YADDA AKE SHAFA JIKI NA MUSAMMAN GA MA'AURATA

YADDA AKE SHAFA JIKI NA MUSAMMAN GA MA'AURATA.

Shafa jiki ya na inganta rayuwar Ma'aurata. Domin abu ne da ke isar da soyayya. Rashin sa kuma na kawo kiyayya da nesanta Ma'aurata.

Kowanne mutum ya na da abin da ya fi so. Ka so mafi yawa na mutane su na son a shafi jikinsu. Hada jiki na nuna kauna sosai.

Masana sun gano cewa: Jarirai da ake yawan daukarsu, da rungume su, da sumbatarsu. Sun fi koshin lafiya da walwala arayuwarsu. 

Shafa jiki ko ince hada jiki na sanya soyayya ta dinga tasiri. Ma'aurata mu saki jikinmu mu dinga hutawa tare. Ko za iya say nawa ka kwanta a jikin matarka? To in ba ka yi , sai ka fara. Ga wani kyakkyawan misali.

 Aisha ta ce:" Annabi (SAW) ya na kishingida akan cinyata, Alhali ina haila, sai ya karanta Qur'ani".
(Bukhari ).


*HANYOYIN SHAFA JIKI*
1 - Kwanciya a jikin Miji/ Mata. 

2 - Zama atare waje daya. A tabarma ko a kujera.

3 -Rike hannuwa tare ana tafiya. Ko ya yin da ake rakiya.

4 - Rumguma juna akai-akai. 

5 - Sumbata juna da yawa. 

6 - Tausa na sa warwarewa ta gajiya. Ko kuma sanya jin dadi .

A karshe dai Ma'aurata su karanci bangarori jiki. Su gano wanda ya fi jin sako. Kuma ba lalle in da miji ya fi so. Ya zama shi ne matarsa ke jin sako ba. Sai ka tambayi matarka bangaren jikinta da ta fi so.

Shafa jiki na da muhimmanci sosai. Yakamata ya zama mun saba dashi sosai. Domin tabbatar da kauna a tsakani Ma'aurata.

✍ *Amina Yusuf Gwamna*
Litattafai da aka duba

Kitabu Tayammumi
Kitabul haidha
Mukhtasar Sahihul Bukhari.

Physical touch
The 5 love languages
Gary Chapman

Tasirin Soyayya
Amina Yusuf Gwamna

Post a Comment (0)