*_SIFFAR WANKAN JANABA_*
*Tambaya*
Don Allah malam ina so a siffanta min yadda ake yi wankan janaba, saboda ban jima da zama mutum ba!
*Amsa*
To dan'uwa janaba wani hukunci ne da yake faruwa saboda daya daga cikin abubuwa guda biyu: ko dai mutum ya yi mafarki kuma ya ga maniyyi, ko kuma mutum ya sadu da matarsa, duka wadannan suna wajabta wanka Game da siffarsa kuwa, to wankan janaba yana da siffofi guda biyu, duk wacce ka dauka ta yi:
1. Siffar da ta fi kamala ita ce wacce ta zo a hadisin A'isha cewa manzon allah S.A.W. idan ya zo wankan janaba yana farawa ne da wanke hannunsa, sannan sai ya wanke farjinsa da hannun hagu, sai kuma ya yi alwala amma ban da wanke kafa, sannan sai ya debi ruwa sau uku ya zuba a gashinsa, bayan haka sai ya zuba a ragowar jikinsa, sannan sai ya wanke kafarsa. Bukari da muslim.
2. Akwai kuma siffa ta biyu wacce ta zo a hadisin Ummu-salama lokacin da Annabi S.A.W yake siffanta mata wankan janaba, inda yake ce mata: "Ya ishe ki ki zuba ruwa sau uku a kanki, sannan ki zuba a duka jikinki, mutukar kin yi haka to kin tsarkaka" Muslim ne ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 330.
Allah ne mafi sani.
07/03/2014
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
___________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.

A siffa ta biyu ba sai an tsaga jiki gida biyu bah kenan ko farawa da dama sannan hagu?
ReplyDeleteKawai watsa ruwa zanyi ta ko ina
Eh hakane
Delete