BAYANIN AURE DA SAKI DA MAJIƁINTANSU 07


BAYANIN AURE DA SAKI DA BIKO DA ZIHARI DA LI'ANI DA KHUL"I DA SHAYARWA.

Fitowa ta 007

Ci gaba da bayani daga inda muka tsaya: SAKI 3 a Kalma daya. Wanda duk ya Saki Matarsa Saki Uku a Kalma 'daya ya Aikata Bidi'a. Amma kuma Sakin ya Tabbata. Wannan matar ta haramta gare shi har sai taje ta auri wani Namijin ba shi ba.
    Amma a Wannan Zamanin an samu wasu malamai suna kafa Hujjojin cewa ai Auren na nan zaa iya maidashi Saki daya, wannan kuskure ne babba, saboda Saki ya tabbata kuma babu wani hanyar da za'a gyara shi idan ba dai ta sake auran wani kuma sahihim Aure bawai Auren bayan wata guda ka sakemin Matana Zan sake auren ta ba. Daman Annabi Muhammad Saww, yana cewa, Nan gaba Malamai zasu Halattawa Jama'a yin Zina karara, kuma gashi a yanzu tana faruwa: bawai malamai zasu ce muku kuje kuyi Zina yin shi Halal bane, a'a ta gefen Yin Saki uku ne zasu halatta muku yin Zina, domin duk Wanda yayiwa Matarsa Saki Uku kuma a Kalma daya matar ta saku, kuma a yanzu babu wani aure a tsakanin su, toh idan an ce an gyara Auren daga Saki Uku ya koma daya don haka kuje ku ci gaba da Zama a matsayin Miji da Mata. Babu shakka indai kun je kun ci gaba da zama a haka Har kana iya Saduwa da Matar. Toh wallahi Zina kawai kuke yi ba Aure ba. Saboda a yanzu ta haramta gareka, dalilin wannan sakin da akayi mata. Ke kuma a matsayin ki na Mace komin son da zakiyiwa Mijin ki a lokacin da Saki Uku ya shiga tsakanin Ku, kada ki yadda ki sa ke ki koma gidan shi, idan bawai kin sake yin wani Auren ba ne, ki ce ke zaki koma gidan Mijin ki na Da saboda an gyara Auren. Ki tabbata idan kin koma gidan shi toh zaman Zina kuke yi ba Aure ba. Dolen ki, ki hakura har lokacin da Allah zai kawo miki Miji kiyi Aure kuma Sahihim Aure ba Shiri ba. Idan kinyi auren ace Mijin ne yace ya gaji da zama dake saboda haka ya Sake ki. Shikenan zaki iya dawowa gidan tsohon Mijin ki Ya Aure ki. Amma idan bahaka ba koda plan kuka shirya wani ya Aureki daga baya sake ki domin ke ki koma gidan Mijin ki, har gobe kuna gidan Jiya ne, Wajibi ne a kanku Ma'aura biyu kuyi koyi da Sunnah wajen Sakin Matan ku, kada kai ka biyema Sharrin shedan da son zuciyar ka, ka Saki matar ka Saki Uku a kalma daya kace kuma kai yanzu kana son ta dawo, ai babu dawo kam

Saki na Sunnah yin shi Halal ne, shi ne a Saki Mace Saki daya kuma a lokacin tana cikin tsarkin ta, Wanda baka Sadu da ita ba.
   Sannan ba zai sake yin wani sakin ba har sai iddarta ya kare, yana da damar yin Bikon wadda take yin haila muddin dai ba ta shiga haila na uku ba, idan Mijin ki ya sake ki bayan sati biyu ko kwana ki kadan ne, ya zo yace shi fah ya mai dake, toh fah kin koma a yanzu ke matarsa ne, ko iyayen ki na son komawan ki ko ba su so, indai yace yau ya mai dake toh kin dawo Matarsa, sai dai idan ya sake cewa ya Sake ki. akwai Wanda wai idan Mijinta ya Sake ta, kuma ya zo yace shi ya mayar da matarsa iyayen Matar ko yan Uwanta basu yadda Matar ta sake komawa gidan wancan, ah haka zasu hanata a karshe kawai sai a daura mata Aure da wani mijin dabam ba tare da ta koma gidan Mijin ta ba. Kusani cewa duk Wanda yayi irin wannan Jahilcin, toh fah ya Daura Aure akan Aure. Kuma Mijinta na farkon nan yana da dama ya kaisu kotu alkili yabashi Matar shi yadawo da ita gidan shi, kuma idan suka kuskura sukayi Jima'i har Matar ta Haihu toh 'Dan wancan ne ko yara nawa suka Haifa yaran wancan ne saboda Matar shi ne, saboda daman shi bai sake Furta wani kalman Saki gareta ba, aka Aurar da ita. Saboda Haka Shari'a ta bashi wadannan Yaran, nashi ne, wajibi ne ga iyaye su san Shari'a kafin nan su yanke hukunci akan Aure. Saboda Ana yin kuskure mai girman gaske, wani ya rabu da Matar sa tun ba yau ba, amma har gobe suna tare a matsayin Ma'aurata kuskure ne kuna aikata Zina ne kawai.

Idan 'ya ce, bata yi haila uku ba, zaka iya maida Matar ka, idan kuma ba ta yin Haila saboda yarinya ce ko kuma shekarunta sun wuce na yin Haila,
    Toh sai ya sake ta duk lokacin da ya ga dama, Saboda haka bara ka Sadu da Matar ka a yau anjima shedan ya shiga tsakanin ku nan take kace ka Saketa ba, wannan kuskure ne. Haka nan mai ciki ita ma a iya Sakin ta a ko wanne lokacin mutum ya so, Ana iya komar da Mai ciki muddin ba ta haihu ba, amma idan kabari har ta Haihu toh sai sabon Aure, ko a yau ka sake ta matukar baka ce mata ka komar da ita da yamma can ba, da safe sai ta haihu, toh ta fita daga Matar ka. Sai ka sake biyan wani Sadaki a daura muku Aure kafin nan ta zama Matar ka, saboda haka shi iddar mai ciki a lokacin da aka saketa, shine ta haihu, da zarar ta haihu ta fita daga iddarta.

Ita kuma yin idda da watanni, Ana iya komar da ita muddin iddar ta bai kare ba, abin nufi da Alkar'u shine tsarki. An hana sakin Mace a cikin haila kaman yadda mukayi bayani a Sama, idan kuma yayi Saki din to sakin ya tabbata,
   Amma za a tilasta masa ya komar da ita muddin iddarta bai kare ba. Wadda bai Sadu da Matarsa ba kuwa, ya iya Sakin ta duk lokacin da ya ga dama. Saki daya yana mayar da ita ko biyu, amma ba'ina, Saki uku kuwa yana haramta sai bayan wani Auren. Wanda yacema matarsa, ke sakakkiya ce, toh yayi Saki daya ne a kansa, har sai in yayi niyyar fiye da haka, yan Uwa Musulmai muyi Hattara Aure ba abin wasa bane______

Ku biyo mu a fitowa ta faba in Allah yakaimu.

Daga Zauren Muslim Women Mata Zallah
WhatsApp Group.

Muhammad Tukur Jalingo
Domin Shiga Wannan Group Zaki Iya Turo Mana Da Cikakken Sunan Ki Da Jihar Ku Ta WhatsApp Namu Mai Dauke Da Wannan Number
08164223447.
This Group Is Only For Women Please.
Post a Comment (0)