BAYANIN AURE DA SAKI DA MAJIƁINTANSU 10


BAYANIN AURE DA SAKI DA BIKO DA ZIHARI DA LI'ANI DA KHUL'I DA SHAYARWA.

Fitowa ta 010

Ci gaba da Bayani daga inda muka tsaya: LI'ANI; li'ani a tsakanin Namiji da Mata Ana yin sa ne a cikin Hukuncin kin karbar Ciki da aka yi da'awar tsarki kafin sa, ko kuma mijinta na ganin ta ita Matar tana yin Zina da wani kuru-kuru ba Jita jita ba, wato ka ganta kamar Mashiyyi(Mashi) a cikin kuratandu. Ko kaman turmi da tabariya,
       An yi sabani a cikin tsayar da hukuncin Li'ani saboda Kazafi, idan Miji da Mata suka rabu ta hanyar Li'ani, to ba za su sake yin Aure ba har Abada. Idan suka zo yin Li'ani sai Mijin ya fara, ya ba da shaida Sau 4 tsakani da Allah cewa lallai ba cikinsa ba ne, wannan Cikin wani ta hanyar Zina, ko ya gan ta tana yin Zinan, sannan ya cika shaida ta biyar da cewa: idan ba haka ba ne, Allah ya tsine masa,

Sannan kuma ita Matar ta zo ta bayar da Shaida 4 itama, ta cika ta biyar da cewa: idan ba haka ba ne, Allaha yayi Fushi a kanta" kamar dai yadda Allah mai tsarki da daukaka ya fada a cikin Al Qur'ani.
    Idan Matar ta ki bayar da shaidar bayan Mijin ya bayar sai a Jefe ta idan katangaggiya ce, mai Aure ce ko kuma a yi mata Bulala Dari idan ita ba katangaggiya ba ce, idan kuma Miji ne yaki bayar da shaidar sai a yi masa Bulala Tamanin haddin Kazafi kenan kuma Shari'a ta ba shi dan, wato idan an yi Mai bulala tamanin saboda yayiwa Matarsa Kazafin yin Zina sai a dauko Dan a ba shi, Mace tana da damar ta fansa kanta daga Mijinta ta hanyar Mayar masa da Sadakinta Wanda mijin ya bata, ko abin da bai kai Sadakin ba ko kuma wanda yafi Sadakin nashi, idan bai kasance cutarta yake yi ba, idan kuwa ya kasance cutarta yake yi toh Khul'i ya tabbata kuma lallai ya Mayar mata da Sadakinta__________

Ku biyo mu a fitowa ta gaba in Allah yakaimu.

Daga Zauren Muslim Women Mata Zallah
WhatsApp Group.

MUHAMMAD TUKUR JALINGO
Domin Shiga Wannan Group Zaki Iya Turo Mana Da Cikakken Sunan Ki Da Jihar Ku Ta Numbern WhatsApp Namu Kamar Haka
08164223447.
This Group Is Only For Women Please.
Post a Comment (0)