UKU-BALA'I 12

UKU-BALA'I

NA

KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


​​WÉ› ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucÉ‘tÉ›, MѳtiѵɑtÉ› ɑɳɗ ɛɳtɛʀtÉ‘iɳ ѳuÊ€ ʀɛɑɗɛʀร​.


BABI NA GOMA SHA BIYU.

Sosai idanuwansa suka kaÉ—a sukayi jajir kamar wanda aka watsawa garwashin wuta. Sosai yake jin wani zafi da zugi a kasar zuciyarsa sosai da sosai kirjinsa yana wani irin bugawa kamar zai rabe gida biyu numfashi yake ajje wa lokaci-lokaci mai tsananin zafi da zugi.
Shisha din dake girke a tsakanin kafafuwansa ya zubawa ido sosai kamar wanda yake son fahimtar wani abu game da ita a hankali ya kamo yar igiyar da ake amfani da ita ya kai bakinsa ya zuga tsayin sakanni talatin kafin ya zare daga bakinsa gami da sakin wani hayaki wanda ya turke masa fuska gabadaya ya kasance ba ka hango kansa ma sosai hayakin yake tuntulowa daga bakinsa da hancinsa sai da hayakin ya debi lokaci kafin ya tsagaita da tuntulowa sosai idanuwansa suka kaÉ—a har da yar guntuwar kwalla kwance a ciki.
GyaÉ—a kai yake faman yi ba abin da yake yi masa shawagi a duniyar tunaninsa da zuciyarsa sai wani lamari da ya kasa gasgata shi ya rasa a ina zai ajje shi domin samun saukin raÉ—aÉ—in zuciya dana ruhi sosai yake jin nauyi a kirjinsa sosai komai ke kwance masa na tunani sosai yake jin abubuwan da suke addabarsa suna amsa kuwwa gami da sauti a kunnuwansa kirjinsa yake ji yana kara nauyi sosai numfashi ma dakyar yake samun ajjeshi.
A hankali ys ajje igiyar shisha din ya fara yinkurin mikewa wani irin nauyin kirji ya sake tokareshi daga hanzarin da ya so amfani dashi da sauri ya koma ya zauna ya na mai sakin numfashi da sauri-sauri kamar wanda aka sanyawa Oxgyen sosai yake jin bacin rai in ya tuna kalma guda da yanayin da take furtata akansa sosai yake jin É—aci a ruhinsa akan duk kan wata kalma da ta fito daga bakinta sosai yake jin zafin tsakin da tayi masa a daidai wannan lokaci.
Mai yasa... Mai yasa mai dauki mataki tun a waccan lokacin ba, mai yasa ya bari damar ta subuce masa mai yasa yake kasa aiwatar da duk wani kudiri da ya daukarwa kansa in har yana kusa da ita ya rasa dalili.
Zancen da yake ta saƙawa kenan a kasar zuciyarsa sosai yake ganin tana yi masa kwarjini a idanuwa sosai yake kasa aiwatar da komai in yana gabanta.
Kai ya shiga girgizawa yana faman taunar laɓɓansa kamar su ne masu laifin sosai yake jin komai ya cushe masa sosai yake ganin kwanciyar hankalinsa na guje masa sosai komai ke shirin ƙwaɓe masa a rayuwa a dalilinta a matsayinta na kaskantaciya wacce bai dauka a bakin komai ba.
"Ni Huzaif ni ta wulakanta".
da sauri yake girgiza kai ya nasake furta.
"ya zama dole nasan abin yi zuciyata ba zata yafe mani ba sam! na lura da hakan".
Haka yake ta sakin zance kamar wani zararre tsayin lokaci kafin ya mike cikin karfi hali ya fada Toilet ruwa ya watsa wa kansa nan ya fito ya shirya domin ya lura in har yana zaune a waje daya komai zai iya hanashi sakat! musamman kan maganar yarinyar da yake ji a ransa ya tsana tsana mai tsanani.
*****
"Please Khairiyya!".
Ya fadi cikin wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa a gareshi sosai yake jin zafi a zuciyarsa sosai yake jin ko ina na zuciyarsa na yayyagewa sosai kansa ke sara masa komai ya kwance masa sosai ya shiga tashin hankali mara yankewa wanda yake tsammanin zai iya tafiya da numfashin sa.
Sai da ya gama ja-in-ja da numfashin sa kafin ya daga laɓɓansa daƙyar.
"Ina cikin Matsala sosai da sosai na rasa ya zan yi komai yake kwance mani na tunani na komai zai iya faru ki taimaka ki zo".
A wannan karon muryarsa ta rage sauti sannan kuma tana rawa hannayensa duk biyun ya daura akan sa bayan ya sauke wyar daga kunnansa sosai yake jin tashin hankalin da ya tunkaro shi sosai yake jin bugun zuciyarsa na sauyawa daga kwanciya hankali zuwa akasinsa.
"ban san abin da ya sanya ni gamu da ita cikin duniyata ba, ban san abin da yasa ta shigo rayuwata ba ban san abin da yasa ranar ta zo mani a haka ba ban san mai yasa tsautsayin da nake gudu yake kokarin fado mani ba ban san gangancin da ya kai ni wannan ranar har hakan take dauko mani tashin hankali wanda ba zan iya dauka ba".
Gabadaya ya zube kan cafet din dake tsakar dakin yana faman sakin numfashi a hankali ji yake yi kamar gabadaya tashin hankalin duniya a kansa ya kare.
Marikin kofar da yaji an murza ne ya sanya shi saurin buÉ—e idanuwansa da suke rintse sosai yake kallonta da yanayin da ta shigo dashi kau da kai yayi gami da jan gudun tsaki wani haushi ne yaji ya tokare masa wuya ji yake kamar ya tashi ya rufe ta da duka sai yanzu yake dana sanin kiranta bai san dalilin da yasanya shi kiranta ba wani haushi yake ji a game da ita gabadaya yake ganin muninta da wani haushi nata yana tun karoshi mai da idanunsa yayi ya rufe.
Ita kuwa ganin irin Halin-ko-in-kula da ya nuna mata sai ta dauke kai tana mai jan tsaki a hankali ta fara taku har ta isa kan daya daga kujerun falon ta zauna kafin ta dube shi sosai kallo take masa na TUHUMA sosai take ganin sauyi gareshi sosai take ganin komai nashi ya sauya ba yarda ta san shi ba kyaɓe baki tayi kafin ta motsa laɓɓanta da suka sha Pink din jambaki.
"Huzaif".
Ta fadi a hankali tana kara kureshi da idanuwanta manya masu kalar madara sai faman kaÉ—a su take yi.
Bai motsa ba balle ta saka ran masawar sa sosai taji haushin haka amma bata nuna ma sai ma sake kiransa da tayi nan ma bai amsa mata ba hakan ya kara kular da ita a zafafe ta mike ta fara kokarin barin falon tana fadin.
"A rayuwa na kijin wulakanci zan iy daukar komai amma ban da wulakantawa kuma wannan zai zama karo na karshe wallahi!".
tana gama fadin haka ta rike murfin kofa tana kokarin murÉ—awa ta fice.
Huzaif da yake fama da zafin zuciya ya kokarta buÉ—e idanuwansa ya sauke akanta.
"Khairiyya".
ya fadi a raunane ita kanta sai da taji wani iri a jikinta a sanyaye ta saki kofar gami da juyowa ta dube shi tana harÉ—e hannayenta a kirji.
"Taimako nake bukata don Allah".
Da mamaki take dubansa tana juya maganar tasa akanta kafin ta yi taku uku sannan ta tsaya.
"Huzaif taimako fa kace?".
Kai ta shiga girgizawa tana faman sakin yaƙe.
"me ke damunka har kake neman taimako a duniyar nan?".
Ta sake fadi tana mai kafeshi da idanu sosai.
"Nima ban sani ba komai ya kwance mani kawai ji nake kamar bani ba...".
Da hanzari ta tare shi.
"Ban gane ba Huzaif?".
Tashi yayi daga kwancen da yake a hankali ya mike tsaya sosai yake kallon Khairiyya sosai yake hango zata iya taimaka masa sosi yake ganin ita kadaice zata iya yi masa komai da yake bukata.
Gyaɗa kai yayi kafin ya ciji laɓɓansa hannunta ya kamata ya fara kokarin ja da sauri ta fizge tana masa kallo mai dauke da TUHUMA shima kallonta yayi wani iri kafin ya sake jan hannun nata suka fice daga cikin falon.
******
Sosai ya zuba musu ido yana jin wani iri a gameda su gabadaya zuciyarsa ta ki yarda da su sosai gabansa yake faduwa ji yake kamar akwai mugun nufi a tattare da su sosai ruhinsa da zuciyaesa suke nuna masa shakka akansu idanuwansa sosai yake dubansu da su tun da yayi Parking a harabar asibitin ya tokare a jikin motarsa kira BMW yanayin su kawai yake kallo yake hango rashin gaskiya da kuma tashin hankali a tattare da su a hankali ya fara takunsa cikin natsuwa idanuwansa na kan su har izuwa lokacin kofar da zata sada shi da cikin asibitin ya dosa sai da ya zo daidai da su gabadayansu idanuwansu suka sarƙewa juna wani irin kallo suke duban junansu dashi kamar wanda suka san juna da jimawa zuciyoyinsu sai fama kawo musu wani lamura suke ma bambanta wanda su akaran kan su ba su na me nene ba.
Kau da kai Dr.Karami yayi da sauri yana gyara zaman niktayal din wuyarsa ya cigaba da takunsa ba tare da ya sake bi ta kan su ba har ya isa cikin asibitin.
Sannu a hankali ya fara takunsa yana ajje wa dakin su Mariya yanu fa yana kokarin sa kai itama ta sanyo kai zata yo waje kamar daga taji a kirjinsa da sauri cikin yanayi na firgici ta ja da baya tana mai zare idanu.
"Subhanallah!".
Ta fadi cikin tsanani kaÉ—uwa sosai take kallonsa shima idanuwansa na kanta sosai yaji wani irin Shock a ko ina na hanyar jininsa har sai da ya runtse idanuwansa domin ji yayi gabadaya kansa ya shiga juyawa kamar wanda wayar wuta ta zukar wa jini yayi low sosai
"Don Allah...".
Ta fadi tana mai rawar baki idanuwanta ta sauke su kasa sosai da sosai take jin ko ina na jikinta na sauri jininta yana kara gudu zuciyarta na kara sauti wajan bugawa.
Hannu ya daga mata yana mai sakar mata murmushi gami da lumshe idanuwansa sosai yake fuskartar natsuwar da take dashi sosai yake jin tana burgeshi duk da kananun shekarunta amma hankalinta na yanayin natsuwarta kamar mai shekaru sama da ashirin ko da yake duk wanda ya ganta ba zai taba bata haura shekaru sha biyar domin Mariya tana da tsayi da kuma kaurin jiki irin matan nan ne masu diri da cikar matantaka sosai ta ko wani fanni sosai jikinta yake bayyana irin baiwar kirar jikin da Allah ya bata ko ina na jikinta sosai ya cika sai dai ace yarinya ne a jikinta rintse idanuwansa yayi jin zuciyarsa na hasaso masa abubuwa ma bambanta da sauri ya zare tunani ya ajje gefe yana mai sauke numfashi.
"Yaa Allah! Mariya zaki fasa min kirji ko".
Ya fadi yana mai haÉ—e girarsa kamar gaske yanayin da ta dan razana ta dago kamt da sauri tana kallonsa lokaci guda idanuwanta sukayi rau-rau kamar za su zuvda hawaye.
"Don Allah...".
Da sauri ya kai dan yatsarsa bakinsa gami da furta.
"Shiit".
Yanayin yarda yayi salon sai ta saki baki tana kallonsa sosai taji ya burgeta da yanayin da murmushi ya sauka a fuskarsa ta tabbata wasa yake yi mata kasa tayi da kai ta dag laɓɓanta.
"Ban sani ba, ban san kana taho wa ba na rokeka...".
"Nace kiyi shiru mana!".
Ya fadi muryarsa da dan sauti a cikinta. GyaÉ—a kai ta shiga yi tana kokarin giftashi ta wuce ya tae ta da cewa.
"Ina kike kokarin zuwa?".
Shiru tayi tama rasa mai za tae dashi sai juya faka din dake hannunta take mai dauke shara.
Sosai ya gane in da ta dosa amma so yake yi tayi magana da kanta amma ya lura magana ma wuya take mata
"koma ciki to tunda ba in da zaki".
Da sauri ta dago kanta tana kallonsa yanayin da taga ya ci mur ta san da gaske yake baki ta fara motsawa.
"Shara...".
Abin da ta fadi kenan ta tsuke bakinta ta sake yin kasa da kai tana cigaba da wasa da fakar dake hannunta gabadaya taji gajiya na saukar mata sosai ta matsu ta bar wajan amma ta lura Dr.Karami sai ya ga kafarta ta zubda ita kasa sannan zai rabu da ita.
"Ya jikin Umma?".
"Da sauki".
Abin da ta fadi kenan domin ta lura in dai yayi magana bata amsa ba hakan ne zai sanya ya hanata tafiya.
"Madallah! zaki iya tafiya".
Kamar wacce take jira da sauri ta fara jan jikinta har tana kokarin tuntuɓe sosai yake kallonta yana kallon yarda take ajje taukunta duk da dai cikin yanayin tsoro take amma hakan bai hana bayyanar da natsuwa a takunta ba sai da ya ga fitarta sannan ya numfasa ya karasa shiga dakin.
Tunda Mariya ta fice take gayyato natsuwa tana yafawa kanta sodai tsoro da kunyar Dr.Karami suke samun mazauni a zuciyarta sosai komai nashi yake burgeta sosai take jin wani iri in suna tare sosai zuciyarta ke natsuwa in suna tare amma a zahirince tsoro ne ke bayyyana a fuskarta ta rasa dalili ko da yake zata iya ajje hakan a matsayin Kwarjini da yake mata sosai musamman yanayinsa da cikar halintar mazanataka da yake dashi sosai take jin wani iri in tana gabansa sai ta raina kanta sai taga kamar dan tsako ne a gaban rakumi.
Har tasa inda za ta zubda sharar bata daina zancen zuci ba saura kadan ta afka cikin dan wajan da aka tanada don zubda shara ita kanta sai da taji kunya da sauri ta zubda sharar ta juyo domin komawa cikin asibitin taku kadan tayi da yake kanta a kasa yake sam ba ta lura da wanda yake gabanta ba gabadaya ta ji ta ci karo da mutum sosai ta tsoro zuciyarta lokaci guda ba wanda ta kawo mata sai Dr.Karami tunanin ya kawo mata wato yana biye da ita kenan lokaci guda ta sake tsora a ranta tana fatan Allah yasa bai ga halin da take ciki ba a dalilinsa.
Tunaninta ya tsaya lokacin da taji wani wari gami da kamshin tuarare sun haɗe waje daya sun ba da wani kamshi mara dadi don sai da taji zuciyarta ta fara tashi da sauri cikin tsananin haushi da takaici ta dago kanta ta sauke kan mutumin da ya kusan tafiya da numfshinta da sauri ta ja baya tana mai zare ido bakinta na ƙarkarwa sosai take kallonsa gabadaya take jin tsoro da dukan zuciyarta na karu yanayin da ta ga idanuwansa sun kaɗa sunyi jajir har wani launi duke sauyawa nan da nan ta shiga waige waige domin neman hanyar cetar kai sai dai sam hankalin mutane da suke kai kawo baya kan su da sauri ta ja da baya tana ambatar sunan Allah a zuciyarta lokaci guda ta ji wani irin takaici da haushinda ya sake turnuke ta kau da kai tayi domin ta fusakanci rainin hankali tsantsa yake son kawo mata sabo ya rainata ya raina girmanta ya ganta kankanuwa shiyasa ya sami lasisin da zai shigo rayuwarta ya yi abin da yake so saboda ya mai da ita marashin 'yanci in ba wai tanuna masa zahirin ta bane ta nuna masa ita ma mutum ce kuma ta san darajar kanta ba za su zauka lafiya.
"Na rokeka da Allah da Annabi ka fice daga rayuwata amma ka ki ji ko to bari in hadaka da Iyayenka kila a dalilin su ka bar ni".
Ta fadi tana kara tsuke fuska sosai idanuwana kansa amma sam bata ga yanuna wani alamun yin wani abuba sai ma kara wani yaƙe yake yi saman fuskarsa haka kular da ita sosai.
"ban san mai nayi maka ba, ban san mai yasa kake kokarin shigowa rayuwata ba, ban dan abin da ka gani a duniyata ba har kake kokarin shigowa na rokeka ka fita harkar ta bana bara ma da kai ko miskala zarratin".
"Mariya!".
Sautin muryarsa da ta doki kunnuwanta sosai hakan ya kara tsinka mata zuciya amma hakan bai sanya tsoro ya bayyana a fuskarta ba.
"karka sake kiran sunana kuma ina mai rokon ka da karka sake batar sunana mai so ka ajje sunan Mariya a matsayin wanda baka taba sani ba ko a Mafark...".
Gabadaya taji hannunta cikin nasa ya sarƙe waje daya ba ta san lokacin da ta saki fakar dake hannunta ba cikin tashin hankali tana kokarin kware baki ta kurma ihu taji ya saka dayan hannunsa ya rufe mata baki nan ta kara hargitse tana faman zille-zille domin kwatar kai amma ina ta kasa domin ji take kamar wacce aka daure da sarƙa idanuwanta suka kara yo waje sai faman nishi take yi amma ko a jikinsa sai ma faman murmushi da yake yi idanuwansa na kara hargitsewa waje guda a hankali ya zare hannunsa daga bakinta hakan ya ta damar sakin ihu amma ba mai sauti ba ganin irin alamu da yayi mata alamun shiru.
"kin fiye tsiwa Mariya".
Ya fadi yana kara sarke hannayensu waje daya yana murzawa kadan sosai take jik wani iri a jikinta ko wani sashi na hanyar jininta take jin yana tsayawa cak! da aiki sosai sumar wucin gadi ta ziyarceta a hankali ta fara rintse idanuwanta tana jin tashin hankali na samun ma sauki a kowa ni sashi na jikinta zuciyarta na kin abin da yake mata tsanarsa take ji sosai da sosai tana jin haushinsa na samun matsuguni a zuciyarta.
Sosai wani sashin zuciyarra ta shiga biya mata karatu.
'Ke fa mace ce akan mi zaki tsaya wani namiji gardi yana rike miki hannun kin san illar haka kuwa shin ko kin manta kalamansa da yake fadi miki a haduwarku ta farko'.
Sosai zancen zucin ta yayi tasiri a ko ina na sashin jikinta abin zuciyarta take sanar da ita a yanzu shi kawai ke amsa kuwwa a kunnuwant sosai take jin tana da karfin gwuiwar aikatawa in dai ita kadai ce hanyar da zata kwai kanta da mutuncinta.
Tun da Mariya ta kulle idanuwanta ya zuba mata idanu sosai yake kallonta sosai yake kallon fuskarta da laɓɓanta da suka tsuke waje daya sun yi jajir da su hancinta dan madaidaici mai tsayi idamuwanta da suke rufe haƙa suka kara bayyanar da girmansu yake sosai yake jin zuciyarsa na sauya salon wasu lamurka sosai yake jin komai na kwance masa sosai yake kallonta tana burgeshi.
Mariya da ta buɗe idanuwanta a daidai lokacin shi kuma ya shigar da laɓɓansa cikin bakinsa yana lasa ba ta san lokacin da ta daga hannu ta sauke masa zara-zaran yatsunta a kan kuncinsa ba ji kake Tasss!!.
"ji ba yar iskan ba ce ka sani ni 'yar mutunci ce kuma iyayena masu mutunce ne sun san daraja da kimata ba wai sun haifeni bane don kowa ni dan duniya ya zo wajena ya yashe ka sani ni da kake gani nafi karfin ka wallahi bar ganina karama wanda yake baka lasisin zuwa gareni da mugun nufinka to ka sani nayi maka nisa wallahi na wuce da saninka ni ba irin 'ya'yan da ake ribata bane har a bata masu rayuwa don haka ka kiyaye".
Ta karashe cikin yanayi na rashin tsoro ko abin da zai je ya dawo a da sauri ta fizge hannunta tana tsartar masa da yawu ta wuce abin ta.
gabadaya komai nashi yaji ya tsaya na jikinsa sosai ya ji sa wata duniya wacce mai san ta mene ne ba sosai sosai yaji kansa na juyawa sosai yaji komai ya kwance masa gani yake yi kamar bashi ba gani yake yi wannan lamarin da ya faru kamar ba gaske ba gani yake yi ko a mafarkinsa ban yi tunani haka ta kasance ma dan yatsansa ya saka a baki sosai ya ciza shi kamar zai tsinkeshi zafin da yaji ya ziyarce shi ne ya sanyashi sauri buÉ—e idanunsa ganin lamarin gaske ne bai san lokacin da wasu kwala suka taru masa a idanu ba da sauri yayi kokarin mai da su yana mai dafe kirjinsa ba abin da yake hangowa sai hannun Mariya lokacin da ta daga ta sauke a fuskarsa ba abin da kunnuwansa ke jiyo masa sai yarda sautin marin ke sauka a kan fuskarsa.
Sosai kalaman da ta furta suke dawo masa sosai yake jin wani irin yanayi na zarya cikim gudu suna samun masauki a ransa sosai yake jin wani katon abu mai nauyi na samun masaukin a zuciyarsa da kasan ruhinsasosai yake jin wani irin abu maɗaci da bauri na sarƙe masa harshe sosai kalmar MUTUNCIN tana dashi yake amsa masa kuwwa a ko wacce dakika gyaɗa kai ya shigayi gabadaya ya kasa motsawa lokaci mai tsayi ya dauka a haka har zuwa lokacin mai gama tantacce abin da ya faru dashi gskiya bane.
"Uhm ai ita dama WUYA MAKARANTAR KARE ce wallahi".
Abin da muryar Khairiyya ta fadi kena tana dosa in da yake sosai take masa wani irin kallo na raini da takaicin abin da ya faru sosai take jin ɗaci a ranta musamman yarda taga komai ya faru akan idom ta ba abin da y kara tsikar mata da zuciya sai Yainyar da ta gani wai akanta Huzaifa yake zaucewa ta rasa ma mai ya dace tayi ji take kamar ta tsinke shi da mari amma ina! ba za ta iya ba a hankali ta fara riko hannunsa ta na murzawa sannu a hankali ta fara jansa tamkar rakumi da aƙala har suka isa wajan motar gidan baya ta buɗe ta turashi cikin wani irin yanayi kamar wanda akayi wa dukan shan gishiri.
Sai da ta kare masa kallo sosai da sosai tana kallon yarda ya rintse idanuwansa kirjinsa na harbawa da sauri-sauri kamar zuciya zata fasa ta fito kau da kai tayi jiki a sage ta koma gidan gaba wajan zaman direba ta shiga ta tada motar cikin wani irin yanayi ta fizgi motar har sai da kura ta tashi ta fice daga harabar Asibitin.
Post a Comment (0)