Dole fa za ka tashi bayan ka mutu
Sau da yawa Allah yakan hada imani da shi da imani da ranar karshe, da tashi bayan mutuwa, la'alla ko mutane za su ji tsoron Allah su yi abin da aka hallicce su dominsa.
Amma in ka lura da hali da aiyukan masu kangare ma Allah bisa mataki daban-daban; manyan Mulhidai, Mulhidai 'Yan Boko Aqeeda, da kuma sauran masu aikata sabo da zalunci da ta'addanci a kan mutane, sai ka ga kamar ba su yarda za a tashi a ranar Lahira ba. Kamar gani suke yi in an mutu shi kenan babu abin da zai biyo baya.
To su masu sabo sun yarda in an mutu za a tashi, kuma akwai hisabi, akwai wuta da Aljanna, amma sha'awar abin Duniya ya rufe musu ido. Amma su Mulhidai ba su yarda akwai wani abu bayan mutuwa ba, alhali akwai tarin dalilai da suke sa duk mai hankali ya san akwai barzahu (rayuwar kabari), akwai tashi bayan mutuwa, akwai hisabi, akwai wuta da Aljanna.
Daga cikin dalilai na hankali a kan haka akwai:
1- Tayar da kai bayan ka mutu shi ya fi sauki a kan kirkiran halittarka da samar da kai bayan babu kai. Duk wanda ya yi inkarin tashi bayan mutuwa to ya manta da cewa; a da babu shi amma aka samar da shi.
2- Samar da manyan halittu; sammai, kassai, rana da wata, taurari da manya duwatsu da gingima - gingiman halittu yana nuni a kan cewa; tayar da mutum bayan mutuwa abu ne mai sauki. Wanda ya samar da wadannan manyan halittu abu ne mai sauki a wajensa ya tashi mutum -karamin halitta- bayan ya mutu.
3- Rayar da kasa ta hanyar saukar da ruwan sama bayan ta bushe k'arau dalili ne a kan rayar da mutum bayan ya mutu. In har kasa da take da tauri za ta rayu ta yi laushi har ta fitar da tsirrai bayan ta bushe to ina kuma ga mutum da yake da jini da tsoka da fata mai laushi?!
4- Wani abu mai kama da rayar da kasa shi ne rayar da bishiyoyi da tsirrai da suka bushe. Wannan ma dalili ne a kan rayar da mutum bayan ya mutu.
5- Mutane da dabbobi sukan yi rama imma saboda rashin lafiya ko rashin abinci ko rashin kwanciyar hankali, amma in wannan sababi ya kau sai ka ga mutum ya dawo da jikinsa ya yi k'iba. Lallai wannan dalili ne a kan cewa; ashe za a iya sake dawowa da mutum kamar yadda yake bayan ya mutu jikinsa ya zagwanye.
Saboda haka duk mai hankali, matukar zai yi amfani da hankalin nasa lallai zai san cewa; lallai fa za a tashe shi bayan mutuwa, kuma za a yi masa hisabi, zai yi bayani a kan duk abin da ya aikata. Don haka ka ji tsoron ranar da za ka fanshi kanka ko ka halakar da ita.
To Mulhidi, sai murna ta koma ciki!
Dole za a tashe ka bayan ka mutu.
*Rubutawa:✍🏻*
*Dr. Aliyu Muhd Sani*
(Hafizahullah)
*🕌SAUTUS SUNNAH*