WATA MATA TA KASHE MIJINTA A MALUNFASHI

Da dumi duminsa jami'an yansanda dake karamar Hukumar malunfashi a jahar katsina sun damke wata mata yar shekara 19 da laifin kashe mijinta har lahira. Matar mai suna rabi Shamsudeen ta kashe mijnnatane mai suna Shamsudeen salisu dan shekara 25 da misalin karfe 4:00am na safiyar litinin tahanyar daba masa wuka. Lamarin yafarune a wani kauye mai suna danjaku dake karamar Hukumar malunfashi. Mai magana dayawun yansandan jahar katsina ne malam SP Gambo musa ne ya bayyana hakan a yayin ganawar shi da manema labarai Yace a biciken da sukayi basukai ga gano dalilin dayasa ita mai laifin ta aikata kisanba amma dai zasuyi bincike. Makwaftan Shamsudeen nedai suka jiyo ihunsa suka fito suka same shi rike da cikinsa yana Cewa ku taimake ni a YAYINDA ita kuma rabi take rike da wuka da jini a hannun ta to Allah ya kiyaye ya kumasa mufi karfin zuciyoyinmu. Ameen


Post a Comment (0)