YADDA TURAWA SUKA Ƙwace Sokoto

YADDA TURAWA SUKA KWACE SOKOTO
Daga Sadiq Tukur Gwarzo, RN.


Turawa sun riski Arewa a zamnin Sarki Musulmi Abdurrahman ɗan Atiku.
Shikuwa Anyi masa mubaya'ar sarauta a gidan waziri Buhari ne bayan rasuwar Sarkin musulmi Ummaru, sannan ya taso daga Kauran Namoda ya nufi sokoto.
Akan hanyarsa ya sauka a Gora, ya aika cewar Sarkin Mafara yazo gareshi, sarkin mafara yace bazai iya zuwa ba saboda rashin lafiya, amma ga galadima nan ya amsa mubaya'a..
Sarkin musulmi yace baya amsar mubaya'ar galadima, sarkin yakeso yazo da kansa, amma sai sarkin Mafara yaki yaje.
Rannan bayan sarkin Musulmi Abdurrahman ya isa gida Sokoto, sai aka sake aikewa sarkin musulmi da cewar husuma ta auku tsakanin sarkin Mafara dana Burmi, har sarkin mafara ya kame Birnin Tudu dake ikon sarkin Burmi.
Sarkin musulmi ya aike zuwa Mafara cewa ya saki wannan gari indai ya tabbatar Birnin Tudu na sarkin Burmi ne, idan kuwa ba nashi bane to ya aiko da jawabi mai daɗi gareshi.
Sarkin Mafara ya aiko da cewar Birnin Tudu ba na sarkin Burmi bane, na Namai-barau ne, shikuwa nasa ne. Yanzu kuma Ibo ke ikon ta, shima kuma nasa ne.
Sarkin musulmi ya aike ga waɗannan sarakunan da cewa suyi sulhu a tsakanin su, amma sai sarkin Mafara yaki ya karɓi sulhu.
Sarkin musulmi ya aike da sako Mafara cewar matsawar sarkinsu bai karɓi sulhu ba, to yaki na zuwa daga gareshi.. Mutanen Sarkin Mafara suka haɗu da jakadan sarkin musulmi a wani wuri mai suna Rini suka harbeshi da kibiya, sannan sukace sun ɗauki faɗa da sarkin musulmi.
Sarkin musulmi ya aikewa Sarkin Anka wannan abu, amma shima sai aka tarar yana goyon bayan Sarkin Mafara ne.
Daga nan kuwa sai sarkin musulmi ya hori a buga tamburan yaki, yace mutanen Anka da Mafara sun zama abokan gaba, sannan ya aike da sarkin zamfara Ummaru ɗan Mahmudu gabas, yace ya rinka aikewa da hari mafara.
Ya kuma hori Sarkin Rafi Alhaji daya zauna a Magami ya kuntatawa mutanen muradun da hsre-hare.
Sannan ya aike jarumai domin su zauna tare da sarkin Burmi a Modocci don maganin harin da abokan adawa zasu iya kawowa.
Haka kuma ya umarci sarkin Sulluɓawa shuni daya rinka kai hare-hare ga Anka da Mafara babu sassautawa.
Yace da Magajin gari ya tafi Maru ya tara jarumai su tafi sukai hari ga Mafara.
Ya umarci sarkin Danko Ali yazo su haɗu a Laje don su kaiwa abokan adawa hari.
Da sarkin Mafara yaga haka, sai ya aike wa sarkin Gobir neman taimako. Sarkin Gobir Almu ya tashi da gagarumar runduna zuwa Mafara, suka tafi ga sarkin Burmi suka buka yaki har sau uku ana gwabzawa amma basu samu gagarumar nasara ba, anan nema aka halaka Bawa ɗan sarkin Mafara.
Daga nan sai sarkin musulmi ya aiki jarumai su tsare wababe, sannan yahau zuwa Mafara da yaki, ya buga yaki dasu da fari sannan ya koma gida.
Bayan ya komo gida sai mutanen Mafara suka saduda, suka aiko neman sulhu saboda kuntatar da akayi musu.
Sarkin musulmi yaki amsa musu, ya cigaba da shirin yaki abinsa.
Amma da suka matsu sai suka kori sarkinsu Buzu, suka aika da rawaninsa ga sarkin Burmi domin ya nemar musu sulhu da sarkin muslmi.
Da sarkin musulmi yaji abinda sukayi, sai yace indai da gaske ne suna son sulhu, to sai sabon sarkin da suka zaɓa ya zo gareshi.
Daga nan Sabon sarkin Mafara da sarkin zamfaran Anka suka taso izuwa ga sarkin musulmi suna masu neman amana, suka haɗu dashi a Gandi, yace su saki duk bayin da suka kama a yayin wannan rikici, sukace sunji zasuyi yadda duk yace.
Yace kuma bai yadda da amanar suba har sai sun bashi bayi dubu.
Sai da suka bashi kuwa sannan ya aminta dasu.
Sannan yace ya mayarwa sarkin Burmi birnin Tudu, suka ce sun yadda,.
Ya hori sarkin mafara da jama'ar sa duk su daina al'adar nan tasu ta ahi( atire) da aka sansu da ita, ya rarraba yankuna kuma ga sarakunanda suka taimakeshi a wannan yaki.
Ya baiwa Alhaji Maradun, ya raba wasu yankuna tsakanin sarkin Mafara Laje da Sarkin Danko Ali.
Bayan duk an kare wannan, sai ya shirya zuwa Argungu da yaki, yaje ya kai mata hari ya dawo gida.
Bayan ya dawo ya kai yaki Ruwan Bore ya kame waɗanda ke ciki, sannan ya sake shiryawa zuwa Argungu a kashi na biyu.
Bayan ya dawo dai, ya sake kaiwa Ruwan Bore da Argurgu hari a karo na uku.
Daga nan sai yaron turawa mai suna Adamu yazo masa. Yazo tare da yaron sarkin zazzau, da gaisuwa da hajoji da suka saba aikawa ga sarkin musulmi. Sarkin musulmi yaki amsar gaisuwarsu ya kuma koresu.
Daga baya sai aka shirya gyara da turawa, sarkin musulmi yaci gaba da karɓar gaisuwarsu.. Ana kan haka kuma sai ƙlabari yazo cewa turawa sun kone Nufe, sun cinyeta da yaki..
Koda sarkin musulmi yaji haka sai ya daina amsar gaisuwarsu. Amma kuma labarin ciye-ciyen garuruwa daga turawa ya zamo yanata karuwa a kullum.
A haka har sukaci Bauchi, sarkin Bauchi ya gudo zuwa kano.
Rannan bayan an kare Basasar Kano lokacin da waziri ya sauka a zariya sai kwatsam ga turawa sun dira da rundunar su ta yaki, suka ce sai a saki bayi duka, aka sakesu.
Suka tsare waziri a zazzau.
Suka sa dogarai biyu a kowacce kofa, amma akwai wata kofar da waziri ya sulale ya bar zazzau zuwa kano da ba susan da itaba, daga kano ya komo sokoto abinsa.
Sai Ya zamana zazzau ta fita daga ikon sarkin musulmi.
Sannan Gwamna Lugga ya aiko da wasika zuwa ga sarkin musulmi da Cewa:-
Bayan gaisuwa, Ka sani, idan shekara ta kewayo, zamu zo gareka, idan kana wurno zamu sauka a sokoto, idan kana sokoto kuwa zamu sauka a cikinta.
Sai sarkin musulmi ya juya takardar tasu ya maida jawabi da cewa
"La Haula Wala kuwwati Illa Billahi"
Ya aike musu dashi.
Sai dai bayan watanni 6 sai Allah yayi masa rasuwa, yana da shekaru 75 a duniya, yana kuma da shekaru 12 bisa mulki.
Kabarinsa na nan a Wurno.
Haka kuma Azamaninsa akayi basasar kano. Kuma a zamaninsa turawan Faransa suka kone Salame da dare, mutane suka firgita matuka.
Da fatan Allah yajikansa Amin.
Post a Comment (0)