Shekaru Biyu Rabona Da Yin Jima'i Da Mijina:
Na kanyi mamaki idan naji wasu matan suna maganar cewa basa samun lokacin zama su tattauna da mazajensu, wasu matan ma cewa suke da zaran mijinsu ya shigo gida, sauran walwala ya kare kenan a gidan daga ita har 'ya'yanta ganin yadda irin wadannan magidanta suke zama abun tsoro a idanunwan iyalansu.
Irin wannan bakar dabi'ar da wasu mazan suke aikatawa, yana matukara cutar da matansu na aure don haka nema wasu matan suke kasa sani da kuma samun dadin dake kunshe cikin rayuwar zaman aure.
Jahilan mazan dai na ganin cewa, sakarwa mace fuska da kuma yi mata fara'a da sakan mata fuska yakan kawo raini, wannan tunanin nasu yana kama da irin tunanin nan ne na wasu matan da suke ganin cewa duk wanda ya rike namiji uba zata mutu ne a maraya.
Babu shakka, duk matan aure data tsinci kanta cikin zaman aure da bata samun lokacin namiji domin gudanar da wata mu'amala na zama a tattauna tare kuma da sakin fiska, tabbas wannan baiwar Allah bata wani bukatar yin doguwar bayani duk wani mai hankalin da zai mata kallo irin na idanuwar basira zai fahimci cewa wannan matar komai darajar gidan mijinta, komai mulkinsa, arzikinsa ko kuma daukakarsa, wannan matar tana cikin matukar kunci na abar tausayawa.
Haka nan kuma a duk lokacin da kikaci karo da matar da take samun lokacin mijinta na zama ya tatattauna da ita, ya nemi shawaranta a manyan mahiman batutuwan da suka shafeta, tabbas da ganinta, ko da talauci da rashin ya mamayeta yana da matukar wahalar gaskeki iya fahimtar hakan ganin yadda irin wadannan matan hankalinsu yake kwance duk kuwa da irin rashihalin rayuwa datake fama dashi a zamanta na aure.
Wannan doguwar shinfidar dana gudanar ya biyo bayan wata kawata da mukayi makarantan sakansare tare ne, kuma mun haura kimanin shekaru 15 bamu hadu da ita ba sai kwanan nan. Duk kuwa da labarin aurenta danake dashi, nasha matukar mamaki yadda na ganta cikin halin tausayi da rashin kuzari, duk kuwa da wani hamshakin mai kudi kuma mai mulki take aure, kai masu karatu a lokacin data shigo gidana ta shigo ne ta masu mata hidima guda shida, ga direbanta wanda ya kawota cikin sabuwar marsandin nan 2016, amma duk da wannan gatan, daraja da daukaka da ake gane mata a zahiri, kawata saida ta gwammace ina ma duk wannan alfarmar da jin dadin zasu kau muddin dai zata samu wata rana mijinta ya zauna yayi hira da ita na tsawon awa guda ko kuma rabin awa.
Da yake daman ina tunanin abunda zan rubutawa masu karatu a wannan watan, bayan munyi doguwar hira da ita na kuma fahimci matsalarta da suka janyo duk kyawunta data ke alfahari da shi a lokacin da muke makaratanta ya gushe, naga ya kamata na kawowa masu karatu wannan hiran danayi da kawata da duk wani abu da mace zata bukata a gidan miji ta samu, amma rashin samun zaman hira da mijinta kawai, ya galabaitar da ita.
http://sirinrikemiji.blogspot.com/2018/07/shekaru-biyu-rabona-da-yin-jima-da.html#.XkQkQShjPto.whatsapp