FASSARAR WAƘAR AE DIL HAI MUSHKIL

Fassarar Waƙar Ae Dil Hai Mushkil (Title Song)

Sunan Waƙa: Ae Dil Hai Mushkil (Title Song)

Sunan Shiri: Ae Dil Hai Mushkil

Shekarar Fita: 2016

Haɗa Sauti: Pritam

Rubutawa: Amitabh Bhattacharya

Kamfani: Sony Music

Rerawa: Arijit Singh

Fassarawa: Haiman Raees


* Tu Safar Mera, Hai Tu Hi Meri Manzil

Ke ce tafiya ta, ke ce bigire na

* Tere Bina Guzara, Ae Dil Hai Mushkil

Yin rayuwa ba tare da ke ba, Wayyo zuciya, abin da wahala

* Tu Mera Khuda, Tu Hi Duaa Mein Shaamil

Kece abar bauta na, kina cikin kowace Addu'a tawa

* Tere Bina Guzara, Ae Dil Hai Mushkil

Yin rayuwa ba tare da ke ba, Wayyo zuciya, abin da wahala

* Mujhe Aazmaati Hai Teri Kami

Rashin ki ba jarabata (koda yaushe)

* Meri Har Kami Ko Hai Tu Laazmi

Kin cike kowane gurbi na rayuwa ta

* Junoon Hai Mera Banoon Main Tere Qaabil

Son samu ba shi ne in cancance ki

* Tere Bina Guzara, Ae Dil Hai Mushkil

Yin rayuwa ba tare da ke ba, Wayyo zuciya, abin da wahala

* Yeh Rooh Bhi Meri, Yeh Jism Bhi Mera

Wannan ruhin nawa ne, wannan jikin nawa ne

* Utna Mera Nahi, Jitna Hua Tera

Amma su ba nawa bane kamar yadda suke naki (sun fi zama naki fiye da nawa)

* Tune Diya Hai Jo, Woh Dard Hi Sahi

Abinda kika bani shi ne baƙin ciki

* Tujhse Mila Hai Toh, Inaam Hai Mera

Amma tunda ke kika bani, sai ya zama tamkar kyauta ne a gare ni

* Mera Aasmaan Dhoondhe Teri Zameen

Sararin Samaniya na yana neman Duniyar ki

* Meri Har Kami Ko Hai Tu Laazmi

Kin sa komai na rayuwata ya zamo cikakke

* Zameen Pe Na Sahi, Toh Aasmaan Mein Aa Mil

In ba a ƙasa ba, to ki zo mu ki haɗu da ni a Samaniya

* Tere Bina Guzara, Ae Dil Hai Mushkil

Yin rayuwa ba tare da ke ba, Wayyo zuciya, abin da wahala

* Maana Ki Teri Maujoodgi Se, Yeh Zindagani Mehroom Hai

Na san cewa rayuwata tana cikin rashi in har babu ke

* Jeene Ka Koi Dooja Tareeka, Na Mere Dil Ko Maaloom Hai

Zuciyata bata san wata hanya ta yin rayuwa ba (face son ki)

* Tujhko Main Kitni, Shiddat Se Chaahun

Ina Matuƙar ƙaunar ki tare da cikakken miƙa wuya

* Chaahe Toh Rehna Tu Bekhabar

Kina iya ci gaba da zama ba tare da kin fahimta ba in kin so

* Mohtaaj Manzil Ka Toh Nahi Hai, Ye Ek Tarfa Mera Safar

Tafiya ta haka take ta yadda bata dogara da bigiren da zata ba

* Safar, Khoobsurat Hai Manzil Se Bhi

Wannan tafiyar ta ma fi bigiren kyau shi kansa

* Meri Har Kami Ko Hai Tu Laazmi

Kin cika min kowane gurbi na rayuwata

* Adhura Hoke Bhi Hai Ishq Mera Qaamil

Duk da ya ke cewa ni ba a kammale nake ba, soyayya ta a gareki cikakkiya ce

* Tere Bina Guzara, Ae Dil Hai Mushkil

Yin rayuwa ba tare da ke ba, Wayyo zuciya, abin da wahala


<••••••••••••••••••••••••••••>
      ɧãımãŋ Řâééʂ <••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees
Instagram: Haimanraees
Infohaiman999@gmail.com

Miyan Bhai Ki Daring
Post a Comment (0)