DARUSSAN RAYUWA DAGA JARUMI SHAH RUKH KHAN 03

 DARUSSAN RAYUWA DAGA JARUMI SHAH RUKH KHAN

Kashi Na ɗaya 02

Fitowa Ta uku 03

Daga Haiman Khan Raees

Bismillahir Rahmanir Raheem.

Barkan Mu da Warhaka.


Kamar yadda na sanar a cikin rubutu na da ya gabata cewa a fitowa ta biyu zan taɓo Darussan da ke cikin Fina Finan Jarumi Shah Rukh Khan, to Alhamdulillahi gashi Allaah Ya amince min. A ƙalla daga farkon fara aikin sa zuwa yanzu jarumin ya fito a cikin Fina Finai sama da 80, don haka ba dukkan su ne zan yi magana a kansu ba, zan taɓa waɗanda Allaah Ya bani iko ne kawai.

1. DILWALE DULHANIA LE JAYENGE:
Daga cikin fannonin da Jarumi SRK ya ƙware a fagen su akwai fahimtar yanayin motsin jiki da Ma'anar sa watau body language kenan. Mun ga misalin hakan a cikin Fim ɗin DDLJ, in da ya tsammaci cewa yarinyar da yake so zata waigo bayan ta tafi kuma hakan alama ce na tana son shi. Kuma a wajen Raj Malhotra, kwalliya ta biya kuɗin Sabulu.
Sannan Kamar dai Raj, in dai har ka san ka faɗa soyayya to kada ka sake ka bar abinda kake so ya tsere maka. Kayi iya yinka wajen ganin ka tabbar cewa abin nan da kake so bai kufce maka ba, kada ka sake ka karaya. Sai dai kuma fa, yayin da kake neman wannan abu da kake so, ka kula kada ka cutar da ahalin ka.

2. SWADES: A cikin Fim ɗin Swades, bayan nuna tsantsar kishin ƙasa da jarumin yayi, ya kuma koya mana Darasin aikin gayya tare da miƙewa kayi aikin da kake buƙata iya ƙarfin ka, ko da kuwa babu wanda ya shirya yi maka.

3. CHAK DE! INDIA: A cikin wannan Fim Jarumi SRK ya bayyana Ma'anar YI KO KA MUTU a wani irin yanayi na musamman ta hanyar nunawa ɗaliban sa muhimmancin lokaci, yin aiki da lokaci da kuma yin abinda ya dace a cikin lokacin da ya dace.

4. KUCH KUCH HOTA HAI: Anan kuma jarumin ya nuna mana muhimmancin abota ne da yadda soyayya mai Ƙarfi ta ke gudana a cikin jinin abokai, ko dai a zahirance ko kuma a baɗini. Kamar dai yadda ya ce: "Pyaar dosti hai".
"Love is friendship, friendship is love". Ma'ana dai so yake anan ya nuna mana cewa abota ne matakin farko na soyayya.

5. DEAR ZINDAGI: A cikin wannan Fim, jarumin ya bayyana mana yadda tarayya ke Wanzuwa tamkar Kujera. Kujera ta kan zo a mataki iri daban-daban a kuma zubi iri daban-daban, kana iya jaraba kowacce, amma ka tabbata cewa ka zauna akan wacce ta fi maka daɗin zama.

6. RAB NE BANA DI JODI: A cikin wannan Fim, SRK ya koya mana cewa sirrin samun daddaɗan kuma dogon zaman lafiya a rayuwar aure duk ya ta'allaƙa ne wajen Sadaukarwa tare da maida komai ba komai ba. Ya sadaukar da gashin bakin sa, saka matsattsun kaya, ƙona gashi, koyon wasa da mashin, lokacin sa, Dukiyar sa da kuma abu mafi wahala shi ne ɗaukar Darasin rawa, duk don ya farantawa Masoyiyar sa. Sannan kuma yana koyar da mu cewa akwai dalilin faruwar duk wata zamantakewa da gani, domin nufin Allaah ne.

7. BAAZIGAR: Kabhi kabhi kuch jeetne ke jiye kuch haarna bhi padta hai. Aur haar ke jeetne wale ko Baazigar kehte hai ." No risk, no reward -- Jarumi SRK ya tari Aradu da ka ta hanyar gwamutsa soyayya da ɗaukar fansa a lokaci guda kuma yayi nasara daga Ƙarshe, hakan yana koya mana cewa, Matuƙar da gaske muke yi, to zamu iya bugun Jaki kuma mu bugi Taiki a lokaci guda ba tare da an ankare ba.

8. KAL HO NAA HO: Ba abu bane mai sauƙi ka iya karanta Zafafan Kalaman soyayya daga cikin fankon kundi, musamman a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci. Abu ne mai Matuƙar wahala, amma kamar yadda yayi, a duk lokacin da kake buƙatar shawo kan wani lamarin soyayya domin farantawa abokin ka, yi maza ka buɗe littafin SRK, ka kalle ta da kyau sannan ka furta wani kalami mai nagarta kuma har cikin zuciyar ka kamar haka: ' Main aankhen bandh karta hoon toh tumhe dekhta hoon. Aankhen kholta hoon toh tumhe dekhna chahta hoon.
Sannan shirin ya koya mana cewa ita fa rayuwa ɗaya ce, mu tafiyar da ita da iya bakin iyawar mu a kullum. Mu Rayu, mu so juna, muyi dariya sobada kowane yini yana da amfani, ka Rayu kamar yau ce ranar ka ta Ƙarshe domin baka san me zai faru gobe ba.

9. CHALTE CHALTE: A zamantakewa irin ta aure dole ne a samu rashin jituwa watarana, amma kada ku bari hakan ya ɓata muku zamantakewar ku. Kada ku bari son zuciya ya hana ku ganin gaskiyar abokan zaman ku, kada kuma ya hana ku ganin laifukan ku. Ku fahimci cewa kuna iya yin dai dai kuma kuna iya yin kuskure a koda yaushe. Wannan shi ne saƙon wannan Fim.

10. DIL TO PAGAL HAI: A cikin wannan Fim, jarumin ya koya mana Darasin cewa mu yarda da haɗi daga Allaah. Wasu mutanen dama an halicce su ne domin su kasance tare da junan su, wasu kuma akasin haka. Ko kai ɗan ba ruwana ne kamar Rahul, ko kuma ke mace ce mai gaskiya kamar Pooja, Allaah Ya riga ya tanadar maka da abokin zaman ka tun gabanin wanzuwar ka. Abinda kawai ya kama ce mu shi ne mu yarda cewa, Matuƙar lokaci yayi, to zamu haɗu DA wannan zaɓin ta kowane hali.

Zan Ci Gaba In Shaa Allaah

<••••••••••••••••••••••••••••>
  Hãïmâñ Khãñ Řăééş <••••••••••••••••••••••••••••>
 08185819176
Twitter: @HaimanRaees
 Instagram: Haimanraees
 Infohaiman999@gmail.com


Post a Comment (0)