MATSALAR RASHIN YIN AURE DA WURI

MATSALAR RASHIN AURE DA WURI 

 IYAYE WANNA MATSALAR KUCE ?

Tana daga cikin abubuwan da suke ci ma al-ummar musulmai tuwo a kwarya a wannan zamanin
zakaga budurwa yar shekara 30 ko 40 da dai sauransu amma bata taba yin aure ba yawansu ba wai abisa son ransu bane a'a illa dai matsalar yanayin halin rayuwa ko dai matsalar jinnul ashiq dinnan wacce muke magana akai ko kuma matsalar iyaye muke magana a kai musamman ma iyaye maza zaka ga dattijo yarsa ta samu mijin aure amma sai yace wai ba zata yi aure yanzu ba sai ta gama UNIVERSITY.

UNIVERSITY zata iya jiran yarka amma AURE ba zai jirata ba
don haka ya kamata iyaye su rika sanya tsoron Allah a cikin wannan al'amari kuma su guji kallo abin duniya a matsayin shine kwanciyar hankalinsu.

✆ WhatsApp +2348141712330

IYAYE=tambaya ta gareku.

・ ita wanna yariya bata sha'awa.

・ shi wannan yaro baya sha'awa.

duk fa mutane ne kamar ku iyayena.

wanna yana jefa mata da yawa gaske =LESBIAN=madigo
=sex wannan yana jefa matasa da yawa SEX AMFANI DA HANNU iyaye ku duba wannan matsala ta matasa da idon basira.

NEMAN DUNIYA YA HANA IYAYE SAMUM LOKACIN TARBIYYA:

uba ya tafi kasuwa bai dawo ba sai bayan la'sar basu san kalan abokan da yaransu ke ma'amala dasu ba sun manta da hakkin tarbiya yar-yaro dake kansu.

・ wannan yasa yan'mata da yawa sun rasa budurci su.

・ RASHIN YIN AURE DA WURI: a shekarun baya an aurar da 20 duk da cewa akwai rashin karatu amma kuma akwai tarbiyya a shekarun baya ba'a samu cikin shege kuma gashi yan mata da samari sukan kwana daki 1 yanzu kuma saboda kokarin tafiya da zamani ba'a yiwa yarinya aure sai ta gama gajiya da zaman tuzuranci saboda karatu babu ruwan iyaye na irin halin da yariya zata shiga na bukatar miji yayin karatun damuwarsa kawai ta gama makarantar don ta samu aiki ita kuma kafin ta gama sai ta nemi hanyoyin biyan bukatarta ta kowane hali imma ta hanyar samun namiji a matsayin mai temakonta a karatu!!! Friend ko ta hanyar yan'uwanta mata a matsayin kawaye haka shima namiji anki masa aure har ya haura sama da shekara 30 amma yasan komai ta hanyan haramun kafin aure damuwar iyayensa ace masa DR,KO INJINIYA KO LAUYA DSS.

MATSALA GA IYAYE

BALAGA:don wanna lokaci ne wanda yaro ke canzawa a rayuwa ya fara ganin mutane duk basusan me sukeyi ba shine kadai mai wayo ita kuma.

'YA MACE a wannan lokacin ya kamata mahaifiyarta ta kusanceta kuma ta koya mata abubuwa da hukunce-hukunce da suka kebanci 'ya mace amma sai yariya ta kai minzalin aure iyayenta basu taba koya mata wankan janaba ba ko kuma hukunce-hukunce jinin haila.

MATSALOLI KAFIN AURE

wasu daga matsalolin da saurayi ko budurwa kan iya fuskanta kafin aure ko bayan aure-wani lokaci saurayi da budurwa suken fuskanci matsala ne kamar haka.

BURIN DA KOWANE BANGARE DA IYAYEN SAURAYI DA BUDURWA: 

ko su kansu saurayi da budurwa suke ci game da saurayi ko budurwa kamar daki da yake tunanin a kawo ta da shi da sauransu ko kuma shi kayana da take tunanin ya kai gidansu.

NAU'IN SADAKIN DA AKE AYYANAWA: 

ko kuma ince kayan mun gani muna so da lefe a al'adunmu da ake sanyawa a kan saurayi da idan suna da yawa yakan sanya jinkirin aurensa.

kudaden kashewa domin bikin aure.

tsanantawa wajen binciken laifufukan juna.

binciken matsayin dangin juna ta fuskacin wani MUKAMI KO DUKIYA UWARGIDA KIYAYE WANNA.

+KI RIKE MATSAYINKI
+KIYI HADIN GWUIWA
+KIYI MASA KYAKKYAWAN ZATO
+KI SO MIJINKI YADDA YAKE
+KI AMSA KIRANSA
+KI SAMU LOKACINSA
+KI KASANCE MAI JITUWA
+KI NEMI SHAWARA
+KADA KI HADA KANKI DA WATA
+KI FADA MASA GASKIYA
Sirrin rike miji

¤da fatan zamu gyara mata da miji

: sirrin rike miji
WhatsApp: ☏+2348141712330

Post a Comment (0)