UKU-BALA'I 14

UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
​​WÉ› ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucÉ‘tÉ›, MѳtiѵɑtÉ› ɑɳɗ ɛɳtɛʀtÉ‘iɳ ѳuÊ€ ʀɛɑɗɛʀร​.
BABI NA GOMA SHA HUDU.
Hannu bibbuyu ta zabga tagumi idanuwanta kan Mu'azzam. sosai take kallonsa tana jin wani irin abu na sauka kan zuciyarta da ruhinta, sosai take jin wani abu mai kama da ruwa yana kwaranya a ko wani sashi da loko na ma'ajiyar zuciyarta, komai take ji yana yi mata wani iri sosai take jin kauna da so mai girma na saukar mata akan kaninta ba abin da take nisawa a ranta sai yarda duniya lokaci guda take shirin juye mata da wata irin ƙaddara mai girma a rayuwarta. sosai take jin duniyar na wargajewa da dukkan wani farinciki mai girma, da ta san tana samu cikin kankanuwar rayuwarta.
Ya za tayi kenan in ta rasa wadannan madogaran rayuwarta ta mai duniyarta za ta kwaso mata in ta rasa wadannan mutane masu matukar muhimmanci a duniyarta.
Wasu hawaye masu zafi matuka taji suna sauka akan fuskarta da can cikin zuciyarta da ruhinta.
Ta sani kuma ta dade jimawa cikin duniyarta ba ta da sa'a a rayuwarta domin kuwa sosai ta fuskata ƙaddara mai kaifi ce ta fado mata da abubuwa masu matukar tashin hankali da yankewar farinciki Babanta ya tafi ya barta ga Ummanta bata da lafiya ga karamin kaninta wanda shi ƙaddara ta sunkuto shi cikin wannan duniyar mai dauke da kwamatsai rashin dadi ina ma tana da dama ina ma tana da iko ina ma ta san zai fado duniyar nan a haka da bata yarda ba da bata amince ba ina ma ace ana tuntuba kamin a sako dan'uwa duniya da ta roki ubangiji bai sako kaninta ba sai dai ba yarda ta iya komai na Allah tabbatacce ne a duniyar dangin rai kana naka yana nashi.
Hannu ta sanya tana mai dauke zafafan hawaye da take jin su a ko ina na sashin zuciyarta tana dauke su wasu na biyo bayan su tana jima cikin wannan yanayin kafin ta motsa ganin Mu'azzam yayi barci ta kai shi makwancinsa ta kwantar bayan tayi Hugging din sa a ko ina na fuskarsa sosai take jin kauna mai girma a tsakanin ko ina na sassan jikinta akan shi sosai take hango wa a duniyar nan bata da kowa dangin yan uwa sai shi dole ta kula dashi dole ta so shi domin shi kadai ne take zaton zai shafe duk wani daci da kunci da ukuba da take ji a zuciyarta na rashin yan uwantaka.
A hankali ta fara takawa har inda Umma take kwance ta na barci hankali kwance kallo daya zakayi mata ka tabbatar akwai alamun warakar natsuwa a tare da ita. Idanuwanta sosai ta buÉ—e akanta tana kallonta kamar wacce aka ce in ta dauke idanuwanta za a gudu da ita zuciyarta taji tana wani amsawa da wasu abubuwa mabambanta wanda ita kanta ba za ta ce me nene ba.
Wani murmushi ya subuce mata kalaman Dr.Karami suke mata yawo a kunne a jiya bayan ya zo ya duba Umma.
****
Kallonta yake yi sosai yana yawatawa da idanuwansa masu wani irin yanayi mai matukar kashe jikin wanda ake kallo sosai take jin kallon nasa na shiga duk wani sassa na jikinta yana haifar mata da wasu abubuwa wanda ba ta san a mizanin da za ta ajje su ba sosai take jin bugun zuciyarta sosai take jin yarda zuciyar ta ta take tsalle a duk wata dakika daya na kallon da Dr.Karami yake yi mata ta rasa mai yasa take jin haka ta rasa dalili lokaci da dama ana kallonta mutane masu muhimmanci a idanuwanta amma bata jin haka sai a kansa shi kadai kwallin kwal!.
"Mariya".
Yarda Dr.Karami ya ambaci sunan sai taji aduniyar rayuwarta bata taba jin wanda ya kira sunan da wani irin yanayi mai matukar amsa kuwwa a kwakwalwa da kashe jiki da sanya zuciya tsalle tsalle kamarsa ba sosai take jin duk wani sashi na jikinta na wani irin amsawa da narkewa kamar ana narka roba a wuta wani numfashi take ja mai matukar girma wanda take ji kamar in har batayi jarumtar jan sa ba numfashin katsewa zaiyi daga gareta kanta a kasa tana faman wasa da kasar rigar atamfar ta da take jikinta wanda kallo daya zaka yi mata kasan taji jiki sosai da sosai.
"kin fiye kunya da yawa. Ya kamata zuwa wannan lokaci ki saki jikin ki da ni domin an zama daya".
Wani irin kuwwa taji maganar tasa ta nayi cikin kwakwalwarta ji take kamar kasa ta tsage ta zurma ciki sam bata son yarda Dr.Karami ke mata amma kuma ta na son ta zauna dashi sosai a waje daya domin mutum ne mai saukin kai da kokarin kwantarwa da mutum hankali.
A hankali take daga kai domin ita dai ba ta san mai zata ce dashi ba bama ta san yarda kalaman nasa su ke zuwa ba cikin kwakwalwarta ita dai kawai sautin muryarsa take jin na amsa amo nata.
"kin ga dai yau kuna cikin kwana na Arba'in da takwas kin ga kenan yau saura kwana goma sha biyu su cike KWANA SITTIN da nace in Allah ya yarje mana komai zai daidaita a wajan Umma. Shin ya kike ganin jikin nata me kike karanta game da ita?".
Ya dasa aya yana mai dubanta sosai cikin idanuwansa yana faman murmushi yana gyada kai sosai yake jin Mariya na samun masauki a zuciyarsa da duk kan wani sashi na jikinta sosai yake jin ta tamkar uwa daya uba daya suke sosai yake jin wani abu mai girma yana samun waje a filin zuciyarsa yana zama wanda a kullum yana jin yarda yake daÉ—uwa ba wai raguwa ba murmushi ya sake yi.
"ban san mai zan ce miki ba, ban san ya kike rayuwarki bs, ban san mai yasa ba ki sakin jiki da mutum ba, ban san mai yasa kike gujewa mai...".
Sosai yaji kalmar da zai fadi tayi nauyi a bakinsa ta danne harshensa da wani gingimeman abu mai girma sosai yake buÉ—e idanuwansa akanta wani irin bugu yake jin kirjinsa nayi bai san mai zuciyarsa take kokarin yi ba bai san abin da take kokarin dauko masa ba wanda sam bai yi tunanin haka ba.
A hankali take dago kanta tana kokarin ajje idanuwanta akansa cikin yanayi na TUHUMA tana jin yarda zancen da yake yi ya yanke wanda take jin alamun akwai dalili kamar wani abu ne daban ya hana shi furta abin da yake kokarin cewa ko da dai ita akaran kanta ba ta san ina ya dosa ba kallo daya tayi masa ta kau da kanta jin yarda jikinta da zuciyarta sukayi wani irin tsalle.
Girgiza kai ta shiga yi tana tura laɓɓanta cikin bakinta tana tsotsa kamar wacce ta samu alawa ta rasa mai zata ce masa bata san abin da ya dace ta ce dashi ba sosai take hango wasu abubuwa da suke rikirkita mata lissafin kwakwalwarta a idanuwansa sosai take jin abu mai girma game dashi sosai take hango kwarjini da haiba na dandatsa ko ina na cikin idanuwanta in ta dube shi can kasan makoshi ta fara kokarin furta wani abu a hankali laɓɓanta suka shiga motsawa.
"Ban san yarda zan fuskance ka na ce da kai komai ba, ban san da harufan da zan yi amfani wajan cewa da kai komai ba amm...".
Da sauri taja numfashi gami da tafiya da sauran abin da tayi niyyar cewa.
Sosai ya ware idanu yana kallonta yana ganin yarda take datse laɓɓanta kamar wacce take tsoron furta wata kalma mai muni gareshi.
"Fadi mana ko ya kike zo da maganar ki zan fahimta ba zan ajje ta a mizanin da bata dace ba".
Ya fadi yana kara ware idanunsa sosai akanta wani matsayi yake jin ta na kara samu a gareshi sosai yake hango natsuwa da kula da kai tatttare da ita a hankali ya mike kan kafafuwansa yana duban in da Umma ke kwace tana barci Mu'azzam kusa da ita murmushi yayi kafin ya juyo ya dubi Mariya da take tsaye kikam! kamar wacce aka dasa gabadaya ta gama tafiya cikin wani irin yanayi, ba abin da take roko a ranta illa Dr.Karami ya tafi ko ta samu damar jan numfashi mai dauke da iskan Rahama.
"na tafi Mariya tun da yau na lura azumin magana kike yi".
Yana gama fadin haka ya fara taka kafafuwansa kamar da gaske tafiyar yake yi so yake yi ta dago ta kalle shi haka kuwa akayi tana jin tafiyar tasa tayi nisa gabadaya ta dago da idanuwanta aiko sai suka sarke da nashi ba ta san lokacin da ta saki kara ba gami da ja da baya tana runtse idanuwanta sosai ta sanya tafukan hannunta ta kara rufewa wata irin kunya take ji tana yawatawa a dukkan sasssan jikinta ji take kamar kasa ta tsage ta shige.
Sosai ta bashi dariya ganin yarda tayi a hankali ya taka ya fice daga dakin yana faman sakin murmushi wanda shi kansa mamaki yake yi komai na Mariya na burge shi sosai da sosai.
****
"Yaa Allah!".
Abin da ta furta kenan tana sakin murmushi gami da dafe kai bata san abin da ya shiga kanta ba gabadaya take jinta wani iri sosai take jin ta a wani irin yanayi in tana zaune ko suna tare da Dr.Karami rintse idanuwanta tayi gami da jan numfashi wani kamshi ne taji numfashin nata ya jawo mata ya kai mata cikin hanci a dan firgice ta ware idanuwanta tana Ambaton Allah tsoron ta daya Allah yasa ba Dr.Karami bane domin ko tantama bata yi wannan kamshin nasa ne amma bisa mamaki ba kowa da ta gani ajiyar zuciya tayi tana dungurin kanta domin ta tabbata sharrin tunani ne kawai da na zuciya suke mata haka.
*****
Dakiku masu dama ta dauka cikin motarta kafin ta fara kokarin buÉ—ewa ta ziro kafafuwanta zuwa waje nan ma sai da ta ajje dakiku sannan ta fara kokarin ziro da gangar jikin zuwa waje ta mike kan kafafuwanta sosai take yawatawa da idanuwanta izuwa wajen da take tsaye tana faman yatsine fuska duk da bakin glass din da ya rufe mata idanu hakan bai hana bayyanar yarda take yi da fuskarta ba cikin wani irin yanayi ta tura murfin kofar gami da sanya mata secure kafun ta fara kokarin jan kafafuwanta.
Sanye take da wasu kaya riga da wando fitted sosai wandon ya matse ta wanda iyakarsa gwaurinta mai kalar pink rigar dake jikin yar shara-shara ce mai kalar white da hannayen rigar ves ne wanda hakan ya bayyanar da rabin kirjinta sosai da ilahirin damatsan hannayenta fuskarta dauke take da Make-up sosai hakan ya kara ƙawata fuskarta ta laɓɓanta sun sha pink din jan baki sai daukar idanu suke gashin kanta ya ci gyara sosai sai fama daukar idanu yake yi ta barbaza shi a gadon bayanta a hankali take takawa saman takalamanta masu matukar tsine sosai komai nata motsawa yake a duk lokacin da tayi taku daya.
Sannu a hankali har ta isa cikin wajan wanda kallo daya zakayi masa ka tabbatar da wani babban ma'aikace bene mai dauke da hawa goma sha biyu daga yanayinsa in ka kalla sai ka rantse ba a kasar najeriya yake ba.
Kofar da zata sada ta cikin wajan ta dosa mutane da yawa masu harkokin gaban su sai bin ta suke da kallo na mamaki har ta isa kofar glass da take watayawa da mutane domin zuwa duk wani bene da suke bukata.
Ba tayi kokarin barin baban Falon dake kasa na cikin ma'aikatar ba domin ba ta bukatar haka koma ta bukata dole tayi hakuri a dalilin rashin sanin in da ta dosa ko ta shiga yau ne karo na farko da ta tako kafafuwanta zuwa cikin wannan waje yau ne farko da ta fara ajje idanuwanta akan wannan waje a zahirance yau ne kuma take bukatar duk wasu mafarkanta su tabbata yau ne take so ace sun yi gaba da gaba da shi yau ne take so komai ya zo kamar yarda ta jima tana burin abubuwa daban-daban kafin wannan rana tana so ace wannan rana ta kasance cikin ranakun da nasarrorin ta za su fara shawagi cikin duniyarta yau ne take da yakinin lissafinta zai fara aiki kamar yarda ta tsara komai nata...
"Madam!".
abin da securty din wajan babbar kofar da suke zaune daya daga cikin su ya fadi kenan yana mai mikewa bisa kafafuwansa ya tsaya gabanta.
Da sauri ta dawo daga duniyar tunanin da take yi ta sauke idanuwanta gabadaya akansa tana wani yatsine fuska gami da da sauke glass din fuskanta kadan manyan idanuwanta farare fes suka sauka akansa sai da ta gama kare masa kallo kafin ta gyaÉ—a kai cikin nuna halin-ko-in-kula gareshi.
Shima bai damu da irin kallon da take masa ba haka ya sanya abin binciken dake hannunsa yana yawatawa dashi a sassan jikinta kafin ya dago kai ya dubeta yana mai bata hanya domin karasawa wani murmushi ta saki wanda ita kadai ta san in da ya saka gaba a hankali ta kama Handle din kofar ta tura cikin wani irin taku na musamman wanda kallo daya zakayi mata kasan akwai abin da ta taka karan takun takalmanta bisa tayal din dake shimfiɗe a harabar wajan duk ya karkato da mafiya yawancin mutanen da suke zazzaune suna gudanar da aiyukansu kowanne mutum daya akwai table a gabanda da kuma fiyal fiyal gefe guda kuma kwafuta ce girki tacin glass dinta take ƴawatawa da idanuwanta a dukkanin sassa da kowa ni mutum dake zaune sosai ta lura ita suka zuba wa idanu murmushi ta saki har gefen kumatun ta na loɓawa sosai taji wani abu na yawatawa a cikin kirjinta wanda take jin sa ba abin da ke cikin sa sai hango abubuwan da take tsammanin za su faru.
"Heyy".
Abin da ta fadi kenan gaban wani table da wata mace ke zaune hankalinta gabadaya ya ta'allaka ga aikin da take yi sanye take da jallabi mai kalar Ash ta nannaÉ—e fuskarta da kallabin jallabiyar fuskarta fayau ba wata kwaliyya ta azo a gani amma hakan bai hana bayyanar tsantsan kyan da Allah yayi mata baiwarsa ba.
A hankali ta fara dago kanta ta na saukewa a in da ta ji maganar sosai ta ware idanu ganin wacce take gabanta cikin yanayi na mamaki da wani irin haushi da ya kasa boyuwa har sai da ya fito cikin idanuwanta gyaÉ—a kai tayi kafin ta mai da kanta kan Aikin ta.
"Dr.Abdurrazaq Erena".
Abin da ta fadi kenan tana mai wani kara bayyanar da wani murmushi dake fuskarta wanda kallo daya zakayi masa ka san ba a so ba.
Ba tare da ta dago da kallonta ba murya kasa kasa.
"Hawa na biyar hannunki na dama office mai lamba Uku".
Ba ta tsaya ansa ta ba ta dauko kafafuwanta ta fara tafiya a haka har ta hau Abin da zai kaita wajan cikin yan sakanni ta isa bayan ta sauka ta kalli kwatance da kayi mata wata kofa glass ta hango sannan ta kalli samanta murmushi ta saki ta fara takawa a hankali ta isa sakatariya ta gani zaune tana ta faman aikinta hankali kwance kwankwasa kofa glass din tayi kadan tana mai kallonta cikin wajan a hankali ta dago kai ita ma ta sauke a kanta murmushi akan fuskarta lokacin da ta dago amma tana cin karo da wacce ke gabanta ta tsuke fuska hadi da jan guntun tsaki tana kau da kanta.
Sai da ta shafe sakanni kafin tayi mata alamun ta shigo a hankali ta taka ta shiga ta dan yi kasa da glass dinta ta shiga motsa laɓɓanta.
"Please wajan Dr. Abdurrazaq Erena nake bukatar zuwa".
Kallon ban gane ba sakatariyar tayi mata tana mai kwaɓe baki kafun ta kau da kai hadi da fadin.
"Ya san da zuwan ki ne?".
Shiru tayi ba tare da cewa komai ba na yan dakiku hakan ya kullar da sakatariyar da sauri ta shiga duba cikin kwafutar dake gabanta tana yawatawa da idanuwanta cikinta.
"Duk yau a cikin jerin mutanan da za su zo gare shi ban ga alamun da ke a ciki ba".
Ta fadi tana mai dago kanta ta saukewa gareta.
a dan harzance ta sauke glass din ta sosai idanuwanta kan sakatariya kallonta take yi tana karantar yanayin da alamun so take ta samu wani tangarÉ—a da zata jona mata amma cikin nuna na fiki.
"ki je ki ce masa Areefa Saifullah ita ce take son ganin sa ya san da zuwana".
Yanayin yarda take maganar a dake da yanayin bacin rai ya sanya sakatariyar ware idanu sosai gami da tallaɓe haɓa tana kallon yarda wannan mai kalar gangar ke mata magana akai.
A hankali ta mike saman kafafuwanta masu sanye da wasu takalma masu matukar tsine kamar za su karye a hankali ta fara taku da dan guntun suket dinta wanda iyakarsa guiwa kadan taɓe baki Areefa tayi tana bin dumemiyar matar da kallo wacce tayi biyunta.
Mintina kalilan sai gata ta dawo tana faman tsuke fuska.
"ki Shigo kofa ta uku ita ce in da yake ciki".
GyaÉ—a kai kawai tayi gami da wucewa tana taku ko ina na jikinta rawa yake yi lokaci guda ta canza tafiyar da take yi ita dai sakatariya sakin baki tayi tana kallon ikon Allah har sai da Areefa ta bace mata sannan ta saki ajjiyar zuciya ta koma ta cigaba da aikin da take yi.
"Areefa Saif...".
Abin da ya fadi kenan yana hanzarin mikewa cikinsa har É“ari yake yi ya zagayo izuwa in da take tsaye hannunta rike da Handle din kofar sai faman yawatawa da idanuwanta take yi cikin Office din har ya iso ya tadda ita nan tsaye sai faman sakin wani murmushi yake yi hakan ya bayyanar da wawulan hakorin sa daya na gaba da ya cire amma in ba ka gane ba sai kayi zaton wushirya ce ta buÉ—e sosai a jerin hakoransa masu dan duhu kadan.
"Ban yi zaton ai yau zaki zo ba, domin Alhaji Abdulwahab ce mani yayi sai nan da gobe".
Ya fadi har lokacin idanuwansa na bin duk wani sashi na jikinta yana kallo kafun ya yi mata nuni da kujerun dake cikin office din alamun taje ta zauna sosai take kallonsa ta cikin glass dinta tana karantar yanayinsa sosai take hango komai kamar ma ya yuwu kallonsa take yi tun daga fuskarsa har kafafuwansa babban mutun ne don a kalla zai baiwa shekaru hamsin baya amma hakan bai nuna a fuskarsa ba saboda yanayin huta da jindadi da suka taimaka ma jikin nasa baki ne amma ba can ba yana da idanuwa masu dan girma sun dan yi ja kadan hancinsa ba dogo bane yana da fadi haka ma bakinsa mai dauke da manyan laɓɓa masu kalar baki baki haka zai tabbatar ma da yana shan wani abu.
Ba tare da ta ce da shi kala ba ta doshi cikin Office din sosai tana wata irin tafiya ta firgita duk wani namiji da yake gabanta har ta isa ta zauna ta ajje jakar dake hannunta gami da daura kafa daya kanta daya a hankali ta sauke glass din dake fuskarta gabadaya shima ta ajje shi kan Table din dake gaban kujerun ajje numfashi tayi alamun gajiya gami da dan dafe kai.
A hankali ya fara takowa in da take kallo daya zakayi masa kasan sosai Areefa ta tafi da guntun imaninsa jikinsa sai É“ari yake yi fuskarsa tana sakin murmushi idanuwansa kamar za su fado kasa.
"Areefa Saif...".
Ya sake fadi cikin salo na yin kasa da murya kamar wanda yake rokon wani abu a gareta.
KaÉ—a idanu tayi gami da dan daga girarta tana mai yawatawa da idanuwanta akan sa zuciyarta nayi mata wani tsalle na murna da jin wani dadi amma bata bari hakan yayi tasiri a fuskarta ba domin a gimtse take ba alamun dariya.
A hankali ta fara motsa laɓɓanta da wani irin yanayi tana mai kaɗa idanuwanta.
"Ya kamata ace ka koma ka zauna domin time dina a tsare yake akwai in da zan je ne".
Ta fadi tana da murmushi a fuskarta da sauri ya ja gefe gami da ware idanuwansa sosai ba tare da yace komai ba ya koma can inda kujeransa take mai juyawa ya zauna gami da saka kan biro a bakinsa yana cizawa kujerar na watayawa dashi idanunsa akanta sai faman sakin murmushi yake yi a hankali ta kau da kai gami da tura masa fiyal din da ta zo dashi.
Hannusa guda ya kai yana janyo fiyal din yana mai sauke idanuwansa akansa buÉ—ewa yayi a hankali yana yawatawa da idanuwansa a cikin tsayin minti daya kafun ya mai da ya rufe ya dan bugeshi kadan ya dago kansa ya dubi Areefa wacce ita ma hankalinta na kansa ta na kallon yarda yake duba fiyal din.
"Komai yayi daidai zaki iya fara aikin zuwa On Monday in kuma akwai Time din da kika zaba zaki iya amfani dashi...".
Hannunta ta dan daga kadan tana dan murmushi.
"No ba ni da wani lokaci sai wanda ka yanke mani domin ina bukatar fara aikin ne akan lokaci ba tare da zabina ba sai zabin da kuka bani".
Ta karashe tana mai mikewa kan kafafuwanta gami da daukar jakarta ta.
"Ina Godiya".
Ta fadi tana mai kara sakar masa murmushi shi dai idanuwansa har zuwa lokacin suna kanta kamar wanda aka jona wa mayen karfe har ta fara taku amma bai motsa ba motsin Handle din da ya ji ne ya fargar dashi da sauri ya ware idanu yana kokarin tashi amma ina kafun ma ya kai ga tashi ta fice daga cikin Office din komawa ya yi ya zauna jikinsa ba kwari hannu bibbiyu ya tallaɓe haba da su yana kallo kofar yana faman sauke numfashi a hankali

Post a Comment (0)