KU AURAR DA 'YA'YANKU IDAN SUN BALAGA


KU AURAR DA ƳAƳAN KU (Maza ko Mata) IDAN SUN BALAGA....
.
.قال عمر بن الخطاب رضي الله عنه:

 *"زوجوا أولادكم إذا بلغوا، لا تحملوا آثامهم".*

ذكره ابن الجوزي في أحكام النساء ص 304

وذكر ابن الجوزي عن بعض السلف أنه قال: "كان يقال العجلة من الشيطان إلا في خمس، إطعام الطعام إذا حضر الضيف، وتجهيز الميت إذا مات، *وتزويج البكر إذا أدركت*، وقضاء الدين إذا وجب، والتوبة من الذنب إذا أذنب" (أحكام النساء ص304).
.
Ma'ana:
Umar dan Khaddab (r.a) yace: "Ku aurar da yaranku [maza ko mata] idan sun balaga, kar ku dauki zunuban su". [Ma'ana, idan suka lalace laifi na kanku].
.
Sannan Ibnl Jauziy (r.h) yace:........ "ya kasance ana cewa gaggawa daga shaidan ne, amma ban da gurare 5...". Daga ciki yace: "aurar da mace da zarar ta kai".

Ahkamun Nisa', shafi na 304
.
Sun fadi wadannan maganganu shekaru aru-aru. Yau an wayi gari maza da mata na cikin sha'awa da lalacewar da suna bin wasu hanyoyi don kauda sha'awar su a boye inda iyaye ko wasu ba za su gan su ba, saboda rashin aure. Musamman yanzu lokacin wayoyin Android.
*"Dukkan Ku Masu Kiwo Ne, Kuma Dukkan Ku Se An Tambaye Ku Akan Abinda Aka Baku Kiwo"*. Inji Annabi (s.a.w)
.
Ba'a taba al'ummar da sha'awa ta yi yawa cikinta ba kamar al'ummar da muke ciki. Yau idan ka nemi taba jikin mace se ka ga kamar daman jira take ka taba. Idan itama ta nemi taba jikin namiji se ta ga kamar daman jira yake ta taba. Sha'awa ta ko ina: ga waya; ga TV; ga kan layi da bakin titi da kasuwa. Ba'a son a yi auren kuma ana son a biya bukata. Wasu ko na son auren amma bidi'o'i sun dabaibaye auren sun tsadar da shi ya fi karfin talaka ko da mutumin kirki ne. *Allah Ya Kyauta*
.
Da na yi sharing wannan a WhatsApp, akwai wadanda suka ce min inama iyayen su su gani su kirasu a zauna maganar aure! Wannan zai nuna maka cewar wasu tsoron isarda maganar ga iyayen su ya hanasu magana, saboda ba'a bude musu kofar hakan ba. Ba'a tambaye su aka ji ra'ayin su ba. 
.
*_Abu muhd_*
*10/11/2018*
Post a Comment (0)