UKU-BALA'I 29

UKU-BALA'I

NA

KAMALA MINNA

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.
 
BABI NA ASHIRIN DA TARA.

Cikin wani irin yanayi ta kai wayar kunnan ta sai faman jan numfashi take yi daƙyar idanuwanta sun kada sunyi jajir kamar an watsa mata barkono zuciyarta take ji tana mikata cikin wani irin waje mai dauke da tashin hankali mai girman gaske komai take ji ya tsaya mata cak! ji take yi kamar motar ta ta tuntsiran da ita ta mace ko ta huta da wannan tashin hankalin da kunar da zuciyarta ke yi tana babbaka duk wani sashi na kirjin ta ruhinta take ji yana wani irin fizga mai haifar mata da wani matsanan cin ciwo a dukkan sassan jikinta.
Girgiza kai take yi tana jin yarda yake wani irin sarawa da duk tashin hankalin da take ciki komai take ji a wannan lokacin yana barazana da duk ragowar farincikin da yayi sauya a gareta na filin duniyarta.
Ba ta san abin da ya sa ta fito yau ba bata san mai alkalamin ƙaddararta yake kokarin rubuto mata ba sosai take jin zuciyarta na haifar da wani kunci mai radadin gaske sosai take jin duk wani sashi na jikinta yake narkewa kamar ba na ta ba kafafuwan da suke kan giyoyin motar take jin su kamar ba a jikin ta suke ba ta tabbata da a tsaye take ba za su iya daukar gangar jikinta ba.
Nisawa tayi a daidai lokacin da taji iska mai nuna alamun an daga wayarta ta buso cikin kunnuwan ta runtse idanu tayi gami da tura laɓɓanta gabadaya cikin bakinta tana cizawa kamar zata fizgesu daga mazauninsu.
A hankali ta fara gangarawa gefen titin domin ba zata iya furta ko da kalma daya a yarda take jin zuciyarta ba, ba za iya motsa wani sashi na laɓɓanta a cikin halin tuki ba ji take yi kamar in ta motsa su komai zai tarwatse a gareta.
Sai da ta shafe mintina biyu kafun ta ja wani dogon numfashi ta fesar mai matukar ciwo.
"Alhaji Abdulwahaab".
Ta fadi can kasar makoshin ta kamar wacce akayi wa dole sai ta ambaci sunan.
"Na'am Areefa".
Ya ansa da yanayi na farinciki a muryarsa.
Runtse idanu tayi kafun ta sake jan numfashi.
"Kana ina Please I need your help right now?".
Yanayin da take furta kalmar cikin sauti mai rauni ya sanya Alhaji Abdulwahaab yin sanyi sosai.
"What is wrong with you Areefa me ke faruwa dake ne naji muryar ki So Sad?".
"Kana ina right now Alhaji Abdulwahaab don Allah ina son ganin ka ko a ina kake ka fada min gani nan zuwa".
Sosai muryarta tayi rauni kamar zata fashe da kuka a hankali ta kai hannunta baki tana toshewa.
"Ok...Cool down Please yanzu haka ina Muhabbir Coffee daidai Alo-Vera Hotel ki zo nan ki same ni".
Ba ta ji ra abin da zai ce ba da sauri ta sauke wayar tana cilli da ita kan kujerar dake gefen ta wani wawan ribas tayi tare da juya akalar motar ta koma kan titin sosai ta hau hanya.
Zabga gudu take yi kamar wacce zata tashi sama ita akaran kanta ba ta san ta nayin sa ba zuciya ce kawai ke aikinta domin ba ta cikin hayyacita motoci da yawa sai dai su kauce mata domin sun lura ba ta cikin hayyacin ta cikin mintina kalilan ta hau titin da zai kai ta alo-vera Hotel kwanar da zata sha saitin W. I .WUSHISHI ESTATE. Sukayi a rangama da wata motar saura kadan su haye juna Allah ya tsagaita amma duk da hakan ta bugar wa mai motar fitilu har sun dan tsage hannu kawai ta daga masa alamun bashi hakuri ta shiga layin girgiza kai yayi mai motar don ya lura bata cikin hayyacin ta.
Tun kafun ta isa Muhabbir Coffee din tayo parking din motarta gefe guda ta fito cikin hanzari murfin motar ma da kafarta ta tura ta shiga sauri kamar zata kifa har tana turgudewa Allah ya taimaka bata je kasa ba.
Ta shiga Get din wajan ta shiga rarraba idanu can gefe guda ta hango shi yana dago mata hannu kamar wacce aka ingiza haka ta tafi tana isa ta tsaya kinkam! A tsaye tana mai da numfashi ta shiga nuna kanta da hannu kirjinta sai faman dagawa yake yi idanuwanta na juyawa kamar mai shirin zubewa a kasa da sauri Alhaji Abdulwahaab ya mike don ya lura bata cikin hayyacinta jakarta ya riko ya ajje kan Table din dake wajan kafun ya riko hannunta ya zauna da ita sosai gorar ruwan dake ajje a wajan ya murɗewa kai ya tsiyaya cikin Glass Cup ya mika mata kau da kai tayi cikin wani irin yanayi.
"Haba mana anshi ki sha ko kya samu sa'ida a zuciyarki".
"Bana tunanin ruwa zan yi mani wani amfani a halin da nake ciki a yanzu".
Ta fadi cikin wani irin yanayi tana daura hannayenta saman goshinta da take ji kamar zai dare gida biyƴ.
"Ki ansa ki sha Areefa ruwa zai miki abin da baki taba zato ba".
Ba ta bukatar surutu da yawa don haka ta anshi ruwan ta kai bakinta aiko sai gashi ta take ruwan gabadaya ta dire kofin da karfi har sai da ya tsage don wahala runtse idanuwanta tayi tana faman sauke ajiyar zuciya a hankali gumi ya karyo mata saman goshi idanuwanta a lumshe sosai taji wani sashi na zuciyarta da ruhinta sun yi sanyi kadan da ta sha ruwan.
Lokaci guda ta ware idanuwanta kan na Alhaji Abdulwahaab da yayi kuri yana dubanta nisawa tayi cikin fesar da wani zazzafan huci.
"Wai ni Dr.Erena yake so har yana ikirarin zai aure ni".
Ta fadi tana runtse idanuwanta zuciyarta take ji tana kartawa da wani irin tashin hankali mai girma wata irin tsana mai tsanani da take ji akan Dr.Erena take samun fili a zuciyarta tana kara hauhawa sosai take jin kalamansa na ansa kuwwa a kwanyarta da zuciyarta.
Da na sani take yi na zuwan Company yau da na sani take yi da har ta je Office din sa ta saurare shi dana sani take yi da har ta bari kunnuwanta su ka jiyo mata kalaman da suke kokarin tarwatsa mata zuciya.
Wasu hawaye ne masu tsananin dumi taji suna biyo fuskarta da sauri ta ware ido tana kai hannayenta tana taba su murmushi take saki mai tsananin ciwo kafun ta dubi Alhaji Abdulwahaab mamaki fal a zuciyarta da fuskarta murmushi taga yanayi har hakoransa na bayyana kafun ya mike kan kafafuwansa yana taku a hankali hannayensa goye a bayan sa.
Juyowa yayi ya dubi Areefa har lokacin murmushin bai kau ba sai ma kara fadada da ya yi dawo wa yayi ya zauna sosai yana daura kafa daya kan daya ya jawo Mug din Coffee yana kaiwa bakin sa da wani irin yanayi na nishadi sai da ya kurba sosai sannan ya dire ya daura hannunsa kan Table din yana dan kwankwasawa har zuwa lokacin idanuwansa na kan Areefa da tayi fakare tana dubansa a wani irin yanayi mai cike da mamaki da AL'AJABI mai girma gaske wanda ya kusan sanya zuciyarta tsalle sama. 
"wondefull Story".
Ya fadi yana mai girgiza kai cike da farin ciki kafun ya dora da fadin.
"Sosai da sosai naji dadin wannan ranar a daidai wannan lokacin da na samu daddadar lamari irin wannan How Comes na ce miki yau ce ranar farko da nake hango cinmma nasarata akan Dr.Erena".
Mikewa ya kuma yi kan kafafuwansa hannunsa rike da Mug din Coffee.
"Areefa ya kamata ace wannan lamarin ya samu nishadi a filin duniyar rayuwarki a yanzu...".
"Alhaji Abdulwahaabbb!!".
Areefa ta fadi cikin wani irin sauti mai haifar da ɗaci a saman zuciya tana mikewa kam kafafuwanta idanuwanta a warwaje tana dubansa ciki da kunci zuciyarta na wani irin zafi.
"Ban san mai yasa kake farin ciki da haka ba, Ban san mai yasa kake so nayi farin ciki da wannan lamarin ba, shin ka mance abin da ke tsakanani da Dr.Erena, shin ka mance abin da yasa na ke zaune a INUWA DAYA tare dashi, shin ka mance bani da makiyi a filin duniyar nan sam dashi, shin ka manta ba wanda na tsana duniyar nan na ke son na ga bayansa sama da Dr.Erena".
Runtse idanu tayi tana jan numfshi kafun ta ciji laɓɓanta tana dakune fuska.
"Alhaji Abdulwahaab ta ya ya ke zaton zan yi farin ciki, ta ya ya kake zaton ko hakorana zan bayyana a fili a dalilin wannan maganar haba mana Alhaji Abdulwahaab kayi tunani mana".
Ta karashe tana komawa saman kujera ta zauna hannayenta dukka biyu ta dafe kanta dasu wani irin yanayi take jin zuciyarta na haifa mata wanda take jinsa kamar kirjinta zai kama da wuta ya babbake duk wata halitta dake da gurbi a filin kirjin nata ba ta san mai yasa ma ta zo wajan Alhaji Abdulwahaab ba tayi tunani zai ce da ita wani abu akan wannan lamarin ba amma sai taga sabanin haka wai farin ciki yake yi har ma da dariya.
"Yaa Salam".
Ta fadi tana saukar da hannunta daya tana dafe kirjinta dake ji yayi mata wani irin nauyi mai girman gaske.
"AREEFA!".
Alhaji Abdulwahaab ya fadi da murya mai zurfi. Dago kai tayi ba tare da ta ansa shi ba illa ido da ta zuba masa.
"Wannan lamarin da ya faru nasara ce a tsakanin ni da ke".
Kau da fuskarta tayi jin zuciyarta na kara rura wutar zafin da take ji.
"Nasan zaki ji ba dadi amma wannan hanyar ita ce ta dace ki bi don cimma kudirin ki har ma da nawa".
Girgiza kai ta shiga yi tana yatsine fuska kafun ta mike kan kafafuwanta tana dubansa.
"Ina! wannan ba hanyar mafita bace Alhaji Abdulwahaab bana hango nasara ta a wannan hanyar".
"Don ya furta ya na son ki ko shine kike wa kallon rashin nasara?".
Ta gaji da sauraron kalaman sa domin ranta ya fara baci ba za ta iya cigaba da zama ta na sauraronsa ba.
Hannu ta saka ta janyo jakarta kafun ta dube shi.
"Tafiya zan yi nayi tunanin in na zo maka da maganar nan zan samu mafita a gareka domin cimma burinmu da KUDIRI ashe ba haka bane".
Ta karashe tana takawa kan kafafuwanta.
"Areefa".
Ya fadi yana mikewa da sauri ya isa gabanta yanayin sa ya sauya sosai yake jin tausayin Areefa sai dai wani abu guda yake hango wanda wannan hanyar ce kawai da suka samu ita ce dama da ya kamata ace sunyi amfani da ita kar su sake ta kubace musu.
"ki tuna Areefa kudina ya ansa da sunan muyi haɗaka wajan bude Company kudin da bana wa ba kudin Marayu wanda sam bani da hakki a cikin su kudin da suke zama masifa ga duk wanda ya cisu ya kamata ki tuna ba yarda za ayi na so bayar da gudun mawa ya cutar dake nima ina bukatar naga Dr. Erena ya shiga tashin hankali ina so naga Dr.Erena ya fada cikin halin masifa domin ba mutum bane mai tausayi ba mutum bane mai imani jahadi zakiyi sosai yaci zarafin mutane da ba su ji ba su gani ba sosai ya zalunci mutane wanda na tabbata har dake a ciki. AL'UMMA zaki taimakawa jama'a duniyar na zaki ceto daga fadawa komarsa damarki ce wannan lokacin ki ne wannan Areefa kiyi amfani da ita nasara na tare dake mutane da yawa za su shi miki albarka za suyi miki fata nagari za suyi miki addu'a ki gama da duniya lafiya na rokeki ke kadai ce zaki iya wannan aikin".
Komawa yayi ya zauna yana mai ajjiyar zuciya tausayin Areefa yake ji sosai a ransa ya sani dole taji ba dadi a ranta dole tashiga wani hali na tashin hankali
Amma kuma jahadi za tayi taimakon mutane za tayi ya sani Dr.Erena yana da hatsari Areefa kawai zata iya yin komai in tayi taka tsantsan ba tare da ya gano ta ba musamman yanzu da ya nuna yana sonta ya sani sosai hankalinsa zai karka akanta da komai na shi ya sani Dr.Erena bai iya son abu ba yana nuna maitarsa a fili kuma yana bi ko ta halin k'ak'a ne don ganin ya cimma burinsa akan abin da yake so.
Areefa da ta kasa tafiya tun lokacin da Alhaji Abdulwahaab ya fara bayaninsa gabadaya jikinta yayi sanyi sosai taji zuciyarta narkewa da wani irin rauni mai girma a hankali ta juyo ta dube shi kafun ta gyada masa kai shima kai ya gyada mata don bai gane in da ta dosa ba.
A hankali ta juya ta fara tafiya a jiki a sanyaye zuciyarta na shiga wani iri yanayi tana cakuda maganganun Alhaji Abdulwahaab a zuciyarta da kwakwalwarta har ta fice daga wajan ta isa inda ta ajje motarta tashiga sai da ta shafe mintina kanta akan sitiyari domin komai take ji ya tsaya mata cak! gabadaya taji duniyar tayi mata wani gin-girin-gim kafun ta yi wa Motar Key ta falle kan titi.
*******
A hankali ta turo kofar falon idanuwanta a rufe kadan saboda raɗaɗin da taji sunayi mata kamar jijiyoyin su zasu tsintsinke haka ta zuro kafa cikin falon tana mai ware idanuwanta baki daya tana kokarin gayyato natsuwa ko ya ya ne bata so Hajiya Layla ta san tashin hankalin da tashiga sosai da sosai bata so ta gane tayi kuka da idanuwanta bata so ta saka ita ma cikin tashin hankali don ta tabbata itama akwai abin da ke damun filin rayuwarta.
Nisawa take yi a hankali zuciyarta na kara matsewa wani irin yanayi mai girman gaske idanuwanta ta sauke a inda take tsammanin samunta kamar ko yaushe da ta maida wajan zaunin ta har in ita ba ta nan.
Hango tayi zaune ta zabga tagumi da hannu daya hannu guda m
Kuma rike yake da wani kwali wanda bata gama hakikance na mane ne ba amma zuciyarta ta buga lokacin da taga Hajiya Layla ta kura masa idanuwa ko kaftawa bata yi.
Kara ware idanuwa tayi tana fiddo su kamar wacce zata barsu su faɗo kasa nisawa take yi da wani irin yanayi ganin kwalin dake hannunta sosai ta tsorata tana sakin jakar dake hannunta tana faduwa kasa ba tare da ta sani ba kafafuwanta taji sun shiga rawa kamar za su kasa daukar gangar jikinta da sauri ta fara taku tana haɗe hanya har ta isa gareta ba tare da ta sani ba.
Hannu ta kai ta ansa kwalin cikin wani irin yanayi mai nuna alamun mamaki matuka gaya idanuwanta take yawatawa kan kwalin ba tare da tace kazil ba ta shiga bin Hajiya Layla da kallo wacce ita ma ansar kwalin da Areefa da tayi a hannunta shi ya dawo da ita hayyacinta ta shiga duban Areefa a daidai lokacin kwalla masu yawan gaske wanda suka jima tare a idanuwanta suka zubo ta shiga girgiza kai.
"Maama".
Areefa ta fadi da muryarta mai zurfi idanuwanta da tuhuma acikin su take dubanta tana mai gyada kai tana jin yarda zuciyarta ke kara matsewa da mamakin da bata yi zaton taddashi a gidan ba.
"Dama Da...ma ba ki dai...na baaa!".
Ta sake fadi muryarta na rawa kalmomin da take fadi suna rarrabuwa da junansu.
Wani kuka ne ya kufcewa Hajiya Layla hannu ta saka ta toshe bakin ta kafun ta shiga girgiza kai.
"A,a Areefa wallahi na daina ban sha yanzu kwata-kwata ko kaunar ta bana yi kisan nayi miki alkawari har gaban abada ba zan sake ba".
Girgiza kai Areefa ta shiga yi tana mai zubewa a wajan numfashi take ja dakyar zuciyarta na wani irin zafi da radadi kafun ta fesar da wani zazzafan huci.
"Haba mana Maama sau nawa za muyi maganar nan dake na fada miki illar wannan abun likitoci ma sun fada miki wanda suke k'irk'irarta ma sunyi nuni da cewa tana da illa ga rayuwar duk mai ta'amali da ita ya kamata ki san wannan ya kamata ki duba halin da kike ciki ya kamata ace kin ceto sauran rayuwarki da tayi saura a filin duniyar nan kina ji likita ya fadi ta fara baki matsala sosai wanda yace in ba daina wa kikayi ba to tabbas nan da dan lokaci kadan zaki rasa rayuwarki gabadaya ni kuma ba zan so haka ba Maama AKWAI ILLA a rayuwar shan taba tana da matukar hatsari ga duk mai rayuwa da ita kin sani kuma kinji a jikinki lokacin da kika kwanta rashin lafiya kin ga yanayin da kika shiga na tashin hankali da kyar da taimakon Allah ki ka samu kan ki sosai likitoci suka nuna miki dokoki da zaki bi sannan kiyi kokarin fidda sha'awarta a rayuwarki ko ganinta ki nisanta daga rayuwarki haba mana Maama me yasa haka me ya kawo kwallin taba cikin nan gidan?".
Areefa ta karashe cikin muryar rawa da son fashewa da kuka tasowa tayi ta iso gareta ta kama hannayenta ta rike su gam!. Tana mai a jiyar zuciya laɓɓanta take tura cikin bakinta tana cizawa a hankali.
"Me ya kawo kwallin sigari nan gidan Maama?".
Ta sake fadi idanuwanta na kawo kwalla kafun ta rintse idanu.
"Nayi dana sani a rayuwa ta nayi tir da rayuwar da nayi a duniyata duk a dalilin rashin 'yanci yau na ga illar rashin iyaye yau na ga illar haihuwata da kayi a titi ban san me nayi wa iyayena ba suka yasar dani suka tafi suka bar ni a titin Allah ban san mai yasa sukayi mani haka ba yanzu ga shi nan na rayuwa cikin rashin amfani na tashi cikin rashin 'yanci na rasa mai kwaɓata na rasa mai kula min da rayuwa har ya nuna min kuskure na rayuwata gabadaya ba tayi amfani a duniyar nan ba ni ban yi aure ba balle na samu zuri'ar da za su ji k'ai na ni ban yi rayuwar yanci ba rayuwar titi nayi wacce ba zan ce miki ga yarda na kasance a rayuwata a shekarun yarinta ta ba".
Nisawa tayi wasu hawaye suka zubo mata kafun ta cigaba da fadin.
"kawai na yi rayuwa ce a yarda ta zo mani a yarda Alkalamin kaddara ya zana min wani fannin kuma da nawa kason na lalacewar rayuwata ban san dadin iyaye ba ban san su waye iyaye ba ban san ya yaro yake ji a wajan iyayen sa ba ban san wacce irin kauna ce da ake fadi ana ji a wajan UWA DA UBA ba iyayena sun kasance ne bakin titi da wajan masu abincin saidawa nan ne suka kasance jigon rayuwa ta su ne suka kasance iyaye a gareni har lokacin da na dauki kazamar rayuwa da nake zaton ita ce mafita a gareni na daura a duniya ta".
runtse idanu tayi tana jin yarda kirjinta ke harbawa da duk wani ɗaci gami da zafi a ranta.
"Areefa na daina shan sigari tun da nayi miki alkawari yau ma fita nayi aka zageni aka tsine mani har ake kokarin marina akan sigari wai don kawai nace na daina yaro karami wanda in a haife ne na haife shi in jika ne ma zan iyayi dashi amma akan abin banza abin Allah wadai ya zage ni yana jifana da kwalin sigari dake hannunsa Yaa Allah wannan wacce irin rayuwa ce Areefa nayi dana sanin rayuwa a duniyar nan".
Wata irin zabura tayi idanuwanta a warwaje hannayenta saman kirjinta.
"Maama zagi fa kika ce waye ya zage ki fada min waye shi na nuna masa ke ma kina da gata a rayuwarki rashin iyaye ba hauka bane zan nuna masa kina da gata kuma kina da 'ya a filin duniyar nan da ta san darajar ki da kimarki ki fada min shi please Maama".
Cikin sauti take maganar kamar wacce ta fice daga hayyacin ta da sauri Hajiya Layla ta mike ganin Areefa na kokarin ficewa daga gidan sosai ta rikota ta zauna da ita tana mai kwantar da ita a jikinta tashiga shafa mata baya a hankali har zuwa lokacin idanuwanta na zubda hawaye masu tsananin zafi da take ji kamar za su keta mata duk wani sashi na kirjinta.
"ki bar komai na yafe masa rayuwa ce ta zo da haka inda ban yi harkar shan sigari ba ba yarda za ayi ya tare ni a hanya har ya ci mani mutunci in ba don ya ga alamun nayi shaye shaye ba a zamani na ba yarda za ayi ya dube ni yace na bashi sigari komai ya faru ni ce sanadi ni ce sila Areefa ki bar komai na yafe masa".
Da sauri ta dago kanta tana duban Hajiya Layla da take shafe hawaye.
"Haba mana Maama hawaye fa ya sakaki zubdawa akan mi zaki ce a bar shi bayan ya ci miki mutunci".
"ki bar shi nace kawai ki bar shi komai ya wuce a wajena har a zuciyata na yafe masa fata na Allah ya shirye shi ya sa daga kaina ya daina abin da yake yi domin na lura illar shaye-shaye yawa gareta ba abin da ba zata iya sanya wa ka aikata ba wanda zai cutar da rayuwarka sosai AKWAI ILLA sosai da sosai".
Ta karashe tana mai kalato murmushi tana daurawa a fuskarta domin kwantarwa da Areefa hankali domin bata so ta sake sanya rayuwarta a damuwa nan ta shiga bubbuga bayanta domin kwantar mata da hankali.
Wani numfashi a Areefa taja mai tsayi kafin ta saki ajiyar zuciya.
"Maama ke dama baki da iyaye dama ke ma marainiya ce kamar ni".
"Ya isa haka Areefa mu bar wannan zance haka ba shi da amfani".
Ta katse ta da wani irin yanayi da ta ji zuciyarta na shiga da tashin hankali mai girma.
"Mai ya dawo dake wannan lokacin ba tare da lokacin tashi ya yi?".
Ta fadi domin kau da zancen da Areefa ta dauko.
Da sauri ta tashi zaune tana duban idanun Hajiya Layla kafun taji wata irin tsanar Dr.Erena ta sake samun fili mai girma a zuciyarta a hankali ta shiga cizon laɓɓanta tana runtse idanu.
"Dr.Erena Maama".
Ware idanu tayi kafun ta mike tsaye tana kai kawo a tsakar falon lokaci guda ta tsaya cak! fuskarta ta kara cakuɗewa da bacin rai mai girman gaske.
"Ba dai kin yi sake ya gano ke wa ce ce ba in kuwa haka ne komai zai wargaje mana".
"A,a Maama wai cewa yayi yana sona har cewa yayi zai iya aure na in har na yarda dashi".
Zare idanu tayi waje bakin ta na buɗe ta iso ta zauna tana janyo Areefa jikinta gami da sarke hannayensu waje guda wani murmushi na takaici ta sako kafun ta dubi Areefa sosai da tayi fakare tana dubanta ganin abin da ke fuskarta.
"Lokaci ya zo Areefa lokacin da nake dako ne Allah ya kawo mana shi tabbas lokaci ne ya zo tsakanimu da Dr.Erena".
"Ban gane ba Maama?".
Areefa ta fadi a dan tsora ce tana kwace hannayenta daga cikin na Hajiya Layla.
"Karki damu kawai ke dai ki kwantar da hankalin ki ki cigaba da zuwa aiki karki sake ko da wasa ki nuna masa baki amince ba sannan gobe karki sake ki ce ba zaki office ba ki shirya ki je ki bar komai a hannu na".
Cikin rashin fahimta da kara bayyanuwar mamaki ta shiga motsa laɓɓanta tana kokarin yin magana amma Hajiya Layla ta hana ta tana mai cewa.
"Maza ta shi ki je ki watsa ruwa ki ci abinci ki huta kafin lokacin Sallah yayi".
Ba musu ta mike zuciyarta da wani irin AL'AMARI wanda ta kasa gane kansa sosai kanta ya kulle sosai taji tunanin ta ya kasa buɗe mata wannan lamari wanda ya jefata a duhu sosai da sosai haka ta ja jiki tana duban Hajiya Layla har ta isa dakinta.
Mikewa Hajiya Layla tayi tana kai kawo cikin falon hannayenta take hadawa waje daya tana bugawa wani irin yanayi take ji a jikinta sosai taji dadin maganar nan da Areefa ta fadi mata komai take hangowa ya canza sosai take hango nasara a tsakanin ta da Dr.Erena za ta nuna masa ita wacece kuma za ta nuna masa mace ma daraja gareta a duniyar nan ba kamar yarda ya dauka ba...


 *_KAMALA MINNA_*😍😍😍


Post a Comment (0)