*MATA MASU GIDA KU SAURARE NI*
Nasiha ce zan yi muku, aiki da ita kuma ya rage zabinku:-
◼- Duk matar da ki ka ji tana cewa: babu wani da namijin da ya isa ya yi min haka in kyale shi, ki kiyaye ta !
◼- Duk matar da ta ke cewa: namiji ba dan goyo ba ne, ki kiyaye ta !
◼- Duk matar da ta ke cewa: ke ki ka yarda, ai wallahi da ni ce ke, ba a isa a yi min haka ba in yarda, ki kiyaye ta !
◼- Duk matar da ba za ta ba ki hakuri game da matsalolin gidanki ba, ki kiyaye ta !
◼- Duk matar da ta ke cewa: ai ni maigidana idan na shata layi bai isa ya tsallaka ba, ki kiyaye ta !
◼- Duk matar da ta ke cewa: ai ni gidana ba ni da matsala ko wace iri, ki kiyaye ta !
◼- Duk matar da ki ka ji tana amfani da lafuza na zagi da bakaken maganganu, ki kiyaye ta !
◼- Duk matar da ta ke yada sirrin gidanta da abin da yake gudana tsakaninta da maigidanta, ki kiyaye ta !
◼- Duk matar da ta ke ce miki: akwai wani malami, zan kai ki wajensa ya taimaka miki, ki kiyaye ta !
◼- Duk matar da ta ke cewa da ke: kishiya ba abar amincewa/ba `yar uwa ba ce, ki kiyaye ta !
*HUJJA*
◼- Tsakanin mace da namiji sai da yafiya, wata rana shi zai bata miki, wata rana kuma ke ce za ki bata masa.
◼- Allah Subhanahu Wa Ta`ala shi ya halicci mace da namiji, ya danka rikon mace da kula da ita bayan aure a hannun mijinta (namiji).
◼- Kowa a na bata masa, amma kuma idan ya yi hakuri, ya yafe zai ga kyakkyawan sakamako, ko ba a nan ba gidan duniya.
◼- Babu wata rayuwa da za a ci gajiyarta sai fa an hada da hakuri, kuma duk ma`auratan da ba a jin kansu hakuri da juna su ke yi.
◼- Allah bai tsara cewa miji ne zai yi biyaiya ga matarsa ba, sai dai cewa a ka yi: ya kyautata mata, ya kuma ba ta hakkokinta.
◼- Babu wani gidan aure da ba shi da irin tasa matsalar, sai dai ta wani ce ta fi ta wani.
◼- Manzon Allah(saw) cewa ya yi: ``kalma daddada ma sadaka ce``, zagi kuwa da bakaken maganganu, ba dadadan kalmomi ba ne.
◼- Manzon (saw) ya hana ma`aurata su rika yin abubuwansu da dare a daki, sannan da safe su fito suna ba da labari, sannan kuma daman rayuwar ma`aurata ta na bukatar sirri.
◼- Babu wani malami na gaskiya da zai taimaka miki wajen inganta rayuwar aurenki da ya shige ya ce miki:- Ki ji tsoron Allah, ki kiyaye dokokinsa, ki yi bayaiya ga mijinki, ki darajanta danginsa, ki kula masa da dukiyarsa.
◼- Allah Ta`ala shi ya shar`anta aure, ya kuma halatta wa namiji auren mace fiye da daya, duk matar da Allah ya kaddara ba ita daya ba ce a wajen maigidanta, hadin kansu, da rungumar junansu, da yada soyaiya da zumunci tsakanin `ya`yansu, shine zai faranta wa maigidansu, ya kawo masa nutsuwa da daidaito a cikin lamuransa. Sannan kuma wata kishiyar zuwanta ne sanadin yaduwar arziki da wadata a gidanku.
KARSHEN WASIYYAR KE NAN, AIKI DA ITA KUMA YA RAGE NAKI, AMMA DAI BABU DOLE A KANKI !