KU DUBA WANNAN ASARAR


KU DUBA WANNAN ASARAR:
:
A Ranar Al-Qiyama Za'a Tura Wasu Tawagar Mutane Izuwa Gidan Aljannah. Yayin Da Suka Kusanto Ta, Suka Fara Jin 'Kamshinta, Suka Kalli Kyawun Katangun Gidan Aljannar, Da Kuma Abubuwan Jin Dadi Wanda ALLAH Ya Tanadar Ma Mazaunan Cikinta,
:
Sai Su Ji 'Kira(Daga RABBUL-IZZATI) Yana Cewa:"(YA KU MALA'IKU!) KU JUYO DA SU DAGA GARE TA! DOMIN SU BA SU DA RABO A CIKINTA!!"
:
Sai Su Juyo Suna Cikin Asara Da Nadama Fiye Da Dukkan Mutanen Farko Da Na 'Karshe.
:
Za Su Ce:"Ya UBANGIJINMU! Wallahi Mun Fi Wulakanta Da Tozarta a Yanzu Fiye Da Ace Ka Shigar Da Mu Gidan Wuta. Kafin Ka Nuna Mana Wannan Aljannar Da Kuma Abin Da Ka Tanadar Ma Masoyanka a Cikinta".
:
Sai UBANGIJI Ya Ce Musu:"HAKA NA YI NUFI DA KU, DOMIN KUN KASANCE:
:
*. Idan Kuka Ke6ance(Ba a Gaban Mutane Ba) Kuna Aikata Manyan Laifuka a Gabana.
:
*. Idan Kuka Hadu Da Mutane, Kuna Nuna Musu Cewa Ku Mutanen Kirki Ne.
:
*. Kuna Nuna Ma Mutane Kyawawan Ayyukanku, Sa6anin Irin Abin Da Kuke Nuna Min Na Munanan Ayyuka Idan Kun Ke6ance.
:
*. Kuna Jin Tsoron Mutane, Amma Baku Jin Tsorona.
:
*. Kuna Girmama Mutane, Ni Kuma Bakwa Girmama Ni.
:
*. Kuna 'Kin Aikata Zunubi Saboda Mutane(Kar Su Zage Ku) Amma Bakwa Bari Domin Girma Na,
:
A Yau 'Din nan Zan 'Dandana Muku Radadin Azaba Ta, Tare Da Haramta Muku Samun Babban Sakamako Na".
:
(Ibnu Abid-Dunya Ne Ya Ruwaito Hadisin).
:
Ya ALLAH! Don Girmanka Don Buwayar Mulkinka, Don 'Karfin Ikonka, Ka Kiyayemu Daga Sharrin RIYA Da Sauran Miyagun Laifuka Ameeeeeen.
Post a Comment (0)