SHARHIN FIM ƊIN ANT-MAN
Ant-Man fim ɗin jarumta ne da aka fitar da shi a cikin shekara ta 2015 a Ƙasar Amurka. Labarin fim ɗin ya samo asali ne daga littattafan almara mai suna Ant-man wanda Kamfanin Marvel Comics suka Wallafa. Kamfanin Marvel Studios ne suka ɗauki nauyin shirya fim ɗin, Yayinda Kamfanin Walt Disney Motion Pictures suka rarraba shi. Fim ɗin shi ne Fim na goma sha biyu daga cikin Fina Finan duniyar Marvel mai suna Marvel Cinematic Universe (MCU).
Peyton Reed ne ya bada umurnin fim ɗin, Kevin Feige ya ɗau nauyi, sa kuma Edgar Wright, Joe Cornish, Adam McKay da Paul Rudd suka rubuta kuma suka tsara. An fara Ɗaukar wannan Fim ne a watan Agusta 2014 kuma aka kammala a watan Disamba a San Francisco da Metro Atlanta.
An saki Ant-Man a Los Angeles ranar 29 ga watan Yuni 2015 June 29, 2015, sannan aka sake shi a ko ina ranar 17 ga watan Yuli 2015 a zubin 3D da IMAX 3D . Fim ɗin ya kawo kuɗi sama da dala miliyan $519 a harkar Kasuwancin Fina Finan duniya baki ɗaya kuma ya samu yabo matuƙa daga masana harkar Fina-Finai. An saki na biyun sa mai suna Ant-Man and the Wasp a watan Yuli 2018.
LABARIN FIM ƊIN
A 1989, masanin Kimiyya Hank Pym yayi ritaya S.H.I.E.L.D. bayan ya gano cewa sun yi Yunƙurin ruɓanya rigar sa ta Ant-Man.
Yayinda ya fahimci cewa wannan fasaha tashi tana da hatsari sosai, sai Pym ya sha alwashin ɓoye wannan fasaha tasa har zuwa ƙarshen rayuwar sa.
A yanzu kuma 'yar Pym, Hope van Dyne , da kuma tsohon ɗalibinsa Darren Cross sun tilasta masa barin Kamfanin sa na Pym Technologies. Cross ya dake matuƙa wajen ganin ya ƙirƙiri irin wannan rigar tasa ta kansa wacce ya sa mata suna Yellowjacket , wanda hakan ya firgita Pym matuƙa.
Bayan Fitowar sa daga magarƙama, Shahararren ƙasurgumin ɓarawo Scott Lang sai ya koma zama tare da tsohon abokin sa Luis. Lang sai ya ziyarci 'Yarsa Cassie ba tare da sanarwa ba, hakan yasa saurayin tsohuwar matar tasa Paxton wanda ɗan sanda ne ya kore shi saboda baya kawo ma matarsa Maggie wani taimako domin kulawa da 'Yarsa. Lang yayi bakin ƙoƙarin sa wajen samun aiki amma ya gaza samu saboda tsohon laifin sa. Dole ta sa ya yarda ya shiga ƙungiyar Luis domin su je su yi sata a wani gida.
Lang sai ya shiga wannan gida ya buɗe
ma'ajiyar gidan. Maimakon yaga kuɗi, sai yaga wata tsohuwar rigar 'yan tseran babur, haka dai ya ɗauke ta ya nufi gida. Bayan ya sanya wannan riga, sai ya danna wani makunni a jikinta da nan take ya maida shi ɗan mitsili tamkar ƙwaro. Wannan al'amari ya firgita shi sosai, don haka sai nan da nan ya maida wa masu gidan nan rigar su. Sai dai kash! Yana fitowa daga gidan bayan ya ajiye rigar sai kuma 'yan Sanda suka kama shi da laifin ya shiga yin sata ne.
Pym, wanda shi ne mai wannan gida sai ya ziyarci ofishin da aka kulle shi sannan ya taimaka masa bashi rigar ya gudu. Ashe tun dama can Pym ɗin ne ya aikata maguɗi ta hanyar Luis domin ya samu haɗin kan Lang har ya yarda ya zama sabon Ant-man domin ya sace rigar da Cross ya ƙera.
Kasancewar dama sun daɗe suna leƙo asiran Cross tun bayan da suka fahimci Manufar sa, sai Van Dyne da Pym suka horas da Lang faɗa da kuma yadda zai iya kula tare da amfani da ƙwari.
Ita kuma Van Dyne ta tsani Mahaifin ta Pym tun bayan mutuwar mahaifiyar ta Janet, Pym ya bayyanawa Lang cewa Janet, wacce aka fi sani da WASP ta ɓace ne a Daular ƙananun halittu yayin da ta ke lalata wani makami mai linzami da aka harba.
Bugu da ƙari Pym ya gargaɗe shi da cewa shi ma zai iya fuskantar wannan waƙi'a matuƙar yace zai yi wasa da injin ƙayyadewa da ke jikin rigar tasa.
Daga nan sai suka aike shi hedikwatar tawagar Avengers domin ya sato wata Na'ura wacce zata taimaka musu wajen gudanar da aikin su. A garin haka ne ma suka yi wata 'yar ƙaramar fafatawa a tsakanin sa da Sam Wilson.
Cross ya samu nasarar kammala wannan riga tasa ta yellow Jacket har ma ya gayyaci manyan mutane izuwa Kamfanin Pym Technologies domin ya ƙaddamar da ita.
A daidai wannan lokaci ne shi kuma Lang, tare da ƙwarin sa da kuma taimakon abokan sa suka shigo Kamfanin suka lalata kayan aikin kamfanin tare da dasa ƙananan bama-bamai, amma yayin da yayi yunƙurin sace jakar sai Cross ya kama su.
Lang ya samu damar ɓallewa daga kejin da aka kama shi a ciki, inda shi da Van Dyne suka yiwa jami'an Cross Sambaɗebaɗe amma mutum ɗaya ya samu damar guduwa da samfurin aikin Cross ɗin guda ɗaya. A wannan bata kashi ne aka harbi Pym a hannu, yayin da Lang ya bi bayan Cross wanda ya hau jirgi ya gudu, Van Dyne da Pym suna fita Kamfanin na rushewa.
Sai dai kafin Paxton ya kama Lang sai Cross ya saka tasa rigar ya tunkare shi. Cross ya sace Cassie domin ya ja hankalin Lang inda suka yi artabu. Lang ya taɓa wannan inji na ƙayyadewa domin ya lalata rigar Cross, hakan yasa ya koma ƙarami tamkar ƙwayar zarra kuma ya faɗa daular ƙananun halittu.
Sai dai Lang ya samu damar sarrafa Sakamakon da wannan yanayi ya Samar masa har samu nasarar dawowa yadda yake. Wannan jarumta da Lang ya nuna tasa Paxton ya rufa masa asiri ya kuma taimaka masa wajen hanawa a kai shi Magarƙama. Ganin cewa Lang ya rayu kuma har ya samu damar fitowa daga wannan Daula ta ƙananun halittu, sai Pym ya fara tunanin ko dai ita ma matarsa tana raye?
Bayan nan, Lang ya haɗu da Luis inda yake sanar da shi cewa Wilson na neman sa. Shi kuma Pym sai ya Nunawa Van Dyne wata sabuwar rigar WASP kuma ya bata ita.
A wata fitowa ta ƙarshe kuma, an nuno Sam Wilson da Steve Rogers tare da Bucky Barnes a tare da su, kuma basu da damar tuntuɓar Tony Stark saboda dokokin da aka gindaya, har Wilson yake cewa ya san wani wanda zai iya taimakawa.
JARUMAN FIM ƊIN DA MATSAYIN DA SUKA FITO DA SHI A CIKIN SA
* Paul Rudd - Scott Lang / Ant-Man
* Evangeline Lilly - Hope van Dyne
* Corey Stoll - Darren Cross /Yellowjacket
* Bobby Cannavale - Paxton
* Michael Peña - Luis
* Tip "T.I." Harris - Dave
* Anthony Mackie - Sam Wilson / Falcon
* Wood Harris - Gale
* Judy Greer - Maggie
* David Dastmalchian - Kurt
* Michael Douglas - Hank Pym
* John Slattery - Howard Stark
* Hayley Atwell - Peggy Carter
* Abby Ryder Fortson - Cassie
* Gregg Turkington - Dale
* Martin Donovan - Mitchell Carson
* Hayley Lovitt - Janet van Dyne / Wasp
<••••••••••••••••••••••••••••>
Hãïmâñ Khãñ Řăééş <••••••••••••••••••••••••••••>
08185819176
Twitter: @HaimanRaees
Instagram: Haimanraees