ITA TA KAI KANTA

ITA TA KAI KANTA
{Kurma mai ciki}

Wata kurma ce Allah Ya Jarrabe ta da masifar son aure kamar ta kai kanta gidan miji. Ana cikin haka ta sami saurayi suka kulla soyayya har Allah Ya nufe su da aure,bayan tarewa ba da jimawa ba sai Allah Ya ba amarya kurma ciki,tun ba'a je ko'ina ba ta fara laulayin ciki amaye-amaye zazzabi da ciwon kai tabi duk ta rame da kyar dai har lokacin haihuwa yayi, Kurma dai ta haihu a daddafe taji irin abin da 'Yan'uwa mata keji wurin haihuwa,akai suna ta tafi gida wanka bayan ta gama wanka akai-akai ta dawo tace bata komawa ta sake shan irin wannan wuya, karshe dole sai dai auren ya mutu.
Yanzu haka zancen nan da nike da ku kurma na nan gida kememe taki aure kwata-kwata sai dai kawai in an ce mata zo muje barka wance ta haihu ta tambaya ''Haihuwar farko ce koko bata farko bace? In ance ta fari ce sai tace''WAYYO BA TA SANI MUJE AI MATA BARKA'' Inko taji ba haihuwar fari bace sai tace''BANI ZUWA ITA TAKAI KANTA''
Nima ina jin labarin na bushe da dariya sannan nace''KURMA KEMA KE KIKA KAI KANKI''ehe.
Post a Comment (0)