FATALWAR SINU 05

""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""
              FATALWAR SINU 05
""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""
              A Short Story
""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""
       FINAL EPISODE

✹••✹••✹••✹••✹••✹••✹
     ʂɬơrყ/wrıɬɛɛŋ   
            ɮʏ✍🏻:

👉🏻© ɧãımãŋ Kɧâŋ Řâééʂ ✹••✹••✹••✹••✹••✹••✹

Na san cewa wasu daga cikin ku zasu ce: ina Haiman! Ai Sam kada ka damu sun zo ne domin su taimake ka daga hannun SINU da mugyambo, blah blah blah! Erm.. Nagode da irin wannan kyakyawan tunani naku a gareni, amma kamar yadda na faɗa muku a baya, rashin sa'ata ya kai maƙura. Ina nan tsaye ina kallon su tare da jiran ganin abinda zai faru, ai kuwa ban daɗe ba ina wannan jira sai naga Shah Rukh Khan ya rikiɗe izuwa Siffar G.ONE Yayinda shi kuma Rajnikanth ya juye izuwa Siffar Chitti. Kafin kace me ke faruwa tuni sun kacame da faɗa. A'a! Kamar wasa fa, kawai sai naga Salman Khan da Surya suma sun koma gefe suna nasu, can kuma sai na hango Aamir Khan da NTR suma sun ja daga suna sambaɗar juna. Nan fa kowa ya fara jan daga da abokin karawarsa. John Abraham da Prabhas suka tari juna, Ram Charan da Tiger Shroff, Allu Arjun da Hrithik Roshan, Vijay da Arjun Rampal, Vidyut da Sanjay Dutt. Haka dai kowane Jarumi da abokin karawarsa, shi Abhishek Bachchan ko me ya kai shi tarar Mahesh Babu oho, zuwa ɗaya Mahesh yayi mai sai gashi yana aman jini. Can gefe kuma naga Anil Kapoor da Ajith Kumar suna tasu fafatawar, Yayinda Govinda da Chiranjeevi suma suka ja daga. Ana haka kuma sai naga wajen ya ƙara yin duhu, kafin in ankara kuma sai ga jarumai Mata suma suna durowa. Nan take suma suka fara nasu artabun, Kangana da Anushka Shetty suka tarbi juna aka fara fafatawa, Katrina da Tamannah suma suka buɗa, Anushka da Samantha suka ja gefe, Kajal kuma sai ta tarbi Priyanka. Haka dai suma suka ware suka dinga ribzar juna kamar tumun dawa.

Nayi Matuƙar mamakin ganin wannan abu da ke faruwa, can daga baya kuma sai na tuna, sama da shekaru uku da suka gabata wani ƙazamin tunani ya taɓa zuwa min a raina har na dinga riyawa ina ma ace Jaruman kudanci da na arewaci za su yi wani gagarumim shiri wanda za'a caskale a cikin sa? To gashi yanzu yana faruwa a gabana ina gani. To tayaya aka yi har SINU yasan da cewa na taɓa yin wannan tunani? Daga nan sai nayi tunanin in raba su mana, don haka sai na nufe su ina mai basu haƙuri, ni gashi baki ya toye babu damar yin magana, garin bada haƙurin ma ni aka mazge ni na faɗi kasa na fasa kai na kasa tashi. Ina nan kwance sai na fara jin ƙaraji, gunji gami da ihun jarumai, da ƙyar dai na lallaɓa a hankali na tashi zaune. Ai kuwa nan take hwnkalina ya ƙara tashi, ba komai ne ya jawo haka ba face ganin cewa duk yawan Jaruman nan mutum huɗu kawai suka rage a filin dagar, sauran daga waɗanda suka mutu sai kuma masu kakarin mutuwa. A ɓangaren maza Jarumi Hrithik Roshan da Prabhas ne kaɗai suka rage a tsaye suma kuma kowanensu ya samu muggann raunuka a jikin sa. A ɓangaren mata kuma Jaruma Anushka Shetty ce tare da Kangana Ranaut suka rage. Nan fa suka yi cirko-cirko kamar zakaru, da alama dai wani sabon faɗa zasu sake yi. Lallai ya zama dole in san abin yi, to me ya kamata in yi? Me zan yi ya jawo hankalin SINU kaina?

Can kuwa sai wata dubara ta faɗo min, don haka sai na yanke Shawarar faɗawa fagen dagar. Na miƙe a sanyaye jiki ba Ƙarfi na nufi wajen matattun domin samun makami, cikin sa'a kuwa sai nayi karo da gawar NTR, hannunsa riƙe da wani ɗan matashin gatari wanda aka yiwa azargiya da wata sarƙa, cikin azama na finciki gatarin tare da yin kan Jaruman ba tare da shakkar komai ba ina zuwa kawai sai na fara kai Sara ta ko'ina da gatarin, bisa sa'a zan ce ko rashin sa'a oho, kai saran da nayi na farko kuwa sai gashi na fille kan Kangana, aifa nan take sai sauran ukun suka yo kaina suka rufe ni da duka. Kafin in ankara, tuni sun haɗa min jini da Majina, daga nan na faɗi matacce ne ma ko sumamme ne ban sani ba.

Bayan wani ɗan lokaci sai na Farfaɗo, bisa mamaki sai na jini na dawo daidai, bakina ya warke sumul kamar ban taɓa jin wani ciwo ba. Nan take kuwa na miƙe tare da nufin kawo ƙarshen wannan lamari ko ta halin ƙaƙa. Miƙewa ta ke da wuya kuwa sai na ga SINU a zaune akan wata jar kujera, yayi kinini da fuskar nan kamar markaɗe yaso gardama. Ko da naga haka sai na buɗi baki nace: "ina sauran Jaruman?" maimakon ya bani amsa, sai ya ƙara fusata, jikin sa ya fara wani tiririn harzuƙa, kafin in ankara kawai sai gani nayi wata irin iska mai Ƙarfi ta tunkaro ni, cikin sauri na duƙa ƙasa iskar ta wuce. Ko da yaga haka sai naga ya miƙe, yanzu za'a yita kenan, na ayyana a raina. Maimakon in yi kanshi, kawai sai na koma gefe na fara antayo duk wani kafcen sa da zan iya tunawa ina lanƙwashe murya tare da kwaikwayon irin abinda ya aikata a cikin kafcen ina kuma ƙarawa kafcen gishiri da magi.
Wannan abu da nayi fa yasa SINU ya haukace ya dinga yaƙushin jikinsa yana ihu da kururuwa yana buga kansa da duk abinda ya samu. Ni kuwa sai na dage da abin da nake yi, nayi ta kaftawa babu ƙaƙƙautawa, shi kuma ya ci gaba da kururuwa gami da ihu. Ana cikin haka kawai sai ji nayi an buge ni ta baya, hakan yasa dole na dakata da kafcen da nake yi sakamakon faɗuwa ƙasa da nayi. Ai kuwa ina daina yin hakan sai SINU ya dawo hayyacin sa, ba tare da yayi wata-wata ba, kawai sai ji nayi an Luma min wata sharɓeɓiyar Wuƙa a cikina, nan fa zafi zogi, raɗaɗi da azaba duk suka lulluɓeni a lokaci guda, ko ganin mutuwa da nayi ne a fili, ko ya akayi ni dai ban sani ba, kawai ji nayi bakina ya furta INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN!

Ina furta wannan kalma kuwa sai nan take na tuna, tun daga lokacin da wannan yaro yazo yayi sallama da ni ban sake furta sunan Allaah ba sai yanzu, duk abinda nake yi kawai na dogara ne da wayau na da dubara ta. Nan take naji kunya ta kamani, amma da na tuna cewa Allaah mai rahama ne, sai kuma naji kwarin gwuiwa ya shige ni. A wannan lokaci har SINU ya ƙara ɗaga Wuƙar nan da nufin ya caka min, cikin sauri kuwa na fara karanta Alƙur'ani mai girma, ban ma san wata sura nake karantawa ba sai da na kai tsakiya tukun na fahimci Ayatul Kursiyu nake karantarwa. Nan take kuwa sai naji SINU ya kwarara ihu kuma ya ɓace, kamar wasa kuma firit! Sai ji nayi na farka, ashe mafarki nake yi, gashi duk na jiƙe da gumi kamar nayi wanka.

Cikin sauri na tashi na ɗauro alwala nazo nayi sallah Raka'a biyu tare da yin Addu'o'in neman tsari da kariya. Amma bacci sai ya gagare ni, nan na fara tunanin yanzu da ace da gaske ne shikenan na tafi Kenan.

DARASIN LABARIN: Yaku 'yan uwa, shin sau nawa muke mantawa da Allaah mu dogara da tunanin mu, sau nawa muke mantawa da yin addu'a tare da neman taimakon Allaah akan lamuran mu? Sau nawa muke dogara da tunanin cewa mun isa ne shi yasa muke ganin daidai a rayuwa mu manta cewa Allaah shi ne Isashe? Sau nawa muke kasa kaiwa Allaah buƙatunmu saboda muna tunanin cewa zamu iya ko ba tare da shi ba? Shin in muka mutu a daidai irin wannan yanayi me zamu cewa Allaah idan muka haɗu da shi?

Ya Allaah Ka shirye mu, Ka sa mu zamo masu dogara da kai a dukkan lamarin mu. Aameen.

In kunne yaji....


<••••••••••••••••••••••••••••>
  ɧãımãŋ Kɧâŋ Řâééʂ <••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees
Instagram: Haimanraees
Infohaiman999@gmail.com

Post a Comment (0)