NA KASANCE INA SHAYARWA

TAMBAYA
========
👇
Nakasance ina shayarwa kuma idda takamani ma Ana idan ina shayarwa banayin al,Ada to wai ance Zan kirga adadin kwanakin wasu kuma sunce sainabari harnayi yaye to Dan Allah malam yah,abinyake Allah yakara basira.

AMSA
======
👇
Ba haka bane.
Mace mai haila, iddarta shine, zatayi jini ukku kadai daga ranar da mijinta ya saketa.
Wadda jinin haila ya dauke Mata kwata-kwata, zatayi wata ukku daga ranar da mijinta ya saketa.
  Wadda take da ciki, da ta haife abinda yake cikinta, iddarta ta cika, koda kuwa aranar da mijinta din ne ya saketa.
  Wadda aka saketa tana shayarwa kuma bata yin jini har sai ta yaye Dan da take shayarwa, to zata jira har sai ta yaye wannan dan, sannan tayi jini ukku, anan ne iddarta ta cika.
  Wadda mijinta ya mutu, iddarta wata hudu da kwana goma, idan kuma tana da ciki, da ta haife wannan cikin iddarta ta cika.
  Wadda mijinta ya bata, zata jira wasu malaman sukace, shekara ukku, wasu sukace shekara biyu, wasu sukace sukara daya, wasu sukace ya danganta da bukatuwar wannan matar ga mijin aure, idan tana bukatar namiji, bayan an nemi mijinta ba'a sameshi ba, to Alkali zai bata takardarta Dan ta samu ta auri wani.

Allah shine masani.


ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876

Post a Comment (0)