*MARABA DA WATAN RAMADAN*
{ 2 }
AZUMI: ibada ce
daga cikin Shika-shikan musulunci guda biyar.
AZUMI: shine barin ci da sha da saduwa da iyali da kuma Barin dukkan abubuwan ci, tun daga 6ullowar alfijir har Zuwa faduwar rana acikin dukkan kwanakin watan Ramadan.
Wannan bayani yana nuna iyakancewar yinin mai azumi tun farkon yinin har qarshensa, wato daga 6ullowar alfijir har zuwa faduwar rana da fuskantowar dare da kuma 6oyuwar kaskon rana acikin shamaki. Wannan shine cikakken lokacin fara azumi da kuma qare sa.
ALLAH (SWT) Yace: "An halatta muku saduwa da iyalinku acikin dararen watan Ramadana, su (iyalanku) sutura ne agare ku kuma sutura ne agare su" .
Har zuwa fadansa (SWT) "kuci kuma Ku sha har sai farin silale ya bayyanar muku daga baqin silale na alfijir, sannan Ku cika azumi zuwa dare".
(Surah ta 2 aya ta 158)
Hadith yazo daga Umar ya tabbatar da iyakancewar lokacin azumi Inda Yace:
Manzon ALLAH (SAW)
Yace: "idan dare ya fuskanto daga nan yini ya bada baya daga can kuma rana ta fadi to lokacin buda baki yayi ga mai Azumi" .
(Bukhary 4/671, Muslim 1100)
•NIYYAR MAI AZUMI:
Niyya ita ce qudurta wani abu a zuciya, wato Mutum yayi qudurin ko wani irin aiki na ibada a zuciyarsa, domin ko wani aikin ibada baya inganta sai da Niyya.
Manzon ALLAH (SAW)
Yace: " dukkan ayyuka basa inganta sai da niyya, kuma ana sakawa kowane Mutum da abunda yayi niyya" .
(Bukhary da Muslim suka ruwaito shi Umar (RA)
YADDA AKE YIN NIYYAR AZUMIN WATAN RAMADAN:
Bayanin malamai ya tabbatar da cewa:
wajibi ne kwana da niyya a axumin farilla na (Ramadan) wato tun kafin 6ullowar alfijir idan an tabbatar da ganin watan Ramadan daga adilan mutane ko shugaba, ko kuma lokacin da kwanakin watan sha'aban suka cika talatin.
A wannan lokaci ya wajaba akan duk musulmi baligi namiji ko mace suyi niyyar azumin watan ramadan cikin dare kafin 6ullowar alfijir.
Kamar Yadda Annabi (SAW) Yace: "Wanda duk bai wayi gari da (Niyyar) azumi ba kafin alfijir to bayi da azumi" .
(Nasa'i 4/196)
Da kuma fadarsa (SAW) cewa: "Wanda bai kwana da niyyar azumi ba tun da dare to babu azuminsa' .
(Tirmizi 730)
Malamai sun ce " Zuciya ita ce wurin niyya, Amma yin furuci da ita bidi'ah ne koda kuwa mutane na ganin yin haka abu ne mai kyau.
Saboda Manzon ALLAH (SAW) da sahabbansa basu ta6a yin furuci da Niyya ba" Domin qarin bayani duba:
(siffatu saumin Nabiy (SAW) shafi na 30)
Zamu chigaba da yardar Allah...
Faridah Bintu Salis
(Bintus-Sunnah)
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
Don kasancewa damu a shafin telegram sai a danna link din dake Qasa👇
https://t.me/miftahul_ilmi
→Ga masu sha'awar Shiga Zauren *MIFTAHUL ILMI* WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248