BIKIN VALENTINE: RANAR MASOYA KO RANAR MAGUZAWA?
BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allaah mai girma da ɗaukaka. Tsira da amincin Allaah su ƙara tabbata ga Manzon Allahu, Annabi Muhammad sallallahu alaihi wa sallam, mutanen gidansa, sahabbansa da ma dukkan wanda ya biyo bayansu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.
GABATARWA
Bikin Ranar Masoya, watau Valentine's Day a turance kenan kamar yadda ake kiransa, biki ne da akan yi shagalinsa a kowace ranar 14 ga watan Afrilu, ma'ana dai sau ɗaya ake yinsa a cikin shekara.
Ita dai wannan rana, rana ce wacce miliyoyin mutane daga dukkan sassan duniya suke murnar zagayowarta a kowace shekara. Duk da cewa an ɗauki wannan rana a matsayin ranar murnar tunawa da wani waliyyin kiristoci ne mai suna Valentinus, irin wannan rana a yau ta kasance ana alaƙanta ta ne da bikin soyayya, nishaɗi da kuma jin daɗi a mafi yawancin wurare a duniya.
A irin wannan rana, masoya a ko'ina a faɗin duniya kan aikawa juna saƙonnin katuka, fulawoyi, kyaututtuka ko wasu abubuwa makamantan haka domin dasawa ko haɓaka alaƙarsu da juna. A ƙarƙashin haka, akan haɗu a bukukuwa da dama da akan tanada domin irin wannan biki a tsakanin samari da 'yan mata ko ma'aurata domin nunawa juna ƙauna, in da hakan ke kaiwa zuwa ga munanan kalamai waɗanda su kuma su ke kaiwa zuwa ga mummunan aiki. Allaah ya tsare mana Imaninmu.
GA JERIN WASU ABUBUWAN DA A KE YI A RANAR BIKIN VALENTINE.
*. Sanya jajayen tufafi tare da bayyana tsiraici.
*. Bayyanar da farinciki da jin daɗi a wannan rana, kamar yadda a ke yi a sauran bukukuwa.
*. Musayar jajayen fulawoyi waɗanda ke alamta soyayya.
* . Rubuta kalmomin soyayya da amfani da lafuzzan da ke motsar da sha’awa ajikin katin.
*. Aika da saƙonnin batsa da rashin kamun kai ta hanyar saƙo ko kuma ta hanyar wayar tafi da gidanka.
*. Musayar kyaututtukan da suka haɗa da fulawa da alawa da dai sauransu a tskananin ma’aurata ko samari da 'yan mata.
*. Aikawa da katin gaisuwa (greeting cards).
*. A wasu ƙasashen, akan shirya ƙasaitaccen biki inda mata da maza ke cakuɗewa da juna, a yi rawa, a yi shaye-shaye, ayi murna, wani lokaci kuma, a haɗa da masha’a.
Sai dai kafin mu tafi da nisa, bari mu ji taƙaitaccen tarihin shi wannan biki a farkon samuwarsa.
TAƘAITACCEN TARIHIN BIKIN VALENTINE
Daga ranar 13 ga watan Fabarairu har zuwa ranar 15 na wannan wata, maguzawan ƙasar Rum sun kasance suna yin wani bikin maguzanci da suke kira da Lupercalia. A yayin gudanar da wannan biki, mazajen cikinsu kan yanka akuya ko kare sannan su shafe jikunansu da jinin kuma su riƙa dukan matayen cikinsu da fatun dabbobin da suka yanka nan take ba tare da sun wanke jinin ba. A wannan biki, su kan sha kowane irin kayan maye su dinga yawo a cikin gari tsirara yayinda 'yan matan garin za su zo su jeru domin mazajen su zo su jibge su da fatun dabbobin da suka yanka.
Dalilin wannan duka kuwa shi ne, matan wancan lokacin sun yarda cewa yi musu wannan duka maganin rashin haihuwa ne kasadin.
Bayan an gama wannan, sai kuma a rubuta sunayen duk 'yan matan garin a saka a cikin tulu ko kofin gilashi. Daga nan sai samarin garin su dinga zuwa suna ɗaukan sunayen. Duk wacce saurayi ya ɗauki sunanta, to shikenan ta zama tashi a wannan biki, wasu kuma sanadin aurensu kenan. A irin wannan rana zina ba laifi ba ne a wurinsu. Wannan biki dai ya fara aukuwa ne tun kimanin ƙarnuka goma sha bakwai da suka gabata
Sai dai kuma kiristoci na wancan lokacin a Rum ba sa son irin wannan biki domin ya saɓa wa addininsu, hakan ya sa Faparoma Gelasius I (492–496) ya soke wannan biki na Lupercalia. Bayan ya soke wannan biki ne sai ya samar da wani sabon bikin, shi ne bikin tunawa da wani shahidin su mai suna St. Valentine wanda aka kashe a ranar 14th ga watan Fabarairu.
To amma me ya haɗa wannan biki na kiristanci kuma da bikin ranar masoya? Domin samun wannan amsa, bari mu je ga tarihin shi kanshi Valentine ɗin A taƙaice.
TAƘAITACCEN TARIHIN SAINT VALENTINE
Masana sun yi saɓani dangane da wane Valentine ne Paparoma Gelasius I ya ƙaddamar da wannan rana domin tunawa da mutuwarsa. Dalili kuwa shi ne: malaman kiristoci da su ka mutu da dama sunansu Valentine, sai dai akwai guda biyu da suka fita daban waɗanda kuma duk sun mutu ne a ranar 14th ga watan Fabarairu, ko da yake dai ba a shekara ɗaya bane.
Amma wanda aka fi danganta wannan biki da shi, shi ne Valentine na Rome. Shi dai wannan Valentine ɗin wani malamin addinin kiristanci ne wanda Sarki Claudius II ya sa aka kashe a cikin ta hanyar datse masa kai a cikin ƙarni na uku.
Zance mafi ƙarfi dai ya nuna cewa sarki Claudius II, wanda bamaguje ne ya haramtawa sojojin lokacinsa yin aure, saboda a cewarsa, tuzuran sojoji sun fi bayar da abinda ake nema daga sojoji fiye da masu aure. Sai dai duk da wannan doka da sarkin ya kafa, Saint Valentine sai ya ci gaba ɗaurawa sojojin aure a ɓoye, wannan dalili ne ya sa aka kama shi kuma aka kashe shi. Wannan kisa da aka yi masa ne ya sa aka dinga girmama shi a tsakanin 'yan uwansa kiristoci. Shi ma ɗayan Valentine ɗin dai ana tsammanin ya mutu ne a kan wannan dalili.
Sai dai kafin a kashe Valentine, a yayin da ya ke zaman kaso, ya kamu da son 'yar wanda ya sa aka kama shi. To a cikin kurkukun ne ya rubuta mata wasiƙa tare da bayyana mata irin son da yake mata. A ƙarshen wasiƙar ne ya sa hannunsa da cewa: “from your Valentine” (Ma'ana daga Valentine ɗin ki) wannan shi ne asalin yadda kalmar ta samu zama a cikin bikin masoya na duniya da ake yi a yanzu.
Wannan jajircewa ta Saint Valentine ya sa Cocin katolika suke girmama shi, har ma coci suka gina a cikin shekarar 350CE a inda ya mutu da kuma ta hanyar bikin ranar Valentine wanda a wancan lokaci biki ne na addininin kiristanci da a koyaushe ake jinjinawa Saint Valentine a matsayin wanda ya yaɗa ƙauna kuma ya ba soyayya muhimmanci a kiristance.
Hakan yasa da Faparoma Gelasius I ya zo sai ya yamutsa abun ta hanyar daidaita ranar bikin Valentine da kuma bikin Lupercalia domin ya daƙike bikin maguzawan Rum na wancan lokaci.
Sai dai ungula fa ba ta canja zani ba. Domin kuwa banbancin bukukuwan kawai shi ne su kiristoci suna sanya kaya kuma ba sa dukan mata da ɗanyar fata ne kawai, amma shaye-shaye ba'a daina shi ba, kamar yadda kuma ba'a daina alaƙanta bikin da ranar masoya ba.
KO MENENE HAƊIN BIKIN VALENTINE DA HOTON ƊAN YARO MAI FUFFUKE RIƘE DA KWARI DA BAKA?
Shi wannan yaro da akan ga hotonsa a jikin katukan bikin ranar masoya watau Valentine, a zahirin gaskiya ba yaro bane. Ɗaya ne daga cikin ababen bautar Rumawa da a turance ake kiransa da Cupid. Shi ɗa ne ga abar bautar So da kuma kyau wato Venus. Ya shahara matuƙa a labaran kunne-ya-girmi-kaka inda ake cewa yana harbin mutane da aljannu da kibiyarsa ta so wanda hakan ke sa mutum ya ji kawai nan take ya kamu da son wani. Daga cikin dalilan da suka sa ake sanya shi a jikin katukan saƙonnin bikin Valentine kuwa shi ne, saboda masu aika saƙon suna fatar ya harba kibiyar ta soki zuciyar wanda suka aikawa da saƙon domin ya kamu da son su. Allaah ya kiyaye mu.
BIKIN RANAR MASOYA A MUSULUNCI.
Manyan malaman Musulunci na wannan zamani kaf sun aminta dangane da haramcinsa, kamar yadda majalisar malaman Saudiyya duk sun haramta wannan biki bisa madogara ta shari'a. Domin Addininmu ya hana mu yin tarayya da kafurai a bukuwan da suka kebanta da su. Baya ga kamanceceniyar da wannan zai haifar ta wannan ɓangare tsakanin musulmi da waɗanda ba musulmi ba, shi wannan biki ta kowace fuska in ka kalle shi yana keta alfarmar shari’ar musulunci ne, bugu da ƙari akwai fasadi mai yawa da wannan biki ya ƙunsa domin kuwa su kansu kiristocin suna ƙorafi da wasu munanan abubuwan da ake aikatawa a irin wannan rana.
Tunda kuwa hakane, to babu shakka dole mu ƙauracewa wannan biki.
Saboda faɗin Allaah ta'ala:
بِسمِ اللَّهِ الرَّحمٰنِ الرَّحيمِ
۞ يا أَيُّهَا الَّذينَ آمَنوا لا تَتَّخِذُوا اليَهودَ وَالنَّصارىٰ أَولِياءَ ۘ بَعضُهُم أَولِياءُ بَعضٍ ۚ وَمَن يَتَوَلَّهُم مِنكُم فَإِنَّهُ مِنهُم ۗ إِنَّ اللَّهَ لا يَهدِي القَومَ الظّالِمينَ
Ya ku waɗanda suka yi imani! Kada ku riƙi Yahudu da Nasara majiɓinta. Sashensu majiɓinci ne ga sashe. Kuma wanda ya jiɓince su daga gare ku, to, lalle ne shi, yana daga gare su. Lalle Allah ba Ya shiryar da mutane azzalumai.
(Ma'ida: 51)
لا يَتَّخِذِ المُؤمِنونَ الكافِرينَ أَولِياءَ مِن دونِ المُؤمِنينَ ۖ وَمَن يَفعَل ذٰلِكَ فَلَيسَ مِنَ اللَّهِ في شَيءٍ إِلّا أَن تَتَّقوا مِنهُم تُقاةً ۗ وَيُحَذِّرُكُمُ اللَّهُ نَفسَهُ ۗ وَإِلَى اللَّهِ المَصيرُ
Kada muminai su riƙi kafirai masoya, baicin muminai. Kuma wanda ya yi wannan, to, bai zama a cikin komai ba daga Allah, face fa domin ku yi tsaro daga gare su da 'yar kariya. Kuma Allah yana tsoratar da ku kana. Kuma zuwa ga Allah makoma take.
(Ali Imran: 28)
Kuma manzon Allah Sallallahu alaihi wa sallam yana cewa:
“Dukkan wanda yayi kamanceceniya da wasu mutane, to yana cikin su”.
Kenan wannan hujja ce ƙarara kan haramcin yin wannan biki. Allaah ya ganar da mu.
ME YA KAMATA MUSULMI SU YI DANGANE DA RANAR BIKIN VALENTINE?
1. Da farko dai duk wani musulmin kirki ya kamata ya nuna ƙiyayyarsa ga wannan biki ko tarayya a cikinsa ko halartar wurin da a ke yinsa.
2. Ƙauracewa ko bijirewa duk wata ƙofa wacce za ta taimaka wajen ci gaban wannan biki ta kowace fuska.
3. Bayyanar da ƙyamar bikin a fili tare da ƙin shiga duk wani abu da ya jiɓince shi.
4. Kada ka/ki yi wa kowa murnar ranar kuma ko an maka kada ka amsa, in ma da hali ka zaunar da mutum ka bayyana masa dalilanka na ƙin wannan bikin.
5. Yi wa Juna NASIHA dangane da wannan kauce wa irin wannan biki.
A ƙarshe, ina roƙon Allaah da Ya tsare mu da tssrewarsa, Ya karemu da karewarsa, Ya shiryar da mu daga Shiriyarsa, kuma Ya azurta mu da kyakyawar fahimta. Ya Allaah ka yi mana maganin abinda ya fi ƙarfinmu, Ka yafe mana laifukanmu kuma ka azurta mu da gidan Aljanna.
Aameen Thumma Aamen.
•----------•✬(✪)✬•----------•
Jamilu Abdurrahman
•----------•✬(✪)✬•----------
+23481858191
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Twitter: @jamiluwriter
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Instagram: Jamiluwriter
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Facebook
https://m.facebook.com/JamiluWriter
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Tumblr: Jamiluwrite
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Bakandamiya: Jamilu Abdurrahman
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Telegram: https://t.me/Jamiluwrite
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
LinkedIn: https://www.linkedin.com/in/jamilu-abdurrahman-36b88211
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Haimanraees@gmail.co
──────⊹⊱✫⊰⊹──────m─8─r─ ─r─/:─ ─ ─76•
Jamilu Abdurrahman
•----------•✬(✪)✬•----------
+23481858191
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Twitter: @jamiluwriter
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Instagram: Jamiluwriter
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
https://m.facebook.com/JamiluWriter
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Tumblr: Jamiluwrite
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Bakandamiya: Jamilu Abdurrahman
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Telegram: https://t.me/Jamiluwrite
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
LinkedIn: https://www.linkedin.com/in/jamilu-abdurrahman-36b88211
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Haimanraees@gmail.co
──────⊹⊱✫⊰⊹──────m─8─r─ ─r─/:─ ─ ─76•