DARUSSAN RAYUWA DAGA JARUMI SHAH RUKH KHAN
Kashi Na É—aya 04
Fitowa Ta Shida 06
Daga Haiman Khan Raees
Bismillahir Rahmanir Raheem.
Barkan Mu da Warhaka.
A wannan fitowa kuma zamu kawo muku Darussan da suka fito ne kai tsaye daga cikin Kalaman Fina Finan Jarumin. Ga su kamar haka:
1. Dare hue log aksar alfazon ke peeche chupte hai.
Mutanen da suke matsorata ne sau da yawa su kan É“oye ne a bayan Kalamai.
AE DIL HAI MUSHKIL
2. Duniya mein kitni hai nafratein ... phir bhi dilon mein hai chahatein ... mar bhi jaaye pyar waale ... mitt bhi jaaye yaar waale ... zinda rehti unki Mohabbatein
Ƙiyayya tayi yawa a cikin duniya ... Amma duk da haka akwai so a cikin zukata ... Ko da ace mutanen da kake so sun mutu, ko kuma abokan ka sun ɓace ... Son su zai kasance a raye.
MOHABBATEIN
3. Babuji ne kaha gaon chhod do ... sab ne kaha Paro ko chhod do ... Paro ne kaha sharab chhod do ... aaj tumne keh diya haweli chhod do ... ek din aayega jab woh kahenge, duniya hi chhod do
Baba na cewa in bar gari ... Kowa na cewa in rabu da Paro ... Paro na cewa in bar shan giya ... Yau kuma kun ce in bar gidan gaba É—aya ... Watarana zata zo da zaku ce mutum ya bar duniyar ma kanta.
DEVDAS (2002)
4. Kabhi kabhi jeetne ke liye kuch haarna bhi padta hai ... aur haar kar jeetne waale ko baazigar kehte hai
Wani lokacin kafin ka samu nasara sai ka rasa wani abu... Shi kuwa mai cin nasara daga jikin rashin Nasara shi ake kira da ÆŠan Kasada/Mai Nasara.
BAAZIGAR
5. Pyar dosti hai ... agar woh meri sab se achchi dost nahin ban sakti, to main usse kabhi pyar kar hi nahi sakta ... kyun ki dosti bina toh pyar hota hi nahin ... simple, pyar dosti hai
Abota ita ce soyayya ... Idan ba zata iya zama babbar ƙawata ba, to ba zan iya kamuwa da Son ta ba... Saboda so ba ya taɓa ginuwa sai da ƙawance... A sauƙaƙe, Abota ce so.
KUCH KUCH HOTA HAI
6. Main aaj bhi usse utni hi mohabbat karta hoon ... aur is liye nahi ki koi aur nahi mili ... par is liye ki usse mohabbat karne se fursat hi nahi milti
Har yau son da na ke mata bai canza ba ... Ba wai don ban samu wata ba ... Sai don bani da lokaci bayan soyayyar ta.
MOHABBATEIN
7. Itni shiddat se maine tumhe paane ki koshish ki hai ... ki har zarre ne mujhe tumse milane ki saazish ki hai
Na yi Muradin ki sosai kuma da gaske... Ta yadda duniya ma gaba É—ayanta ta goyi bayana domin na same ki.
OM SHANTI OM
8. Aaj ... aaj ek hasi aur baant lo ... aaj ek dua aur maang lo ... aaj ek ansoon aur pee lo ... aaj ek zindagi aur jee lo ... aaj ek sapna aur dekh lo ... aaj ... kya pata, kal ho naa ho
Yau ... Yi murmushi yau ko da sau ɗaya ne ... Ƙara Yin Du'a'i yau ko da sau ɗaya ne ... Sha hawaye ko da sau ɗaya ne yau ... Rayu ayau ko da sau ɗaya ne ... Kalli ko da mafarki ɗaya ne yau ... Yau ... Wa ya sani, ko gobe ba zata zo ba.
KAL HO NAA HO
9. Yadhaash bhi kitni ajeeb cheez hoti hai ... kis cheez ko poori zindagi bhoolne ki koshish karo, woh bhoolti nahi ... kabhi ek choti si cheez yaad karne ki koshish karo, toh yaad nahi aati
Tunani wani irin abu ne mai wuyan sha'ani ... Yayinda kake so ka manta da wani abu a rayuwar ka, sai ka kasa mantawa ... Kuma idan ka so ka tuna wani abu ɗan ƙarami sai ka kasa tunawa.
JAB TAK HAI JAAN
10. Mohabbat mein shartein nahi hoti ... toh afsoos bhi nahi hona chahiye
Babu wasu SharuÉ—É—a a soyayya ... Don haka babu batun neman afuwa
MOHABBATEIN
11. Roti ke bina insaan chaar hafte jee sakta hai, pani ke bina chaar din aur hawa ke bina shayad chaar minute ... lekin umeed ke bina insaan chaar second bhi nahi jee sakta hai
Mutum na iya sati huɗu ba tare da abinci ba, kwana huɗu ba tare da ruwa ba, watakila ma ya iya mintuna huɗu ba tare da iska ba ... Amma mutum ba zai iya yin daƙiƙa huɗu ba tare da buri ba
HAPPY NEW YEAR
12. Dil toh har kisi ke paas hota hai ... lekin sab dilwale nahi hote
Kowa yana da Zuciya ... Amma ba kowa ke da ƙarfin zuciya ba.
DILWALE (2015)
13. Joh dhande ke liye sahi woh sahi ... joh dhande ke liye galat woh galat ... isse zyada kabhi socha nahi
Duk abinda ya dace da kasuwanci ya dace ... Duk abinda bai dace da kasuwanci ba bai dace ba ... Ban taɓa tunanin wani abu bayan haka ba.
RAEES
14. Dosti ke alava bhi kuch rishtey hote hai ... kuch rishtey joh hum samajhte nahi ... kuch rishtey joh hum samajhna nahi chahte ... kuch rishtey jinka koi naam nahi hota, sirf ehsaas hota hai ... kuch rishtey jinki koi deewar nahi hoti, sarhad nahi hoti ... aaise rishtey joh dil ke rishtey hote hai, pyar ke rishtey hote hai, mohabbat ke rishtey hote hai
Akwai wata dangantaka bayan ta abokai... Wata dangantakar mun Fahimce ta... Wata kuma bama so mu Fahimce ta... Wata dangantakar bata da suna, jin ta kawai ake yi... Wata dangantakar bata da Katanga, bata da iyaka... Dangantakar da ke zuci kenan, dangantakar soyayya kenan, dangantakar ƙauna kenan.
KABHI KHUSHI KABHIE GHAM
15. Duniya mein do tarah ke log hote hai ... winners and losers ... lekin zindagi har loser ko woh ek mauka zaroor deti hai ... jis mein woh winner ban sakta hai
Mutane iri biyu ne a cikin wannan duniyar... Masu nasara da marasa nasara... Sai dai rayuwa ta kan baiwa mara nasara damar samun nasara... Ta yadda shima zai iya zamowa mai nasara.
HAPPY NEW YEAR
16. Sachi mohabbat zindagi mein sirf ek baar hoti hai ... aur jab hoti hai ... toh koi bhagwan yah khuda usse nakamyab nahi hone deta
So na Gaskiya sau É—aya yake Faruwa a rayuwa... Kuma idan ya auku... Ubangiji na sa shi ya zama tabbatacce.
VEER-ZAARA
17. Tumhare paas joh hai tumhare hisaab se kam hai ... lekin kisi doosre ke nazar se dekho ... toh tumhare paas bahut kuch hai
Abinda ka/kike da shi ƙadan ne a wajen ka/ki... Amma in ka/kika kalli abun ta idon wani... Abinda ka/kike da shi yana da yawa sosai.
KAL HO NAA HO
18. Kuch kaam aaise hote hai jin mein fayda yah nuksaan nahi dekha jaata ... bus unhe karna zaroori hota hai
Akwai abubuwa ƙalilan waɗanda baka duban riba ko rashin riba a cikin su... Kawai sun zama dole ne ka aikata su.
DON (2006)
19. Agar tum galat raaste par chaloge ... toh ho sakta hai shuruvat mein tumhe bahut kamyabi mile, bahut khushiya mile ... magar anth mein tumhari haar hogi ... aur agar sahi raaste par chaloge ... toh bhale hi shuruvat mein tumhe kadam kadam par thokarein mile, musibaton ka samna karna pade, pareshani ho ... magar anth mein hamesha jeet hogi
Idan kabi hanyar da bata dace ba...
Wataƙila daga farko zaka dinga samun nasara da farinciki... Amma a Ƙarshe ba zaka yi nasara ba... Kuma idan kabi hanyar da ta dace... Wataƙila da fari zaka fuskanci ƙalubale da cin fuska ta kowace ƙusurwa, zaka fuskanci matsala da Jimirɗa... Amma a Ƙarshe kai ne zaka yi nasara.
DILWALE DULHANIA LE JAYENGE
20. Zindagi mein agar kuch banna ho, kuch haasil karna ho, kuch jeetna ho ... toh hamesha dil ki suno ... aur agar dil bhi koi jawab na de toh aankhen band karke apni maa aur papa ka naam lo ... phir dekhna har manzil paar kar jaoge, har mushkil aasaan ho jayegi ... jeet tumhari hogi, sirf tumhari
A Rayuwa idan har kana so ka zama wani abu, ko ka samu wani abu, ko ka cimma wani abu, ko ka yi nasara akan wani abu... To ka kasance mai sauraron zuciyar ka a koda yaushe... Kuma idan zuciyar ka bata baka amsa nan da nan ba to ka rufe idanunka ka ambaci sunan mahaifiyar ka da mahaifin ka... Daga nan ka sa ido ka gani yayin da zaka samu nasara akan komai, duk wani abu mai wahala zai zamo mai sauƙi... Nasara zata zamo taka... Taka kawai
KABHI KHUSHI KABHIE GHAM
Na barku lafiya sai kuma mun sake haÉ—u wa a cikin wani sabon rubutun.
<••••••••••••••••••••••••••••>
Hãïmâñ Khãñ Řăééş <••••••••••••••••••••••••••••>
08185819176
Twitter: @HaimanRaees
Instagram: Haimanraees
Infohaiman999@gmail.com