HUKUNCIN ISKAR DA KE FITA DAGA GABAN MACE


Tambaya
:
Mene ne hukuncin Iskar da ke fita ta Farjin Mace Shin tana karya alwala ko a'a??
:
Amsa:
:
Malamai Ma'abota Ilimi sunyi Saɓani Dangane da hukunci akan Iskar dake fita ta gaban Mace, Mazhabin Hanafiyya da Malikiyya Sun tafi ne a kan cewa dukkan wani abu da zai fita ta gaban Namiji ko kuma ta gaban Mace wanda kuma asali abisa al'ada ba tanan ba ne hanyar fitarsa, wato kamar irin iskar da take fita ta farjin Mata a waɗan su lokuta ko kuma tsakuwa ko tsutsa ta fita ta wajen Malamai sukace irin wannan ba ya warware alwala, domin wannan Iskar ba daidai take da Tusa ba, Sannan sukace ba a samu wani Nassi afili Ƙarara da yake nuna cewa wannan Iskar tana warware alwala, domin Mαnzon Allαh(ﷺ) cewa yayi:
:
"لا وضوء إلا من صوت أو ريح"
(رواه الترمذي)
MA'ANA:
Ba a sake alwala Sai dai idan anji Sautin (fitar tusa) ko kuma anji warin (tusar):
:
Amma Mazhabin Shafi'iyya da Hanabila Sukace dukkan wani abu da zai iya fita ta Farjin Mace ko Zakarin Namiji koda kuwa a bisa al'ada ba hanyar fitarsa bace kamar irin wannan Iskar ko wani abun da yake Nadiran (abinda ba a saba gani yana fita ta wajen ba) sukace dukkan waɗannan abubuwa suna warware alwala, Sannan ita kuma iskar dake fita ta Farjin Mace sunyi kiyasin ta ne da tusar dake fita ta dubura, sukace tunda dai tusa tana karya alwala to duk hukuncinsu yazama Ɗaya da na tusa kenan, danhaka dole a sake alwala.
:
Amma zance mafi inganci shine dukkan wata iska da zata iya fitowa daga gaban Mace to bata warware alwala, amma inda ta fita ne daga duburarta to ko Shakka babu alwala ta warware domin dukkan Malamai Sunyi ijmā'i akan cewa tusar dake fita ta dubura tana karya alwala danhaka dole sai an sake wata kenan, Sai dai wasu daga cikin Malamai sukace idan Mace taji wannan iska ta fito daga Farjinta to abu mafikyau shine ta sake alwala don ta kubuta daga cikin Sabanin da Malamai sukayi
:
※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※
:
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
              Daga Zaυren
             Fιƙ-нυl-Iвadaт
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
           Mυѕтαρнα Uѕмαи
              08032531505
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/
Post a Comment (0)