HIKAYAR WASU SARAKUNAN HINDU
Tare da Sadiq Tukur Gwarzo
A wani zamani mai tsawo daya shude, lokacin da ake cewa mutane na magana da dabbobi, anyi wasu sarakuna biyu manya a kasar hindu, kowannen su na mulkin garin sa daban da dayan, sannan dukkansu sun kasance masu yawan kyauta, amma dayan su yafi daya kyauta.
Sarki na farko sunan sa Karna. A kullum yana rabon dinare dari ga mabukata. Har ma yasha alwashin cewa bazai taba cin abincin safe ba a kowacce safiya har sai ya kammala rabon dinare darin daya saba. Sai dai inda yake samun wadannan dinarai ya zamo abin tambaya da mamaki a wurin jama'a.
Na biyun su shine Vikram. Wannan sarki shahararre ne a wurin kyauta. Domin yana bada kyautar duk abin da aka tambayeshi tun daga kan gwala-gwalai, azurfa, gidaje, kuyangi da sauran su. Ance babu abinda ake tambayar sa ba tare da an samu ba, kuma wai har dabbobi na rokon sa abu.
Wata rana Sarki Vikram na shakatawa a lambunsa, sai ga wasu tsuntsaye mace da namiji sun dira a gabansa.
Namijin yace "Ya sarki mai kyauta, ka ceci rayuwar mu, yunwa zata kashemu".
Sarki yace "Abinci kuka rasa ko yaya? Idan kunaso zan rinka aiko muku da tsabar abinci a kullum".
Ta macen tsuntsun sai tace "Ay bazamu iya cin tsaba ba. Muna rayuwa ne can saman wani tsibiri, kuma 'ya'yan itatuwa ne wadanda ba'ai wa tabo ba kadai abinda muke iya ci"
Sarki yace " To babu matsala". Nan take yasa aka kawo musu zababbun 'ya'yan itatuwa masu kyau aka basu. Sannan aka ce kullum safiya suzo su amshi irin wadannan 'ya'yan itace masu kyau suci.
Hakan ne yayi ta faruwa. Kullum da safe tsuntsayen na samun abinda suke so kamar yadda aka alkawarta musu. Sai dai wata rana, ta-macen tsuntsuwar nan ta lura da cewa an kawo musu 'ya'yan itatuwa wadanda aka gatsa. Sai tace da namijin "kalli da kyau kagani.. Anyiwa wadannan 'ya'yan itatuwa tabo. Don haka sarki bazai iya ciyar damu ba, zaifi kyau mu tashi mu tafi wani wurin daban".
Da fadin haka sai gano su akayi sun shilla sama suna karkada fuka-fukin su tare da fadin "mungode maka Sarki Vikram, kaine mafi kyauta a sarakunan duniya".
Tsuntsayen basu gushe ba suna wannan yabo ga Sarki Vikram har sai da suka yi nesa sosai da garin izuwa wani babban tsibiri. Ashe a hanyar su ta wucewa sun gushe ta saman fadar Sarki Karna har kuma yaji abinda suke cewa, abinda ya sashi kishi, yake tambayar kansa tayaya za'ace akwai wani sarki da ya d'ara shi kyautayi a duniya?
Ai kuwa sai ya umarci wasu sadaukan sa da subi bayan wadannan tsuntsaye kuma su tabbata sun kawo masa su.
Kafin wani lokaci kuwa sai ga dakaru sun zo da tsuntsaye cikin keji ga Sarki Karna.
Sarki ya dube su cikin annushuwa yace " Naji kuna kiran wani sarki a matsayin wanda yafi kowanne kyauta, shin meye dalilin ku na fadar haka?"
Namijin Tsuntsu yace" Sarki Vikram ya kasance yana ciyar damu 'ya'yan itatuwa zababbu kullum da safe kuma baya daure wadanda basuyi laifi ba acikin keji".
sarki karna yace "Na kasance kullum da safe ina rabon dinare dari ga mabukata. Ashe ban fishi ba?" Sannan ya dubi dakarun sa yace "Ku kawo kwandon zababbun 'ya'yan itatuwa zan ciyar dasu yanzu".
Da aka kawo sai ya kalle su yace "Yanzu zan sa a ciyar daku da zababbun yayan itace, shin ban fishi kyauta ba?"
Sai ta macen tsuntsuwar tace "Ai shi sarki vikram da hannun sa yake ciyar damu".
Hakan yasa shima Sarki Karna yayi yinkurin ciyar dasu da hannun nasa, ya bude kejin zai mika musu tuffa. Sai dai kuma cikin hanzari ta macen tsuntsuwar tayi wuf ta fito daga kejin, sannan ta tashi sama. Bata zame ko ina ba sai gaban Sarki Vikram.
Da zuwanta ta fadi gaban sa tana afi, tayi masa bayanin abinda ya faru tare da rokon sa ya 'yanto mata mijin ta.
"Zan 'yan to miki mijin ki". Abinda sarki Vikram kurum ya fada mata kenan.
Kashe gari yayi shigar tsummokara, ya nufi birnin da Sarki karna ke mulki. Da zuwan sa ya wuce fada gaban sarki.
Ya fadi yayi gaisuwa, sannan yace " ya wannan sarki mafi kyauta a duniya, naji labarin karimcin ka da kyautatawar ka, don haka ina neman izinin ka don na zamo maka bara mai maka hidima."
Jin haka sai yasa sarki Karna yaji dadi a zuciyar sa. Sannan yace masa babu komai, " Duk abinda kaji a bakin mutane game dani gaskiya ne, kuma zaka shiga cikin masu dauko mini dinaran da nake rarrabawa kullum da safe".
Da gari ya waye kuwa Vikram da wasu bayin sarki suka kamo mazubin dinarai niki-niki. A kan idon sa Sarki karna ya raba guda dari ga mabukata.Shi da kansa vikram sai daya raya a ransa cewa Sarki karna ya fishi kyauta. Amma kumà sai yasha alwashin sanin inda Sarkin ke samo wadannan dinarai.
Tun daga nan Sai vikram ya ke ta leken asirin aiyukan Sarki Karna. Watarana da dare yayi, vikram ya wanzu leka kofar dakin sarki karna don yaga ko zai ga fitowar sa. Ai kuwa da gari ya dauko wayewa sai Vikram ya hango Sarki Karna ya fito daga dakin sa, yana waige-waigen kada wani ya gansa, sannan yabi wata hanya wadda zata fitar dashi daga cikin gidansa.
A hankali vikram ya rinka bin bayan sa yana labewa don kada ya juyo ya ganshi. Sai da suka fita daga gidan izuwa bayan gari, sannan Vikram ya hango Sarki karna ya nufi wata Bukka, kafin isar sa kuma sai ga wani tsoho irin masu kawwame kawunan su a wajen gari don bauta, ya nufo sarkin. Da haduwar su sai tsohon ya dukursa ya gaishe da sarki karna.
Sarki Karna ya tube kayansa daga shi sai gajeran wando, sannan ya dauki wata sanda ya nufi karkashin wata bishiya dake wurin. Ya rera wasu baitoci kamar haka:-
Ka_s_u_s_u_w_a_ d_a_ d_a_d_i_, a_m_m_a_ b_a_ k_a_m_a_r_ n_a_m_a_ b_a_.
Ka_b_a_ s_h_i_ r_a_y_u_w_a_, n_i_k_u_m_a_ z_a_n_y_i_ a_g_a_j_i_.
Da gamawar sa sai ya zunguro wata shigifa dake saman bishiyar. Nan take sai ga dinarai nata zubowa. Sanna ya karbo mazubi daga wurin tsoho ya zuba, yayi sallama da tsohon nan ya juyo izuwa gida yana dauke da tulin dinarai akansa. Anyi wannan duk akan idon Vikram. Da ganin haka, sai yace "yawwa, yanzu na gano yadda zan ceci Tsuntsu."
Kashe gari da sassafe vikram yayi sammako ya riga Sarki karna fitowa. Yazo wurin dattijo tare dayin duk abinda yaga sarki karna yayi. Tsoho bai iya gane shiba, abinda kurum ya iya tambaya shine sammakon da yayi, tunda yazo ba a lokacin daya saba zuwa ba. Vikram ya make murya ya ce masa uzuri ne ya fito dashi. Da Vikram ya gama yin duk abinda yaga sarki karna yayi, sai yace yau yana son tafiya da wannan shigifar gida, saboda kwana biyu wani uzuri zai hana shi zuwa wannan wuri. Tsoho yace to ba matsala. Sai kuwa vikram ya hau sama ya ciro shigifa yayi gaba da ita.
Anyi haka ba jimawa sai ga Sarki karna ya iso. Tsoho ya kamu da mamaki, ya kuma kwashe labarin abinda ya faru ya shaida masa. Nan take sai sarki karna ya cika da matsanancin bacin rai, lallai yasan cewa wanine yayi shigar sa ya tafi da wannan shigifa ta siddabaru.
Ya gama fadace-fadacen sa ga tsoho akan don me zai bari a tafi da shigifa, sannan ya koma gida. Kwana biyu sarki baya kyauta, kullum cikin bacin rai yake, har abinci ma baya iyaci.
Rannan kwatsam sai Vikram ya faki idon mutane ya shiga dakin Sarki karna. Yace masa "abokina, ka kwantar da hankalinka, shigifar ka na wuri na. Kuma zan dawo maka da ita matsawar zaka saki wannan tsuntsun da kake tsare dashi."
Sarki karna yayi tsallen murna, sannan yace ai a shirye nake na baka duk abinda kake so akan wannan shigifa. Amma yace yana rokon ya sanar masa da labarin sa.
Vikram ya labartawa karna ko shi waye da kuma labarin sa. Wannan abu yayi matukar kayatar da sarki karna. Shine ma har yace hakika tsuntsaye sunyi gaskiya. Ni ina iya yiwa talakawa kyauta don fidda su daga talauci, amma kai ka fini kyautatawa tunda kana iya sadaukar da kanka don 'yantar da tsuntsu."
Ai kuwa sai suka dunguma izuwa kejin da tsuntsu yake a tsare. Sarki karna ya bude kejin, tsuntsu yayi fir ya tashi sama inda ya hadu da matar sa wadda a kullum take rayuwa a boye a saman wata bishiya cikin bakin cikin rashin sa, tana mai fatan ganin ran da zai samu 'yanci.
Tsuntsayen suka wanzu cikin farin ciki suna waka ga sarki vikram, suna cewa " mungode, mungode, mungode wa Sarki vikram, wanda yafi dukkan sarakunan duniya kyautatawa"
Daga nan sai raha ta barke a tsakanin sarki Karna da sarki Vikram. Sarki karna ya tashi runduna don tayiwa sarki vikram rakiya izuwa birnin sa, sannan yasha alwashin shima idan ya samu lokaci zai kawowa Sarki vikram ziyara a birnin sa, zai kuma labarta masa labarin wannan shigifa mai ban mamaki wadda take aman dinare.