GUMBAR BAURE
`
Kamar yanda jarumta ke gan gaba a fagen yaki
haka zalika gidan aure hakuri ke kan gaba,
haryanzu babu mace wanda take kalubalantar
miji tayi nasara a rayuwarta, mata masu
kimah da daraja zaka samu hakuri sukayi su
manta da neman 'yancinsu sukayi bauta a
gidan miji daga karshe suka bayyana masu
nasara,
zaman aure baya tasiri idan aka rasa saduwar
aure tsakanin miji da mata domin babu wata
alaka me hada jinin mata da miji sama dashi,
yayinda shikuma aka rasa ni,ima tofa komai
yanda kike wajen miji ahankali zai kaurace
miki bazaki tabbatar da hakanba sai hakan ta
faru dake,
ita kuma gumbar baure kusan daya take da
tsumin baure domin yanda aka samu tsumin
anan aka kirkiri gumbar wanda tun fil'azal
wasu matan suka riketa sama da tsumin dukda
cewar tsumin yafi saukin hadawa to amma saboda tafi bada ni,ima
a saukake yayinda gaban mace bazai zauna a bushe ba,
ita wannan anaso koda rabin cokali ki zuba
acikin shayi me lefton wanda babu madara
sannan ki zuba zuma bayan yadan dade kamar
mintuna biyar saiki gauraya kishanye anaso
wannan kisha kullum musamman amare,
idan zaki hada kuwa zaki samu sassaken baure
din da 'ya'yansa sai garin dan bashanana, da
gyadar mata kiyi garinsu ki ajiye, sai kuma
kisamu gyada danya me bargo, ki hada da aya
wanda aka soya, sai dabino, ki hada kiyi
garinsu, tofa saiki dauko wancan garin ki hada
kiyita dakashi saiya hade waje daya.