HARAMCIN RUBUTA ALƘUR'ANI DA TRANSLITERATION


*HARAMCIN RUBUTA AYAR AL-QUR'ANI DA HARRUFANDA BANA LARABCI BA*
.
    *(TRANSLITERATION)*

FITOWA (1).
*Suleiman Yunusa Alkali*

Da Sunan Allah Me Rahama, Me Jinķai.
Tsira su tabbata ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W tare da Ãlayensa da Sahabbansa Da Waďanda Sukayi Koyi Dasu Har Zuwa Ranan Sakamako (Allah Yasa Damu Cikinsu).
     Tabbas Al-Qur'ani maganan Allah Ne kuma Shari'arSa wanda Ya saukar wa Annabi Muhammad S.A.W ta hanyar Mala'ika Jibrilu a harshen *Larabci* kamar yadda ko wani musulmi ya sheda wannan, duk da cewa akwai yararruka masu yawan gaske kuma Allah Yasan dasu tunda Shine Mahaliccinsu amma kuma sai Ya zabi yare ďaya tak ya saukar da Al-Kur'ani dashi wanda shine yaren *Larabci*.
       Hakan yasa wasu daga cikin Ajamawa (Duk wani yare wanda ba larabci ba Ajami ne) sukayi ta koyan karatun Al-kur'ani da wannan yaren na *Larabci* tun daga kan Sahabbai har magabata har rana ata yau domin kuwa a cikin sahabbai akwai dayawa wadanda ba larabawa bane amma dole suka koyi Qur'ani da *Larabci* basu koya da yarensu ba (Kamar su Bilal), a cikin magabata ma gasu nan birjik amma duk da hakan babu wanda ya taba koyan kira'a da rubutun yarensa duk da cewa sunada yare amma kowa da larabcin ya koya.
        Saida mukazo wannan zamanin sai wasu suna ganin karanta Qur'ani da *Larabci* yana wahalar dasu saboda haka sukayita rubuta Qur'ani da yarensu, hakan yasa Malluman Duniya suka zauna suka duba halaccin yin haka đin amma *Kashhh* basu samu hujjoji da suka halatta hakan ba saide hujjoji da suka haramta yin hakan.
      Hujjojin kuma sun haďa da *Ayoyin Qur'ani, Da Nassosin Hadisai da Ijma'in Malluma magabata da kuma na yanzu Maganganun Masu fatawa na duniya a baya da kuma yanxu da maganganun ďaiďaikun Malluma da ake lura da maganganun su a duniyar ilimi.
     Hakan yasa nayi alwashin yin wannan rubutun domin ya shiga kowa birni da kauye ta hanyar wannan kafar ta sadarwa domin kuwa;---
    1. Muna fama da wannan matsala sosai musamman a arewacin Najeriya wanda Malluman Islamiyya sun fini sanin hakan.
     2. Idan muka doge a hakan zamu riķa karanta Qur'ani muna samun zunubi ko la'anta maimakon lada.
    3. Zamu dinga chanza maganganun Ubangijin mu da sunan nimam sauki wanda hakan ze kai ga mutum zuwa ga halaka.
*Allah Ya Tsare Mu*
      Hakan ne yasa naga muhimmancin yin wannan rubutun, sannan zanyi kokarin bin qa'idodi kamar haka;---
1. Gabatarwa (wanda gashi mun gama dashi da izinin Allah).
2. Ayoyi da suke nuni akan haramcin yin *Transliteration*
3. Hadisai masu haramta a hakan.
4. Maganganun Magabata.
5. Fatawar Malluman duniya.
6. Ķadan daga cikin maganganun manyan Malluman duniya akan hakan.
7. karkarewa.
           Da wannan ne nake rokon Allah Ya bani ikon yin wannan rubutu da ikhlasi kuma Ya amfanar damu da abunda ke ciki har lahirarmu bayan duniya domin *SHI* Me ikone akan hakan.
.
Sai ku biyomu dan jin waďannan ayoyi da muke magana akansu.
Post a Comment (0)