AERODYNAMICS

Menene Aerodynamics?
.
Aerodynamics kalmomi biyu ne, aka hada suka bada
wannan kalma. Aero yana nufin abun da yashafi iska(air)
ko kuma iskar kan ta, shi kuma Dynamics yana nufi motion
na abu da kuma forces nashi.
.
Aerodynamics a takaice yana nufin kimiyar tafiyan abu
acikin fluid. Idan akace fluid ana nufin abu kaman iska ko
ruwa. Fahimtar wannan kimiya tabada gudunmuwa wajen
tafiyar da kayan sufuri acikin iska, da cikin teku, da kuma
cikin sararin samaniya kaman jirgin sama da jirgin ruwa na
yaki.
.
A duk lokacin da abu yake tafiya acikin fluid dole ne zaka
samu yana fuskantar kalubale ko turjiya(resistance) daga
wannan fluid din. Kaman yanda nayi bayani asama idan
akace fluid ana nufin abu kaman ruwa ko kuma iska. To
lokacin da abu yake tafiya acikin fluid zaka samu yana
fuskantar kalubalen da zaisa karfin gudunsa ya ragu.
.
Misali idan kana tuka mota daga gabar kayi yamma. Sai a
lokacin kuma iskar daga yamma take tanayin gabar. Kaga
kenan wannan iskar tana kalubalantar tafiyar motarka. To
jirage ma yayin da suke tafiya acikin iska suna fuskantar
irin wannan barazana da kalubale, wanda hakan zaisa
jirgin yayi descend.
.
Descend yana nufin gudun jirgi yarage, wanda zaisa
yafado kasa. Aerodynamics ilimin kimiyane wanda gaba
daya yana bayanin tafiye tafiyen abubuwa acikin fluid.
Samun wannan ilimin yakawo cigaban sifirin sararin
samaniya da tafiyar da jiragen ruwa kaman nuclear
submarine wato jirgin ruwan yaki da mutane masu nutso a
teku wadanda ake kira divers.
.
Idan muna biye da kafafen daya labarai, wasu lokutan
zamuji an sanarda cewa tafiye tafiyen jiragen da aka tsara
an sokesu saboda matsalar yanayi. Wannan yana faruwa
ne saboda ana tunanin karfin iskan yayi yawa wanda zaisa
asamu matsala yayin da jirgi yake sama, ko kuma jirgin
yabace gaba daya daga taswiran masu kula da shi.
.
Aerodynamics bawai jirgin ruwa da jirgin samane kadai
yake magana akai ba - hatta mota da mashin da keke da
suke tafiya akan titi suma haddasu, saboda akan titin ma
akwai iska.
.
Abun dayasa nake bada misali da submarine wato jirgin
ruwa na yaki, shine shi submarine yana iya kwanaki
casa'in(90days) ko sama da haka acikin ruwa idan ya
nitse bai leko sama ba. Kuma yana iya yafiya acikin ruwan
bayan ya nutse kaman yanda kada(crocodile) take tafiya
bayan ta nitse acikin ruwa, yanda ba'a gane cewa akwai
wani abu acikin wannan ruwan.
.
Daga karshe muna barar addu'arku ga dan uwa Malan
Real Zaharaddeen M Kt akan Allah yabashi lafiya.
.
Dalibin Physics
Nura Mahdi Idris
Post a Comment (0)