FA'IDA: SAUƘAƘA AURE SHI KE SA YAYI ALBARKA BA TSANANTAWA BA

FA'IDA: SAUKAKA AURE SHIKE KAWO ALBARKA, BA TSANANTAWA BA

Shaikh Uthaimin (Allah yayi masa rahama) a wata risalar da mai suna 'azzawaaj' (Aure), ya ambaci haka, yayin da yake magana akan saukaka sadaki, inda yake cewa:

(... Da mutane zasu takaita su saukaka a sadaki, suyi taimakekeniya a cikin sa, waliyyai da majibinta aure su fara zartar da hakan, da an sami alkhairi mai girma a cikin al'umma tare da kwanciyar hankali, da katange da yawa daga cikin maza da mata.
Sai dai abun bakin cikin shine, yadda mutane suke rigegeniya wajen kara tsadar sadaki, da tsananta shi, sai kaga duk shekara suna kara wasu al'amura wadanda a da can baya ba'a san dasu ba. Bamu san kuma har zuwa ina ne za su tsaya da kare-karen nasu ba).

Risalatuz Zawaaj: 39.
Post a Comment (0)