BAYANIN AURE DA SAKI DA MAJIƁINTANSU 09


BAYANIN AUREN DA SAKI DA BIKO DA ZIHARI DA LI'ANI DA KHUL'I DA SHAYARWA.

Fitowa ta 009

Ci gaba da Bayani daga inda muka tsaya: Ikon Sakin Aure a hannun Bawa yake ba a hannun shugabansa ba, babu ikon Sakin Aure ga yaro karami, Matar da aka mallaka mata lamarinta da wadda aka ba ta zabi, 
      Wato tsakanin zama da rabuwa gaba dayansu suna da damar yanke hukuncin da suka fi so muddin sunada mazaunin haka, amma shi Mijin yana da damar musu hukunci, da kuma wadda aka mallakawa lamarinta ta yanke idan ya wuce Saki daya, kaman misali kai kana tare da Matar ka, zama yayi dadi, kawai sai kace mata yanzu ka bata wannan damar ya zama hukunci gareta, cewa duk lokacin da ta so zata iya yankewa kanta hukuncin Saki, bi ma'ana ta Saki kanta da kanta, toh idan yau tace ta Saki kanta, toh ta Saku indai ta furta da bakinta tace na Saki kaina, toh Sakin ya tabbata, inda Sakin barai tabbata ba, shine ita tace ta Saki kanta Saki uku kai tsaye, toh nan ne zaka iya yanke hukuncin ka, kace Kai daya ne ko Saki biyu, toh muddin ka bama matar ka wannan hukuncin a hannunta, ranan da ta bushi iska tace toh yau na Saki kaina Saki daya, toh saki ya tabbata Saura ma biyu kenan. amma ita wadda ake bai wa zabi ba ta da wani hukuncin da za tayi akan Saki uku, Sannan shi miji ba shi da ta cewa akai, indai ta furta saki daya, duk wanda yayi Rantsuwa akan cewa ba zai Sadu da Matarsa ba Har Sama da wata 4, to ya zama mai ila'i kenan, Saki ba zai tabbata a kansa ba sai bayan Wucewar Ajalin ila'in, Ajalin ila'i shine Wata 4 ga 'Da, wata 2 kuma ga Bawa, har zuwa lokacin da mai hukunci zai tsayar da shi. Duk Wanda yayi wa Matarsa Zihari, toh bai halatta ya Sadu da Matarsa ba, har sai bayan yayi kaffara ta hanyar 'yanta Baiwa Mumina wadda take Kubutacciya ga barin duk wani aibu,

Kuma ta zama babu tarayya a cikinta da wani, kuma babu wani kamshi-kamshin 'yanci a tare da ita, idan bai Sami Baiwa ko bawan da zai 'yanta ba, toh sai yayi Azumin wata 2 a Jere, idan kuma bai sami iko ba, sai ya ciyar da mabukata Sittin, ya bada Mudu biyu ga kowane mabukaci, kuma ba zai Sadu da ita ba da daddare ne ko Rana har sai kaffarar shi ta kare a kansa, idan kuma ya Sadu da ita Kafin ya gama kaffarar sa, sai ya tuba ga Allah mai Girma da Daukaka, idan ya gama da ciyarwa ko Yin Azumi, toh sai ya sake dauko ta daga tushe. Babu laifi a iya 'yanta Bawa ko Baiwa mai Ido daya ko Mara Uba a kaffarar Zihari, ko da yaro karami aka 'yanta ya isa, amma Wanda ya girma kuma ya isa yin Sallah da Azumi shi aka fi so a kaffara na Zihari______

Ku biyo mu a Fitowa ta in Allah yakaimu.

Daga Zauren Muslim Women Mata Zallah 
WhatsApp Group.

MUHAMMAD TUKUR JALINGO
Domin Shiga Wannan Group Zaki Iya Turo Mana Da Cikakken Sunan Ki Da Jihar Ku Ta Number WhatsApp Namu Kamar Haka
08164223447.
This Group Is Only For Women Please.
Post a Comment (0)