ZUNZURUTUN ARZIƘI

       💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

     DARUSSAN RAYUWA


  ࿐​ ​PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION࿐​

༄༄ PWA ༄༄

 ➖➖➖➖➖➖➖➖➖
                ✹••✹••✹••✹••✹••✹••✹
     ʂɬơrყ/wrıɬɛɛŋ     
            ɮʏ✍🏻:
👉🏻© ɧãımãŋ Řâééʂ ✹••✹••✹••✹••✹••✹••✹
 ➖➖➖➖➖➖➖➖➖

                    Fitowa ta 02

         ZUNZURUTUN ARZIƘI

Watarana Wani Hamshaƙin mai kuɗi ya ɗauki Ɗansa domin ya nuna masa irin yadda Talakawa suke rayuwar su, da niyyar ko hakan zai sa ɗan nasa ya godewa Allaah Abisa arzikin da suke da shi. 

Sai da suka yi kwanaki uku a cikin gonar wani mutum da ya kasance talaka ne Matuƙa. Dama shi wannan talaka da iyalan sa duk a cikin gonar suke kwana. 

Yayinda suka shiga mota suna hanyar dawowa, sai wannan Attajiri ya dubi Ɗansa yace: "Shin ya ka gani ɗana? Yanzu ka Fahimci irin yadda Talakawa suke rayuwa ko? Sai yaron yayi murmushi yace; eh Baba na fahimta sosai. Da jin haka sai Attajirin yace:"Ko zaka iya faɗa min wasu abubuwa da ka ƙaru da su a cikin wannan tafiya? 

Yaron sai ya bashi amsa da cewa; “ na ga cewa muna da kare ɗaya ne jal a gidan mu, amma su suna da huɗu. Muna da tafkin ban ruwa da muke amfani da shi a gidan gonar mu Yayinda su kuma suke da kogin da bashi da iyaka. Muna da kyawawan fitilu masu haska mana gidan mu idan dare yayi waɗanda aka siyo su daga Kasar waje, Yayinda su kuma suke da Taurari a matsayin Fitilun su idan dare yayi. Muna da Fankacecen fili a cikin gidan mu, Yayinda su kuma suke da sararin samaniya gaba ɗaya. Muna da fili madaidaici wanda a cikin sa ne muka yi gini muka zauna a takure, Yayinda su kuma suke da fili iya ganin ka. Muna da boyi-boyi masu yi mana aiki, Yayinda su kuma su suke aikin da kansu. Mu kan siyo abinci ne Yayinda su kuma su suke shuka nasu da kansu. Mun zagaye Dukiyar mu da Katanga domin ta kare mu, Yayinda su kuma Allaah suka dogara da shi domin ya kare su!

Yayinda wannan Attajiri yaji wannan batu daga bakin Ɗansa, sai ya kasa yin magana. Daga Ƙarshe sai Ɗan ya ce da shi; "Nagode baba da ka nuna min Zunzurutun Talaucin da muke ciki. 

DARASIN LABARIN: Allaah yayi wa kowa baiwa da ni'ima irin wacce ta dace da shi, kada ka yi tunanin wani ya fi ka jin daɗi kawai don hakan ya bayyana a fili. Rayuwa tana da fuskoki da yawa, wani abun baka fahimtar kana da shi har sai ka rasa, Yayinda wani kuma baka fahimtar yafi ƙarfin ka har sai ka nema.


<••••••••••••••••••••••••••••>
      ɧãımãŋ Řâééʂ  
<••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees 
Instagram: Haimanraees 
Infohaiman999@gmail.com

Miyan Bhai Ki Daring


Post a Comment (0)