*IDAN AKACE KA ZAUNA A GIDA SABODA ANNOBA, TO KA ZAUNA*
🌴BALLIGU ANNI no. 207🌴 23/03/2020
Aisha Uwar Muminai (RA) tace: "Na tambayi Manzon Allah (s.a.w) gameda *annoba*? Sai ya bani labari cewar; 'Annoba azaba ne da Allah ke aikashi akan wanda Ya ga dama, sai Ya sanyashi rahama ga Muminai.
"Babu wani mutum da zai fada cikin annoba, *YA ZAUNA A GIDANSA* yana mai hakuri da neman lada, yana mai sakankancewar babu abinda zai sameshi sai abinda Allah Ya rubuta masa, face ya samu lada kamar na Shahidi".
📚Bukhari, Hadisi na 3474
📚 Nasa'i, a Sunanul Kubra, Hadisi na 7527
📚 Ahmad, Hadisi na 26139 (Lafazin nasa ne)
(Ma'ana mutum yaji zamansa a gida ba shine zai kareshi ba, Allah ne zai kareshi, amma zamansa idan ta kama shine tawakkali ga Allah. Don haka idan akace a zauna, ka zauna, haka shine koyarwar Musulunci)