Corona Na Iya Shiga Makkah Da Madinah?
Daga Malam Zakariyya Shu'aib Adam
Bayan hukumomin Saudiyya sun fitar da sanarwar dakatar da Umrah zuwa wani lokaci saboda Covid-19, cece-kuce ya kaure tsakanin mutane kan ko yana yiwuwa Covid-19 ta shiga Makkah da Madinah ko a'a? Masu ganin cewa cutar ba za ta iya shiga waɗannan garuruwa biyu masu alfarma ba na kafa hujja ne da hadisin da Bukhari (1880) da Muslim (1379) suka rawaito cewa Annabi (SAW) yace:
(عَلَى أَنْقَابِ الْمَدِينَةِ مَلَائِكَةٌ لَا يَدْخُلُهَا الطَّاعُونُ وَلَا الدَّجَّالُ)
(Akwai wasu mala'iku tsaye a ƙofofin Madinah, annoba da Dujal ba za su shige ta ba)
Duba da wannan hadisi, mutum na iya cewa: annobar corona ba za ta iya shiga Makkah da Madinah ba.
A wani hannu kuma, wasu daga cikin mallamai na ganin cewa annobar corona na iya shiga garuruwan, shi yasa ma mahukuntar ƙasa mai tsarki suka dakatar da yin Umrah don gudun kada wani daga wata ƙasa ya kai cutar harami. Waɗannan mallamai na ganin cewa wancan hadisi na sama, yana nufin wata annoba ce ƙayyadadda, ba duka annoba ba.
Shi yasa mallaman suke cewa: akwai bambanci tsakanin الطاعون (Aɗɗá'ún) da kuma الوباء (Al-wabã'). A duka hadisan, Annabi (SAW) cewa yayi: الطاعون, bai ce الوباء ba.
Dalilan da ke ƙarfafa cewa corona na iya shiga Makkah da Madinah da kuma cewa akwai bambanci tsakanin الطاعون da الوباء, suna da yawa, amma ga kaɗan daga cikinsu:
1) Ahmad da Ɗabaraniy da Abu Ya'ala sun rawaito hadisi daga Aisha (RA) ta tambayi Annabi (SAW) kan ma'anar الطاعون, sai yace:
(غدة كغدة البعير يخرج في المراق والإبط)
(Kumburi ne irin na raƙuma, yana fitowa a ciki da hammata)
Dangane da ma'anar الطاعون a yaren larabci kuwa, An-Nawawiy yace a cikin sharhin Muslim:
(الطاعون: قروح تخرج في الجسد فتكون في الآباط أو المرافق أو الأيدي أو الأصابع وسائر البدن، ويكون معه ورم وألم شديد)
(Addã'ún: daji ne (cancer) dake fita a jikin mutum. Yana kasancewa ne a hammata, gwiwar hannu ko hannu, ƴan yatsu da sauran jiki. Yana sabbaba kumburi da kuma zafi mai tsanani)
2) Shi kuwa الوباء, yana nufin annoba gamammiya dake shiga mutane da yawa kuma take aukuwa a garuruwa da yawa. Ya zo a cikin "Al-Mu'ujamul Ma'aniy" cewa:
(الوباء: كل مرض شديد العدوى، سريع الانتشار من مكان إلى مكان، يصيب الإنسان والحيوان والنَّبات، وعادةً ما يكون قاتلا)
(Al-Wabá'u: Duk wata cuta mai tsananin tashi daga wani zuwa wani (infectious), mai saurin tashi daga wani wuri zuwa wani. Tana shiga mutum, dabbobi da kuma tsirrai. Tana kisa a al'adance)
Ibnu Hajar ya hakaito maganar Iyád a cikin Fathul Bári cewa: "Duka الطاعون, to الوباء ne, amma ba duka الوباء ne الطاعون ba." Wannan itace fahimtar Ibnul Ƙayyim a Zadul Ma'ad.
3) Abinda zai ƙara fito maka da cewa corona, a matsayinta na الوباء, tana iya shiga Makkah da Madinah domin ba الطاعون bace, hadisin da Bukhari (2643) ya rawaito daga Abul Aswad:
(أَتَيْتُ الْمَدِينَةَ وَقَدْ وَقَعَ بِهَا مَرَضٌ ، وَهُمْ يَمُوتُونَ مَوْتًا ذَرِيعًا)
(Na zo Madinah (a zamanin Umar (RA)), alhalin wata cuta ta shigo garin. Mutane na mutuwa da sauri)
Wannan hadisi yana nuna cewa annoba gamammiya na iya shiga garin Madinah tun da gashi mutane sa yawa sun mutuwa cikin ƙanƙanin lokaci. Amma الطاعون ba zai iya shiga ba saboda akwai mala'iku da za su kare garin.
4) A likitance, الطاعون shine Plague. Plague epidemic ko pandemic bacterial infection ne da ke samun mutane da wasu dabbobi. Itace cuta mafi kusa da fassarar da Annabi (SAW) ya gayawa A'isha, wacce Imam Nawawiy ya faɗaɗa. Daga cikin alamomin plague, akwai kumburin lymph nodes, musamman na hammata (axillary lymph node) da kuma wuya.
Plague ana kamuwa da ita ne ta hanyar cizo daga infected fleas, ko kuma yayin mu'amala da dabba mai ɗauke da cutar.
Shi kuma الوباء, yana nufin mujarradin epidemic ko pandemic disease ba tare da lura da cewa Plague ne ko ba Plague ba. Ka ga Plague cuta ce da bacteria ke sabbabawa (Yersinia pestis), amma ita الوباء tana iya samuwa ta dalilin bacteria (kamar Plague, Cholera Leptospirosis) ko kuma virus (kamar Covid-19, Ebola, Influenza).
A taƙaice, wannan bayani na nuna cewa Covid-19 ba الطاعون bace, الوباء ce. Kenan tana iya shiga garuruwan Makkah da Madinah. Saboda haka, mahukuntan Saudiyya sun yi daidai da suka dakatar da Umrah har zuwa wani lokaci da Allah zai yaye cutar. Abinda zai ƙara tabbatar maka da haka shine: A yanzu haka, akwai cases 103 na Covid-19 da aka tabbatar a Saudiyya. In da ace Covid-19 itace الطاعون, to da tabbas ba za ta shiga Makkah da Madinah ba.
Allahu A'alam
Rubutawar Mal. Ibrahim Khalil Abdullahi