YADDA AKE DAMBUN KUSKUS

*TAURARIN MATA GROUP*

🌟🌟🌟🌟🌟🌟
🌟🌟
*DAMBUN KUS-KUS (COUSCOUS)*

*kayan hadi :*

🌷Couscous
🌷Zogale
🌷Carrot
🌷Cabbage
🌷Gyada
🌷Mai
🌷Attaruhu ko Tattasai
🌷Albasa
🌷Tafarnuwa
🌷Maggi

*YADDA AKEYI:*

```Da farko zaki samu couscous dinki saiki jika shi na kamar minti 7,idan ya jiku saiki tace ruwan ya tsane,saiki samu steaming pot dinki,ko abinda kikeyin danbu,saiki dauko zogalenki,gyada,carrot,cabbage,maggi,curry,nama da attaruhu da albasarki da ki yayyanka su sai ki zuba ki juya da sauran spices din da zaki saka ki hada akan couscous din ki juya sosai ko ina yaji,
sai ki kawo ruwan dumi ki yayyafa da Mai sai ki zuba a madanbaci ko steamer ki dora a wuta ki bashi minti30 zaki ji yana kanshi kuma zaiyi laushi,idan yayi laushi saiki sauke sai zuba ci😋😋😋```

*ZY MARIAM TIJJANI ADAM*
Post a Comment (0)