SHIN KANA AFUWA KUWA?


SHIN KANA AFUWA KUWA?

Mu karrama wadan da ke son mu, da daddadar kalma da kyakkyawan mu'amala, domin bamusan wanda mutuwa zata fara dauka ba a tsakaninmu.

 Saboda wallahi shaukin bayan mutuwa abu ne mai ciwo da zuciya take wahaltuwa akanshi !!!

 Inama banyi ma wane kazaba.... 
Inama nayi hakuri lokacin da tayi/yayi min kaza....

 Irin wannan shine galibin kalaman da zukata ke fadi yayin da rabuwa tashiga tsakaninmu da wadanda muke tare.

Rayukan mu, an halicce su domin su zauna na wani lokaci a duniya sannan su tafi.
 Yi murmushi.

 Yi afwa. 

Yi sassauci, mance da laifi ko batanci da aka taba yi maka a duniya wannan mai gushewa ne.

A rayuwa za'a iya samun sabani amma matukar a hanyar Allah ake rayuwa,ya kamata ace anbar abinda ya faru ya wuce.... 

Mu sassauta lafuza yayin sabani da bacin rai muyi amfani da lafuza masu sauki.

Mu raka amsar uzuri, domin ko sautin fashewan glass yana da saurin gushewa sai dai kananun kwalaben kan jima mutum ciwo komai dadewa haka mummunar magana take zaka ji sautinta na lokacin amma tana sosa zuciya lokaci mai tsaho!!!

Bai zama dole ka farantawa duk mutane rai ba amma yi kokarin ganin baka cutar da kowaba, da ka cuci wani, gara a cuceka.

 Allah yasa mu dace.
Post a Comment (0)