SARKIN SARAKAI BOOK 1 - 6

 SARKIN SARAKAI BOOK 1. 06
suka jada baya suka tarwatse koda naga hanya ta samu saina ruga da gudu ina gudun ina saransu kafin abokan gaba su ankara nayi nisa.
Ai kuwa sai suka biyoni cikin matsanancin gudu amma na gaba yai gaba na baya sai labari lokacin da nake wannan gudu ina yinsane cikin takaici domin a rayuwata ban taba guduwa ba daga filin yaki yau gashi bala'i yakai har gudu ya zamadole a gareni inba haka ba kuwa na rasa rayuwata shidai wannan yaki muna yinsa ne a wani daji wanda ake kira BAHARUL SHARUL dajin na dauke da manyan tsaunuka da manyan koguna inda ruwa ke bulbulowa daga cikin duwatsu yana kwaranya yana gudu sa adda abokan gaba suka tasoni a gaba na ga babu matsera kawai saina durfafi wani katon tsauni wanda nidai a rayuwata ban taba ganin tsauni mai tsawonsa ba ina kyautata zaton cewa duk duniya babu tsauni mai fadi da tsawonsa nan fa naci gaba da gudu suna biye dani har muka isa can saman tsaunin muka kureshi koda na leqo kasan tsaunin na ga zurfinsa sai zuciyata ta bugu abokan gaba kuwa sai suka ja dinga a bayana suka fara kyakyata dariya don sun tabbatar da cewa duk wanda ya fada daaga saman wannan tsauni sunansa gawa. Nanfa na tsaya ina tunani a raina nace hakika idan ajalina ya tabbata a hannun abokan gaba an rusa mini tunkahona da darajata a idanun duniya kawai saina sake lekawa kasan tsaunin naga yadda ruwa ke kwarara kasa sanna na yanke hukuncin na daka tsalle na sallamo kasa ko dai na rayu ko na mutu kafin nayi hakan saina juya na dubi abokan gaba nayi murmushi nace idan akwai da namijin da ya isa a cikinku ya biyoni inda zan tafi' kafin abokan gaba suyi wani yunkuri na daka tsalle na sallamo izuwa kasan tsauni lokaci guda abokan gaba suka rugo izuwa karshen tsaunin suka yi cirko cirko suna masu lekowa kasa don suga irin mutuwar da zanyi saboda nisan dake tsakanin saman tsaunin da kasansa sai da dakika dari uku ta shude sannan na iso kasa cikin kogi saura kiris kuwa kaina ya fado kan wani dutse amma sai kafata ta bugi wani wuri a jikin tsaunin saina sauya wuri na nutse izuwa can karkashin kogi.
A wannan lokaci na suma bansan halinda nake cikiba kawai sai farkawa nayi na ganni a gabar kogi a can wani daji daban koda na tsinci kaina a raye sai murna ta kamani nan take na mike tsaye na tafi neman itatuwan da zan sarrafa na yiwa raunikan jikina magani saida na shafe kwana sittin ina tafiya a daji na kwana nan na tashi can sannan na koma gida wato birnin misra.
Sa adda sarki sahibul hairi yazo nan a labarinsa tuni sun gama cinye abincin dake gabansu haluf ya jinjina kai yace hakika ya shugabana ka cika jarumi uban jarumai ina ba don wasu dalilai ba da sainace idan akwai irinka goma a birnin misra da munci duniya da yaki. Koda jin haka sai sarki ya bushe da dariya ba tare da yace komaiba ya mike ya fita wajen tantin koda ganin haka sai bawa haluf ya mike da sauri ya harhada kayansu gaba daya sannan suka hau ababan hawansu suka nausa daji. Kamar yadda sarki sahibul hairi ya fada haka lamarin yakasance wato basu isa birnin askandariyya ba sai kwana talatin da bakwai har suka isa can din kuwa basu sake haduwa da yan fashi ba saidai muggan dabbobin dawa wadanda nan take sarki sahibul hairi keyi musu kisan farat daya.
Lokacinda suka iso kofar birnin Askandariyya dare yayi tsaka har bawa haluf ya nufi kofar birnin da nufin yaje ya kwankwasa a bude masa sai sarki ya dakatar dashi yace saurara yakai haluf aini kadai zan shiga cikin birnin nan kuma indai na shiga ba zan tsaya ko ina ba har saina dangana da fadar sarki barusa naje har inda aka ajiye gatarin nan na lu'u lu'u na daukoshi ka sani yaki da daddare na matsoraci ne lallai gobe da safe ido na ganin ido zan shiga cikin wannan birni na nufi gidan sarautar gadan gadan duk wanda ya tsaya a gabana sai dai gawarsa abinda nake so dakai mu kwana nan kofar gari kuma idan gari ya waye ka jirani a nan har naje na dawo bayan cikar burina idan kuwa kayi kuskure ka biyoni lallai zaka rasa rayuwarka.
Koda gama wannan jawabi sai bawa haluf ya sauko daga kan dokinsa sannan yarike taguwar sarki shima ya sauka cikin hanzari ya daure ababan hawansu a jikin wani dutse ya kafa musu tanti suka shiga ciki suka kwanta suka kama aikin rago. Da Asubar fari sarki ya farka daga barci koda bude idansa yaga bawa haluf yanata barci har da munshari saiya mike ya kama yin damarar yaki ya kwaso makamansa ya shiryasu a jikinsa da ya gama wannan shiri sai ya rufe fuskarsa da wani rawani ya zamana cewa idanunsa kadai ake iya gani ba tare da ya tashi bawa haluf daga barci ba sai ya fita daga tantin yaje ya kwance taguwarsa ya haye kanta ya durfafi kofar birnin Askandariyya a lokacinda gari ya waye sosai rana ta fito. Koda ya iso daf da kofar birnin wacce akayita da bakin karfe sai yaja dunga ba tare da ya sauko daga kan taguwar ba ya zare takobinsa ya kwankwasa kofar da ita faruwar hakankeda wuya sai yaji an tambayeshi da kakkausar murya wanene nan yake kwankwasa mana kofa da sassafe haka? Hala kai bakone baka san ka'idar shigowa birnin mu ba.....
Koda budar bakin sarki sahibul hairi sai yace Ubankane yake kwankwasa kofar tun muna shaida juna ka bude kofar nan in kuwa ka kuskura na banke kofar na shigo sai mataccen dake kabari yafika kwanciyar hankali maimakon abi umarni a bude kofar sai aka kyalkyale da dariya Al amarinda ya fusata sarki kenan kawai ya sauko daga kan taguwar tasa yaja da baya kimanin taku Ashirin sannan ya rugo da gudu ya hada karfinsa gaba daya ya doki kofar garin da kwanjinsa take kofar ta fita fit! Shi da ita suka burma ciki kai kace giwace ta rugo ta bangaji kofar .wOHoHO :) Cikin hanzari sarki sahibul hairi ya mike tsaye sai yayi arba da wani murjejen kato a gabansa katon sanye da suulken yaki kuma ga wani shafcecen gatari a hannunsa amma duk jikinsa karkarwa yake ya kurawa sarki sahibul hairi idanu kawai cikin firgici kamar ace kyat ya fita da gudu sbd razana shidai wannan kato ba kowa bane face sarkin kofa sahibul hairi ya dubi katon yace, kai kuma waye kuma me kake jira dani ba tare da ka afko mini ba tunda ga makami a hannunka' cikin murma mai rawa katon yace nine sarkin kofar birnin Askandariyya yau shekarata arba'in ina gadin wannan kofa amma a tsawon wadannan shekaru ban taba ganin sadaukin mutum tamkarka ba ka sani cewa an taba kokarin balle wannan kofa da karfin giwaye biyu amma abu ya faskara yau gashi kai bil adama kai daya ka banketa anya kuwa kaiba aljan bane? Idan kai mutum ne wanene kai kuma menene yazo dakai wannan birni namu' sarki sahibul hairi yace nine sarki sahibul hairi na birnin misa kuma nazo wannan birni nakune don biyan wata bukata tawa, kayi mini jagora izuwa fadar sarkinku inba haka ba kuwa yanzun nan zaka bakunci barzahu, lokacinda sarki yazo nan a zancensa sai sarkin kofa yai ajiyar zuciya yace hakika biri yayi kama da mutum ni kam nasan cewa duk duniya babu wani sadauki da zai iya bangaje wannan kofa ta fadi face sarkin misra tuni labarinka yazo mana nan to amma ina mai shawartarka da ka janye duk irin bukatar dakazo da ita domin na tabbata cewa sarkinmu bazai yarda da ita ba na sani cewa kai jarumine uban jarumai amma kada ka manta cewa sarkin yawa yafi sarkin karfi kodajin haka sai sarki sahibul hairi ya dakawa sarkin kofa tsawa yace ai ragon maza shike tsoron yawan maza kabi umarnina ko kuma na tabbatar da alkawarina akanka sarkin kofa yace nikam bazanbi umarninkaba saidai nabi na sarkina domin idan na saba masa masifarda zan shiga saina gwammace Ajalina kafin sarki yace wani abu tuni sarkin kofa ya zare wani kaho ya busa faruwar hakan keda wuya saiga dakaru suna ta bullowa a guje tako ina duk sun zare makamai ashe tun dazu ma a lallabe suke suna ganin abinda ke faruwa tsakaninsu lokacinda sarki ya balla kofar birnin saida karar kofar ta cika birnin gaba daya amma da yawan jama a basuyi tsammanin cewa kofar birnin bace wasuma sun zata fashewar dutsen wuta ne kafin sarki ya ankara tuni sama da mutum dari uku sun kewaye shi rike da makamai tsirara sahibul hairi ya dubesu yai murmushi kawai saiya yunkura da nufin ya ratsa ta cikinsu yai gaba aikuwa sai suka rufar masa gaba daya da nufinsu daddatsashi suyi gunduwa gunduwa dashi hakika rashin sani yafi dare duhu inda wadannan dakaru sunsan abinda zai biyo baya da basuyi gangancin afkawa sarki sahibul hairi ba domin a cikin dakika dari da ashirin ya rugurguzasu tamkar an kwankwasa gilashi ya zamana cewa sarkin kofa ne kawai a tsaye kikam kamar gunki idanunsa sun zazzaro kamar zasu fado kasa gaba daya jikinsa rawa yake ya firgita fiye da dazu sa adda ya gaya balla kofar birnin ya fado ciki sahibul hairi ya dubi sarkin kofa yace maza ka gayawa sarkinku abinda ya faru yanzu kuma kace dashi idan ya bani abinda nazo nema zamu rabu lafiya idan kuma ya ki a yau dinnan zan baje wannan birni yadda ko a tarihi baza a tuna dakuba. Koda gama fadin haka sai sarkin kofa ya ruga inda dokinsa yake ya kwance ya haye sannan ya sukwaneshi izuwa cikin birnin Askandariyya shikuwa sarki sahibul hairi sai ya koma inda yabaro taguwarsa yahau sanna ya shigo cikin birnin ya kara gaba ++
A can fadar sarki barusa kuwa fadar ta cika makil da fadawa da talakawan gari domin a yaune sarki barusa ke walimar cikar shekaru talatin akan karagar mulki banda shagali babu abinda akeyi a fadar masu kida nayi masu rawa nayi abinci kuwa da abin shaye shaye gasu nan birjik babu adadi kowa abinda yake so shi yakeci kallo daya mutum zaiyiwa sarki barusa ya gane cewa a cikin tsananin farin ciki yake A wannan lokaci Barusa na zaune shirim kamar giwa a kan karagar mulki yanata kwankwadar giya sai rusa dariya yake yana kallon wadansu yan mata dake ta tikar rawa a gabansa yana annashawa. Ana cikin tsakiyar wannan haline akaga sarkin kofa ya shigo a guje yanata faman haki Al amarinda ya dugunzuma hankalin kowa kenan akayi tsit tamkar mutuwa ta gifta kowa kuma ya kame kamar babu mai rai a wajen ++ .......
Zan Cigaba Insha Allah
Post a Comment (0)