaif ba abin da take saki sai murmushi sabanin ta Mariya da take a cungune waje daya kamar wacce aka aikowa da mutuwar wani cikin dangi
A hankali ya fara kokarin saukowa daga kan motar shi yana faman sakin murmushi wanda daka gan shi kasan akwai alamun tambaya akan sa.
Sosai yake tunkaro ta gabanta na sake tsananta faduwa komai take ji na kanta na wargaje mata ba abin da zuciyarta keyi sai É—aci sosai.
Ba ta son ganinsa, bata muradin ganinsa cikin duniyar rayuwarta, ylta tsani shi a zuciyarta tun daga kalaman sa take jin wani irin É—aci tun daga kasar ruhinta a dalilinsa sai dai wani bangare na zuciyarta sam yaki kin yarda da Huzaif domin kullum cikin tono mata sunan yake.
"Yaa Allah!".
Ta fadi tana mai haɗe laɓɓanta waje tana cusa su cikin bakinta a hankali take daura hakoranta akai tana dannawa kanta a kasa tana jin saukar numfashin Huzaif kusa da ita hakan yakara tsinka mata zuciya ji take kamar ta kurma ihu don haushi.
"wai ke mai yasa kullum in za a ganki, sai an ganki tare da kunci ne?".
Ya fadi yana kallonta sosai yana kallon yanayin Emotion dinta da ya sauya lokaci guda yana kallon yarda fuskarta ke wanzar da haushi da ƙi kuma ya tabbata akan sa ne Murmushi ya saki ganin tana kokarin barin wajan ya kai hannu ya riko mata nata hannu.
Ai ji tayi kamar an daura mata garwashin wuta a hannun nata nan da nan jikinta ya dau wani irin Shock har sai da komai ya motsa a jikinta da sauri ta dago kanta sosai take kallon Huzaif da rinannun idanuwanta ji take kamar ta tsinke shi da mari don takaci da bakin ciki bakin tane ya fara motsi alamun son magana laɓɓanta dake cikin bakinta har wannan lokaci ta shiga motsa su.
"Don Allah ka rabu dani!".
Ta fadi cikin murya mai sauti da karamar tsawa a cikinta tana mai dauke kallonta daga gareshi bayan ta watsa masa wani mugun kallo.
Sosai yake mamakin yar mitsilar yarinyar nan, da yarda take yin komai nata cikin rashin tsoro ko fargabar abin da zai je ya dawo ya lura akwai tsoro a zuciyarta sai dai bata barinsa yayi tasiri a zahirinta ba.
A hankali ya saki hannunta da ya rike gami da jan guntun tsaki mara sauti amma hakan bai hana Mariya ji ba ko kallonsa ba tayi ba amma ta lura yaji haushin abin da tayi masa gyaÉ—a kai tayi ta fara hanzarin barin wajan amma maganarsa ce ta sanya ta saurin tsayawa.
"mai yasa baki son mai sonki da alheri, na lura wani naki ne bashi da lafiya amma kin ki bani damar da zan samu ikon duba shi, ko da yake ban san abin da kike tunani akai na ba ni dai ban dauke ki na ajje a zuciyata ba akan wani mugun nufi sai dai na ajje ki a zuciya a dalilin tausayinki da jin kai".
Sosai maganganunsa suka shiga shigarta ta ko ina sosai take jin sautinsu na haifar mata da wasu lamura a kasar zuciyarta sosai take jin tasirinsu a kasar ruhinta sosai zuciyarta ta fara kokarin gasgatawa tunaninta ya karbi lamarin a saukake sosai take ajje numfashi a duk wani kalma daya da ya furta a hankali ta fara kokarin kallonsa idanuwanta a dan tsuke bata bari tasirin maganganunsa sun fito zahiri ba ta fara motsa laɓɓanta.
"bana tsammanin zan yarda waki bugun ya sake gintawa a tsakaninmu kasan ance dukan farko shine duka kuma ka lalata damar ka tun a karo na farko don haka ina mai rokan ka ka fice mani daga rayuwa bana so komai ya faru tsakanina da kai kaji ko kawai ka kama gabanka kowa yayi rayuwarsa ba abin da ya hada kifi da kaska balle kuma har su da zauna inuwa daya".
yanayin yarda ta ajje furucinta cikin halin-ko-in-kula yayi matukar kara zafin zuciya gareshi sosai yake kallonta yana jin rashin wayon da ya nuna akanta har ya tsaya yar yarinyar nan na fada masa abin da ta so a ranta tsaki yaja sam bai lura ta wuce ba sai da ya fara motsa baki yana son yin magana sannan ya lura bata wajan naushi ya kai sa iska gami da cizon Laɓɓa sosai ya ke kallon kofar aasibitin domin ya hango shigarta sosai zuciyarsa take shiga kunci a hankali yana mamakin yarda akayi yake wahalar da kansa akan wannan halintar wanda ko a farkinsa ban yi zaton zai ganta har ta samu damar shiga rayuwarsa ba dole ya san abin yi dole ya dau mataki akanta domin tsana yake hangowa tasa a idanunta ya tabbata ta tsanshi haushi sa take ji a ranta har a bayyane a fuskarta.
"l'm Huzaif!".
Ya fadi yana nuna kansa da dan yatsansa yana mai sakin murmushi gami da gyaÉ—a kai ya juya ya koma motarsa da gudu ya fuzge ta ya bar harabar asibitin.
*****
Sosai Dr.Karami yake aikinsa cikin kwanciyar hankali da kware a harkar cikin kwanaki talatin da biyar komai ya fara kamo hanyar samun waraka ga Habeeba ba wai Mariya kadai ba hanta su Dr.Aqeel sunyi matukar yin farinciki da hakan domin sosai suke ganin komai na zama Normal izuwa wannan lokaci Habeeba ta fara samu sauki sosai don yanzu duk na fizge fizge da rashin magana ya kau sai da lokaci-lokaci in kana hira da ita tana kau ce hanya cikin hirar zaka ji tana wani zance na daban wanda bashi kuke yi ba hakan ya so damunsu Mariya sai dai Dr.Karami yana kwantar musu da hankali gami da sanar da su dole hakan sai ta faru gareta a hankali komai zai daidaita kamar bata tabayin cutar ba.
Kamar ko yaushe yau mariya ce zaune ita da Dr.Karami suna hira domin shakuwa ce ta shiga tsakaninsu sosai da sosai Mariya tana matukar girmamashi gami da kunyarsa hakan yasanya Dr.Karami yake jinta a ransa sosai take burgeshi komai nata yanayi masa musamman da ya lura tana da hankali gami da natsuwa sosi a rayuwarta gata da gamun kai.
Dr.Karami ya numfasa bayan ya gama wayar da yake yi ya dubi Mariya da take ta faman wasa da Mu'azzam dake hannunta shikuma yana faman ƙyalkyala dariya.
Murmushi yayi yana gyaɗa kai kafin ya motsa laɓɓansa.
"Na lura sosai da sosai ki ke son Mu'azzam, anya za ki iya rabu dashi kuwa in wani abu ya taso na zuwa wani waje".
Kasa tayi da kai alamun jin kunya sosai ya kureta da ido.
"kin fiye kunya Mariya anya kuwa".
ya sake fadi yana dariya.
A hankali ta dago kanta ta kalle shi sannan ta ajje kallonta gefe.
"Uhmm Dan'uwana sosai nake son sa ban son rabu dashi ko na sakanne".
"kenan yanzu ko lokacin aurenki yayi ba zaki iya rabu dashi ba a matsayin ki na 'ya mace yar gidan wani".
Ji tayi kamar ta tsune kasa don kunya dalilin aure da ya ambata gabadaya sai ta rikece sai motsu motsu take yi ta rasa abin yi gabadaya.
"wai shin ina zancen makarantarki ya kwana ya kamata ace kin koma makaranta Mariya zaman haka ba zai haifar miki da É—a mai ido ba ke 'ya mace ce sosai karatu ke da muhimmanci a rayuwarki ya kamata ace kin mai da hankali sosai zuwa ga karatun ki ita ce dama daya jal da kike da ita ko don taimakawa iyayenki wata rana kece babba ko da dai ke yar gidan wani ne amma duk da hakan kiyi karatu".
Sosai kalamansa suke samun masauki a zuciyarta sosai take jin dadin yanayin furucinsa cikin sanyin murya mai cike da karfafawa zata so ace hakan ta kasance gareta zata so ace ta samu wannan damar za ta so ace tayi karatu na sosai da sosai domin ta lura karatu a rayuwar zamanin nan yana da muhimmanci sosai musamman 'ya mace ko ba don komai wasu abubuwan na rayuwa da suke gudana a duniyar nan ya kamata ace mata suna samun wannan damar domin wasu fannonin 'YA'YA MATA ya kamata ace a wajan ba maza ba musamman harkar likitanci ko ba komai taimako ne na al'umma ku hakan zai wuce takaicin da wasu ke yi wa mara hali a rayuwarsu.
Sosai take jin tausayin kanta da na iyayenta da kaninta Mu'azzam ta sani ƙaddara ta fado rayuwarsu gami da talauci da ya hana su gudanar da wasu abubuwa sosai da ya kamata ace sunayin sa ba wai rayuwar jindadin duniya take nufi ba a,a wasu abubuwan a rayuwar dangin rai dole yayi a karan kansa ba wai sai ya tsaya wani yayi masa ba musamman duniyar zamanin nan a yanzu in baka dashi ba mai yi da kai balle ya ya jikanka ta sani a duniyar nan in baka dashi kai da banza duk daya ne ta gani an aikaice akan ta anyi mata.
Hawayen da suka zubo mata ne ta sanya hannu ta dauke su sosai take gyaɗa kai ta na son yin magana amma ji tayi wani abu mai nauyi ya saukar mata a kirhi sosai take jin komai na rashin dadi na wanzuwa a gareta sosai take tuno rayuwar da tayi a makaranta da irin yarda ake korota dalilin rashin kuɗi sosai take tuno yarda ake mata gori a makaranta kowa ya gujeta ba ta da kawa ko daya domin ta fita zakka a cikin yaran makaranta kullum cikin rashin babu take ba ta ga watan da zai ya kare ba a ƙore ta ba ta ranar da zata zo har ta fadi ba a tuhume ta da rashin babu ba akan wani abun bukata a makaranta.
Kasa tayi da kai sosai take jin kuncin rayuwar da take yi sosai take hango ƙaddarar da take da wainiya da rayuwarta ita da ahalinta.
"Mariya!".
Sautin muryar Dr.Karami ta sauka cikin kunnuwanta wanda gabadaya ta mance ma da wanzuwan sa a wajan a dan razane ta dago da koÉ—aÉ—É—un idanuwanta ta sauke akan sa.
"karki ce da ni ba ki son karatu, karki ce dani maganar da nayi miki ne ta sanya ki kuka".
Kai ta shiga girgizawa sosai hawaye da sauka a kuncinta a hankali tashiga motsa laɓɓanta.
"ko daya ba ruwanka komai naka gaskiya ne mai kyau ne sai dai...".
Shiru tayi gami da yin kasa da kai sosai ya kafe da ido don ya gama fahimtar inda ta dosa da batun nata amma nauyi ya hanata fadi tausayinta sosai yake ji komai nata na rayuwa yake tausayawa.
"Karki damu Mariya nayi miki Alkawari...".
"Dr.Karami".
Sautin Muryar Dr.Aqeel ne ta katse masa maganarsa tsaye yake ya harÉ—e hannu a kirjisa fuskarsa kadaran kadahan gabadaya ke kallonsu sosai yake son fahimtar abin da zuciyarsa take sanar dashi sosai yake kallon yarda Mariya take kuka wanda sam bai da sauti sai na hawaye sosai ya fara jin wani iri a kasar ruhinsa da zuciya zargin Dr.Karami yake da shiga rayuwar Mariya ya kunsa mata wani abun wanda yasanya shiga damuwa sosai.
"na lura cikin yan kwanakin nan wani lamari ne yake tsakaninka da Mariya, in dai har za ku zauna tare bana taba ganinta ta tashi da dadin rai".
gabadayan su suka dubi Dr.Aqeel wanda shi kansa sai da ya tsargu sosai akan maganar da yayi duk sai yayi wani zuru zuru dashi yana faman yake.
Dr.Karami yayi murmushi domin ya rasa ina zai ajje zancen Dr.Aqeel bai fahimci in da ya saka gaba ba gabadaya tunaninsa ya tsaya akan zarginsa yake yi kenan da kuntata rayuwar Mariya? girgiza kai yayi kafin ya fara duban Mariya sannan ya dubi Dr.Aqeel.
"ce maka tayi ina takura mata hala?".
Sosai Dr.Aqeel yake nuna nadamarsa akan abin da yace ya san tabbas maganar da yayi ba ta da hurumin da za a ajjeta sosai ya shiga girgiza kai yana faman ajje yake kamar wanda aka baiea kyautar bazawara.
"Noo ba haka nake nufi ba".
Sosai su duka biyun suka kureshi da ita musamman Dr.Karami da ya fara hasaso wani abu da zuciyarsa ke sanar dashi amma yaki yarda da hakan mikewa yayi a hankali yana mai duban Mariya.
"ni zan tafi sai gobe kuma ki kula da kan ki sosai".
GyaÉ—a kai kawai tayi alamun amsawa sai dai har ga Allah bata so tafiyarsa ba har a ranta tana jin dadin zama dashi amma ta lura Dr.Aqeel yana yi mata kanzagi akan hakan kamar ba ya so zaman da suke yi a tare tashi tayi tana duban Dr.Karami da yake yiwa Dr.Aqeel Sallama.
"Nagode sosai gobe Allah ya kiyaye hanya ya tsare".
ta na gama fadin haka ta gyarawa Mu'azzam kwanciya a kafadatar ta yi hanyar dakin da Ummanta take tana faman saka da warwara akan Dr.Aqeel gabadaya ta lura dashi ya fiye takura sosai duk da dai shi mai ALHERI ne amma wani lokacin abin da yake yi sam bai dace ba ya kamata ya san wani abu guda ba kowa ne zai iya daukar irin halin da yake nuna wa wanda zai san shi ba sai yaga kamar tsana ce kawai ko da ita a karan kanta ta fara dasa ayar tambaya akansa mafiya yawan lokaci in dai suna tare da Dr.Karami yana yi mata wasu abubuwa kamar natsana ita da Dr.Karami din ta rasa in ya dosa ta rasa menene nufin sa da hakan din.
Tsaki ta ja kamar harshenta zai tsinke ta karasa shiga dakin kwance ta sameta tana barci samun waje tayi ta zauna izuwa lokacin Mu'azzamn barci ya fara tafiya dashi sosai tashi tayi ta shimfiÉ—ar dashi ta sannan ta samu gu ta zauna ta zabga tagumi ta fada duniyar tunanin mahaifinta wamda ba ta san a wani hali yake ba cikin duniyar rayuwarsa tun fitarsa kwanakin baya da yayi har yau ba alamun sa ta rasa ina ya tafi ta rasa mai yasa mahaifinta yayi mata haka ta ba so yayi misa da ita a kowani hali suka tsinci kansu tasani rashin abubuwa yana taka muhimmiyar rawa a duniyar rayuwarsu sai dai ba yarda za suyi ta sani rashin babu ne yasanya mahaifinta fita amma bai dace ace tsayin wannan kwanakin ba asan a inda yake ba har gida taje amma ta sami labarinsa ba sai ma rashin mutunci da Goggo Marka ta aikata mata da kuka ta baro gidan.
Sosai take jin faduwar gaba game da mahaifinta duk lokacin da take tunanin sa komai take ji bai mata dadi a rai ta rasa mai za tayi ta rasa mai ya dace tayi sosai kwakwalwarta ke caji wanda ita kanta ta san tunanin da take sanyawa kanta ya fi karfin kanta sai dai bata san mai za tayi ba komai a cakuÉ—e yake cikin duniyar rayuwarta.



Post a Comment (0)