UKU-BALA'I 13

UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
​​WÉ› ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucÉ‘tÉ›, MѳtiѵɑtÉ› ɑɳɗ ɛɳtɛʀtÉ‘iɳ ѳuÊ€ ʀɛɑɗɛʀร​.
BABI NA GOMA SHA UKU.
Kai komo kawai take yi a tsakar dakin ako wani takunta daya sai ta dubi Huzaif tana mai ajje numfashi sosai da sosai take jin haushinsa da takaici akan abin da ya aikata sosai take kallon abin a matsayin babban kuskure mai girma sosai a idanuwant sosai take ganin wautarsa da ganganci da kuma yada zuciya kare ya dauke.
Numfashi ta ajje bayan ta tsaigata da kai komon da take yi sosai ta ajje ganinta akansa.
"kasan kuwa abin da ka aikata kasan kuskuren da ka aikata ya girmama sosai a idanuwa...Well bana tunanin kai lamarin ka dauke shi a matsayin kuskure mai girma a idanuwanka".
Ta fadi tana mai cizon laɓɓanta bayan ta turasu cikin bakinta sosai zuciyarta ke zafi da raɗaɗi akan komai da ya aikata sosai take jin abu mai nauyi ya tsaya mata a kirji ya samu gurbin zama sosai take jin tamkar ita ce akayi wa wannan cin kashin.
"Bana tsammanin Huzaif din dana sani ne wannan bana tunani Huzaif din asali ne wannan anya kuwa ba wasu abu akan ka ba na tunanin abin da kake sha zai sanya ka aikata wannan kuskuren mafi girma a idanuwana".
Ta sake fadi tana mai girgiza kai sosai take jin komai da ya faru yana dawo mana ina ma tasan hakan zata kasance da tabbas sai Mariya ta raina kanta kamar ta yarinya karama har tasan ta daga hannu ta mari namiji namijin ma Huzaifa.
"Kaico!".
Cikin wani irin sauti ta furta kalmar tana jin É—acin lamarin ako ina na zuciyarta da ruhinta.
HarÉ—e hannayenta tayi a kirjinta tana kallon yarda komai na Huzaif ya canza sosai take ganin lalacia tsakanin idanuwansa da zuciyarsa sosai take hango gazawa a gareshi kau da kai tayi domin in har ta cigaba da dubanda da ganinta tabbas zuciyarta zata iya bugawa don tsananin takaici.
"Yaa Allah ta ya ya zan dubi wannan lamarin a wani MIZANIN HANKALI ya dace na ajje wannan lamarin bana tunani ko mai tabuwar kwakwalwa zai iya abin da ka aikata...".
"KHAIRIYYA".
Muryar Huzaif ce ta karaÉ—e dakin cikin wani irin sauti mai tsoratarwa cikin rashin tsammanin samun maganarsa ta ji ya ambace sosai ta saki zaren kalamanta ta saki baki tana kallonsa sosai take jin gabanta na bugawa gabadaya ganinta ta ajje a fuskarsa komai na shi take kallo da yarda tashin hankali da bacin rai suka nuna a filin komai nashi har zuwa lokain idanuwansa a rufe suke hannayensa saman fuskarsa sai faman juya su yake yi.
"Excuse me. Please".
Abin da ya sake fadi kenan idanuwansa a rufe tana kallon yarda laɓɓansa suke rawa sosai wajan furta ko wani harafi guda na kalaman da ya furta.
"ki bar ni naji da abin da ke kokarin yayyaga mani zuciyata please ki barni naji da abin dake kokarin tafiya da ruhina sosai da sosai nake jin bani bane Khairiyya bana zaton ni Huzaif".
Yanayin yarda laɓɓansa ke rawa da yarda kalaman nasa suke turereniya ga junansu hakan zai tabbatar maka akwai tashin hankali mai girma a zuciyarsa da ruhinsa wanda bai yi zaton wanzuwansa ba a duniyarsa sosai komai na tashin hankali ke bayyana kansa a ko ina nasa.
Rintse idanuwa Khairiyya tayi sosai da sosai take jin wani abu mai nauyi na samun gurbi a zuciyarta sosai da sosai take jin zata iya daukar kowa ni tashin hankali da take hangowa cikin idanun Huzaif ba za ta iya daura ganinta ta cigaba da ganin halin da yake ciki ba ba za ta iya cigaba da jin numfashin sa mai cike da tashin hankali ba.
A hankali ya fara kokarin daga dan yatsar sa dake fama karkawa sosai yake jin wani iri cikin zuciyarsa da inda take zaune a kirjinsa gani yake kamar wauta ya tafƙa sosai a duniyarsa amma ban yi amanar haka a zuciyarsa ba hango Mariya yake yi a matsayim wacce take kokarin kashe kan ta da kanta domin kuwa sosai ta dauka wa kanta fitinar da ba zata iya saukewa kanta ba sosai yakke ganin hauka cikin komai da take aikatawa sosai yake ganin rashin kunya da fitsara tsantsa cikin idanuwanta dole ya dau mataki ko ba komai ya koya mata rayuwar duniyar nan da yarda 'ya mace bata isa ta galaba akan ko wani ɗa namiji ba dole ta san waye HUZAIF ABDURRAZAQ.
A hankali ya mike yana duban Khairiyya da ta zuba masa idanu sosai murmushi yayi gami da dauke kan sa.
"You can go".
Abin da ya fadi kenan ya fara daga kafafuwansa cikin wani irin yanayi mai cike da abubuwa marasa dadi ga zuciyarsa Toilet ya nufa har zuwa lokacin idanuwan Khairiyya na kansa sai faman suke numfashi take yi a sauri-sauri sosai take jin wani iri a zuciyarta sosai take hango abin da zai dauko mata tashin hankali ya ajje mata a rayuwa sosai take hango abin da zai hanata rawar gaban hantsi a duniyar Huzaif sosai take hango komai na wargaje.
Numfashi take ajjewa mai dauke da abubuwa masu yawa da take zaton za su sayo mata tashin hankalin rayuwa a hankali ta daga jakarta zuwa kafatar tana faman gyaÉ—a kai kawai take yi tana tana jin wani abu mai nauyi na sakar mata a zuciya da duk wani gurbi na cikinta a hankali ta fara takunta domin ficewa daga dakin zuciyarta na wassafo mata abubuwa ma bambanta.
********
Sosai da sosai take jin wani irin tashin hankali na kokarin samun masauki a ko ina na sassan jikinta sosai take jin yarda kwakwalwarta ke kwala ihu akan tunanin da ya zo mata a bazata sosai take jin wani sauti mai kara sosai yana amsa kuwwa a kunnuwanta sosai.
Bugun zuciyarta yake kara sauri sosai da sosai takun da take yi da kafafuwanta suke aika mata da wani lamari na daban wanda yake kara hargitsa tunaninta idanuwanta a rintse suke komai take hangiwa komai da komai da ya faru yake dawo mata baya kamar yanzu ne yake faruwa a gigice take ajje numfashi mai tauri a kokarin janyo mata ruhi zuwa waje.
Bata san lokacin da tayi cilli da fakar dake hannunta ba ta sanya hannayenta zuwa kunnuwanta ta rufe su ji take kamar za su tarwatse dalilin sauti da ke musu sukuwa a ko wacce dakiƙa.
"Yaa Allah!".
Abin da ta furta kenan a kasan laɓɓanta cikin wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa a gareta jin gina tayi da kofar da zata sadata da cikin dakin gabadaya taji kafafuwanta na kokarin gaza daukar gangar jikinta ji take yi kamar jikin ba nata bane sosai take hango fuskarsa tun ranar farko komai yake dawo mata har izuwa wannan lokacin sautin saukar marin da tayi masa take ajin yana samun wajan ajje sautinsa a bangarori masu yawa daga sassa na jikinta sosai take hango wautar ta cikin aikata wannan kuskuren mai girma da zuciyarta ke ganin tayi sosai take ganin girmar lamarin na kara girmama a zuciyarta da tunaninta.
'Mai ya kai ta, mai ya kai ta aikata wannan danyen aikin, ta ya ya ma haka ta faru gareta tun da take ba ta taba marin wani mai girma kamarsa ba ko da bai kai shi ba bata taba mai yasa tayi haka ina tunaninta ya kai ta lokacin ina zuciyarta ta cilla a lokacin mai yasa bata hana ta ba'.
GyaÉ—a kai kawai take yi cikin daukar tashin hankalin da taji yana kawo mata hari, ta tabbata ba zai yafe mata ba, ta tabbata ba zai rabu da ita ba, ta tabbata zai shigo duniyar rayuwarta.
Ta ya ya ta wacce suffa zai zo mata?
Tunani da zuciyarta ke ta hasko mata ke tana kara gigita mata kwakwalwa da lamarin da take kara girmamashi.
Abu taji mai dumi na saukar saman kumatunta ko bata tabbata ba ta san Hawaye ne bayan HAWAYEN ZUCIYA da taji ma tana yi abin har ya kai ga bayyana dole ta firgita da lamarin ita Mariya ta mari wani wanin ma mai girma girman da ya dace ace ta ganshi ta daraja shi amma ina! ZUCIYA BATA DA K'ASHI.
'Akan mi akan wani dalilin zaki damu kan ki. Kina zaton in da ya cimma buri akan kudirinsa a kan ki tashin hankalin da za ki shiga mai ya girmema wannan ba kawai don mari har zaki bari tashin hankali ya yi girma mafi girma gareki karki yi sake har wannan kankanin abun ya hanaki abubuwa cikin rayuwarki'.
Wani sashi na zuciyarta ne taje tana amayo mata sautin zantukan nan.
Sosai tayi shiru tana nazarin kalaman sosai komai taji yana kokarin dawo mata daidai a hankali ta fara gyaÉ—a kai tana jin yarda zuciyarta ta cigaba da wanzar mata da wasu batutuwa masu girma a gareta.
'Shin in da ya keta miki haddi mi kik zaton zai faru dake a duniyarki'
Numfashi mai girma ta ajje gami da buÉ—e idanuwanta gabadaya sosai take kallon kanta sosai take kallon yanayin kankatarta tana kara nasarin abin da ta aikata a hankali komai da zuciyarta take fadi mata ya fara tasiri sosai a kanta sosai da sosai zuciyar ta dake komai na tsoronsa ya kai sai dai abu daya da take jin sa a zuciyarta duk a dalilinsa sai dai bata dan me nene ba bata san a me zata fassara shi ba sai dai zata iya barin sa a matsayin 'Mala' har zuwa nan gaba.
A hankali ta fara daga kafafuwan ta da taji sunyi mata nauyi kamar an daura mata wani abu da yai karfin girman jikinta sosai take kokarin amfani karfin zuciya tana jansu tana sanya hannayenta tana dauke guntayen hawaye da suka zobo mata sosai take takaicin zubarsu akan wani can wanda bai san darajarta ba mai san kimarta ba mai san martabar ta ba...
"Mariya".
kamar daga sama taji sautin muryar ya sauka a kunnuwanta da sauri ta ja kafafuwanta da take ja daƙyar ta ajje su waje guda ko ba a fada mata ba ta san waye hakan ya hanata juyawa domin adaidai wannan lokaci tana bukatar zaman kadaici ita kadai ba ta so ta sake daukar wani abu da zai so canja masa lissafin da take faman yi azuciyarta runtse idanu tayi jin takunsa na isowa gareta sosai take nuna rashin so wani abu a yanzu sosai fuskarta ta bayganar da haka.
A hankali ya isa gareta hannayensa sarƙe a juna jikinsa sanye da wani lallausar boyel mai kalar fari anyi masa dinki babu wuyar rigar an mata aiki da jare mai kyallin gold sosai kayan suka dace da jikinsa kansa sanye da hula ita ma dai kalar kyallin Gold ne doguwa ya dan rangwafar da ita kamar yarda yarbawa suke yi fuskar nan tashi fayau ba zaka ce ya hau shekaru talatin a duniya.
Sosai yake karantar yanayin ta da yarda ya hango damuwa dauke a fuskarsa sosai yaji rashin jin dadi a ransa ciza laɓɓansa yayi kafin ya gyaɗa kai.
"akwai abin da ke damunki Mariya".
Ya fadi yana sake kafeta da idanuwansa manya sosai take jin rashin son magana a daidai wannan lokaci amma ba za iya ajje Dr.Aqeel a matsayi marashin girma gareta ba tana jin sa sosai a ranta da irin ALHERI da yayi a rayuwarta.
"Uhmm bakomai kawai dai...".
"Mariya mana".
Ya fadi cikin muryar mai sauti da rarrashi a cikinta.
A hankali ta dago kanta ta dube shi na yan sakanni kafin ta kau da kai tana hango yanayin kulawa sosai cikin idanuwansa gareta tana hango yarda ya nuna alamun damuwa da damuwarta.
"Baabana".
Ta fadi murya na rawa yanayin da tayi maganar zai tabbatar maka kamar iyakar gaskiyarta ta fadi ko da dai ba karya tayi ba lamarin bacewar Baabanta cikin rayuwarta yana cikin sahun abin da take zaton ƙaddara zata kawo mata na rashin natsuwa.
"Yaa Salam!".
Dr.Aqeel ya furta cikin rauni sosai kafin ya daura hannunsa akai yana mai cigaba da cewa.
"Please Mariya ya kamat ace ki na sanyawa zuciyarki natsuwa gami da kwakwalwarki ke fa karamar yarinya ce sam bai dace ace har kin fara cin karo da irin wannan lamarin ba a rayuwarki kwakwalwarki ba komai zata iya dauka ba tsorona kar damu tayi miki yawa sosai wani abun zai iya kama ki na rashin dadin rai Please Mariya Rayuwarki tana bukatar komai mai dauke da sauki".
Yanayin da yake ajje furucinsa da rauni a ciki da kuma rarrashi sosai hakan ya taba zuciyar Mariya ji take yi kamar ta rushe da kuka ita a karan kanta ta san sosai take cikin SIRAƊIN RAYUWA sosai take ganin yarda rayuwarta ke zuwa a a hagu ita kanta ta dani komai na duniyarta ba mai natsuwa bane ta sani sosai da sosai ƙaddara ke dawainiya da ita a duniyarta.
"Mariya komai zai shige in har baki dau komai da zafi ba, rayuwarki tana da muhimmanci ga rasu rayuka masu yawa sosai wasu rayuka za su shiga tashin hankali mai girma in har ba ki rangwantawa kan ki ba".
A dan tsora ce ta dago tana dubansa sosai taji kalamsa sosai take fahimtar in da ya saka gaba rintse idanu tayi kafin ta buɗe su ta fara kokarin daga laɓɓanta.
"Ta ya ya hakan zata kasance, ta ya ya zuciya zata iya daukar wannan lamari mai girma ta ya ya karamar kwakwalwata zata iya daukar wannan lamarin mai girma, bana tunanin zan iya amfanar da wasu rayuka a halin da nake ciki bana tunanin ƙaddara zata iya bani wannan damar bana zatom ƙaddara zata juya daga shafin da ta buɗe mana mai dauke da kaya mai girma na rashin kwanciyar hankali bana zaton hak...".
A hankali ta rintse idanuwanta tana tura laɓɓanta cikin bakin ta sosai take jin abu mai nauyi yana samun gurbi a zuciyarta sodai take jin kirjinta na nauyi da girma a cikinsa.
"Bana tunanin Mahaifin ki zai guje ku a halin rayuwar da kuke ciki. Bana tunani zai samu kwanciyar hankali don ya bar ki bana tunanin saboda gazawa ce ko halin da mahaifiyarki take ciki ya sanya shi bacewa daga rayuwark...".
"Dr.Aqeel mai yasa kake cewa haka, mai yasa kake kokarin sanar dani abin da zuciya ta ba zata iya samun wajan ajjewa ba".
Nisawa tayi tana jin yarda zuciyarta ke wani karfi a duk fitar kalma daya daga bakinta.
"Mai yasa mai tsaya mun tafi tare ba, mai yasa da zai tabi bai tabbatar mani da in da zai je ba, mai yasa ya boye mani wani abu kuma ya san zuciyata ba iya dauka za tayi ba mai yasa ya tafi tsayin kwanaki fiye da arba'in ba tare da ya waiwayo mu ba ina jin zafi a zuciyata ina son Baabana sosai da sosai yarda baka zato ina bukatarsa kusa da ina ina bukatar kullum na dinga kallonsa yana wanzuwa a DUNIYARMU a kullu yau min. Ban so ya tafi wata duniya ba ta daban wacce ba musan a wani hali yake ba kullum tashin hankalin rashin sa kara girna yake yi a ko wani sashi na zuciyata".
Yanayin yarda take ajje kalmominta sosai suke taɓa zuciyarsa zuciyarsa yake jin tana wani iri tana saukar da wani lamari mai nauyi gareshi sosai tausayinta ke kara samun gurbi a ko ina na zuciyarsa sosai yake jin ba zai iya cigaba da kallon yarda komai na muryarta da zuciyarta ke kara rauni ba.
"Yaa Salam! Mariya kiyi hakuri don Allah komai zai zo karshe, kuma Mahaifinki zai dawo gareki na sani duk in da yake kuna ransa domin ku ne rabin rayuwarsa ko ina ya ajje kafarsa dole ya kasance tunaninku yana zuciyarsa".
"Amma...".
"Haba mana Mariya".
Ya tare da sauri domin sam ba ya bukatar ya sake jin wani furuci nata mai rauni ya daki kunnuwansa. A hankali ya fara juyawa domin komawa Office dama ita ya fito dubawa sosai yake jin yarda numfashinta ke sauka a hankali har ya bar wajan.
A hankali ta daga kai ta bashi da kallo sosai idanuwanta suka cika da kwalla suna kokarin zubowa bayan hannunta ta saka ta dauke su ta kwashe mintina a tsaye a wajan kafin ta kokarta jan jiki sosai take jin nauyi a ko ina na sassan jikinta musamman kirji don ji take kamar dutsen Dala aka daura mata kanta a kasa take tafiya sam bata lura da wanda ya ke gabanta ba sai da ya ga ta kokarin tureshi sannan yayi gyarar Murya a dan razane ta dago kai sau kadan ta bugi kirjinsa ta ja baya kadan tana mai jikin kunya sosai da sosai.
Ya lura da haka Murmushi yayi kafin ya fara kokarin magantuwa duk abin da suke yi da Dr.Aqeel akan idanunsa komai ya faru sosai ya ji nauyi mai girma a ransa da zuciyarsa musamman yarda ya ji muryar ta na amon kalamai mausu dauke da rauniya da gazawar zuciya.
"Mariya".
Ya fadi a dan tausashe. Ba ta dago kai ba balle kuma ya saka ran amsawarsa ko da dai ba sosai yake bukatar amsawar ta ta don ya sani dole ya ji rauni a muryarta ko da kuwa ta amsa din shi kuma abin da baya so kenan a ransa.
"Me ya sa?".
Kan ta ne taji ya daure sosai da abin da ya fadi ba ta san ina furucin masa ya dosa bata san mai zata iya cewa a matsayin amsa gareshi ba ta san tambaya yayi amma kuma bata san mai ya dace ta fadi a matsayin amsa ba sosai take jin tsauri a furucin nasa sosai take jin komai na kwance mata domin ita dai ta san ba zata ce ga abin da ya dace tace dashi ba.
Gyaɗa kai take faman yi sai motsa laɓɓanta take yi amma bata da abin cewa.
"Na rasa dalilin da baki daukar shawara, zuciyarki sam-sam bata daukar abin da ake sanar dake, Me ya sa?".
Sosai take jin nauyinsa a zuciyarta sosai take jin kamar bata kyauta masa ba don a yanayin da take jin furucinsa ya tabbatar mata kamar bai ji dadi ba. Amma kuma ba ta san dalili ba, ta san abin da yasa yayi wannan furucin ba, sosai ta fuskanci akwai abin da yake nufi da furucin nasa.
A Hankali ta fara kokarin dago kai domin kallonsa amma tana jin yarda gabanta ki bugwa da sauri sauri a hargitse ta kalle shi idanuwansa na kanta sosai yake kallonta fuskarsa ba ta san a wata matsaya zata ajje taba. Bata hango haushi a ciki ba kuma ba ta hango fara'a ciki ba. A hankali ta fara daga laɓɓanta da taji sun mat nauyi sosai bayan ta kau da idanuwanta daga gareshi.
"Hakuri...".
"Bana bukata ni ba abin da kika yi mani, kuma ba abin da nake son ji daga gareki ba kenan".
Yanayin da yayi maganar tasa sosai taji faduwar gaba don ta hango damuwa a cikinta sosai da sosai rintse idanu tayi ba ta so, ba ta so ko kadan ace ta dalilin ta mutum mai ALHERI ya shiga damuwa rashin kyautawa take hangowa a gareta.
"Ban san mai zance da kai ba, ban san ina ka dosa da maganar ka ba, bani da abin cewa domin maganar taka sosai na rasa inda zan ajje ta kayi hakuri don Allah".
Maganar ta ta tayi rauni sosai hakan ya sanya shi sassautawa a muryarsa don ya fuskanci kamar taji damuwa a maganarsa.
"Ban so na shiga rayuwarki don ta kura miki ba, ban son abin da zai kara rikitar miki da tunani, bukatata kawai shine damuwarki a ranki ki rage ta sam! hakan bai da ce ba a matakin shekarun ki Mariya sosai take jin rashin dadi a rai na da lamarin daukar ki nake kamar kanwata ban son abin da zai dinga saki damuwa bana jin dai har kasar ruhina".
Hannayensa ya yarfar cikin yanayi na rashin jindadi kafin ya sake cewa.
"ki shiga ciki don Allah ki wutar wa ranki Umma ta tashi na bata magani haka Mu'azzam ya faka amma ya koma don haka ba abin da za kiyi yanzu illa ki zauna ki ragewa kan ki tunani in kuma kina da abin yi ki je kiyi don karki zauna kuma ki fada wata duniyar ta tunani na san halin ki Please Alkawari".
Ya karashe cikin muryar rarrashi sosai da sosai taji wani iri a ranta hakan ya haifar mata da kasa mai yawa daga cikin abin da ke damunta a rai.
Kanta a kasa ta wuce shi sumui-sumui kamar maras gaskiya sai da ya ga shigewarta sannan ya saki ajiyar zuciya mai cike da tausaya kafin ya saki murmushi don ya lura ta amince da abin da yace kuma za tayi din rufe idanuwansa yayi na yan sakanni kafin ya buÉ—e su fuskarsa da fara'a kamar koyaushe ya fara taku domin ficewa.
Post a Comment (0)