MARABA DA WATAN RAMADAN 1

*MARABA DA WATAN RAMADAN*

             [1]

KWADAITARWA AKAN AZUMIN WATAN RAMADAN !!!

Haqiqa shari'ar musulunci ta qarfafa kwadaitarwa akan azumtar watan Ramadan tare da bayyana falalarsa da kuma daukakar darajarsa.

Da ace mai Azumi zai kasance yana da zunubai (qanana) kuma ace yawansu ya cika sama da qasa to za a gafarta masa wannan zunubai don Albarkar wannan ibada ta Azumi.

Saboda haka zamu taqaita wannan bayani akan abubuwa guda uku domin Kwadaitarwa akan azumi, kamar haka:

• GAFARTA ZUNUBAI:

Manzon ALLAH (SAW)
Yace:"Dukkan wanda ya azumci watan Ramadan yana mai imani da ALLAH kuma yana mai Neman lada, to an gafarta masa ayyukan da ya gabatar na zunubansa" .

(Bukhary 4/99, Muslim Hadith No.759)
Manzon ALLAH (SAW)
Yace:" Salloli biyar da jumma'a zuwa wata jumma'a da watan Ramadan zuwa Ramadan suna kankare zunuban dake tsakanin su, matuqar an nisanci kaba'ira (manyan zunubai)
(Muslim 233)
• KAR6AR ADDU'A DA 'YANTARWA DAGA WUTA:
Ana kar6ar addu'ar bayi a watan Ramadan cikin ko wani lokaci na watan Ramadan.

Manzon ALLAH (SAW)
Yace:"Lallai Allah (SWT)
yana da bayi abin 'yantawa daga wuta ko wani yini da dare na watan Ramadan, kuma ko wani musulmi da ya roqi ALLAH yana da wata addu'a da idan yayi ana kar6a masa" .

(Ahmad 2/254)
• MAI AZUMI YANA CIKIN MASU GASKIA DA SHAHIDAI:

Wani Mutum yazo wurin Manzon ALLAH (SAW)
sai Yace: Ya Manzon ALLAH shin ko kana ganin idan na shaida babu abun bautawa da gaskia sai ALLAH, kuma na shaida kai Manzon ALLAH ne, kuma nayi salloli biyar na bada zakkah kuma nayi azumin watan Ramadan kuma nayi tsayuwarsa, cikin wani Matsayi nake? Sai Manzon Allah (SAW)
Yace:" cikin masu gaskiya da shahidai)
(Ibn Hibban Hadith No.

19)
WAJABCIN AZUMIN WATAN RAMADAN !!!

•ALLAH (SWT) Ya wajabtawa musulmi axumin watan Ramadan kamar yadda ya wajabtawa al'ummomin da suka gabata.....

(Surah ta 2 aya ta 183)
Amma farkon wajabta azumin watan Ramadan ya kasance akan za6i ne tare da kwadaitarwa akan yinsa, saboda yin azumi abu ne mai wahala ga wadansu sahabbai (RA)
saboda haka sai aka bada za6in cewa wanda bazai yi azumi ba to yayi (Fidya) wato duk ranar da bazai yi azumi ba ya cigar da mabuqaci daya.

• ALLAH (SWT) Yace:" kuma akan wadanda suke yin sa da wahala akwai fansar ciyar da matalauci (miskini),sai dai wanda ya qara alheri, to shine nafi alkhayri agare shi, kuma kuyi azumi da (wahalar)
shine mafi alkhayri agareku idan kun kasance masu sani" .

(Surah ta 2 aya ta 184)
Amma an shafe wannan sauqin saboda ayar data zo bayanta, sahabbai biyu wato Abdullahi dan Umar da Salmatu dan Ak'wa'u (RA) sun bada labarin cewa ayar data zo bayan zuwan wannan aya ta shafeta. Ayar data shafeta farkon itace:

• Fadar ALLAH (SWT):

"Watan Ramadana ne wanda aka sauqar da alqur'ani acikinsa wanda ya kasance mazaunin gida daga cikinku acikin watannan to lallai ya azumce shi" .

(Surah ta 2 aya ta 185)
• Da fadarsa ALLAH (SWT):" Yaku wadanda suka bada gaskiya ga ALLAH da Manzonsa an wajabta azumi akanku kamar yadda aka wajabta ma wadanda me gabanninku, Ko zaku ji tsoron ALLAH?" .

(Surah ta 2 aya ta 183)
Dangane da bayanan da suka gabata na ayoyi da hadithan Manzon ALLAH (SAW) zamu fahimci lallai azumin watan Ramadan wajibi ne akan musulmi maza da mata baligai sai dai idan an samu wani uzuri Wanda shari'a ta yarda da Barin azumin dominsa.

ALLAH Yasa mu dace (Ameen)

Zamu chigaba da yardar Allah...

Faridah Bintu Salis
(Bintus-Sunnah)

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

Don kasancewa damu a shafin telegram sai a danna koren rubutu👇 (link) 

https://t.me/miftahul_ilmi

 →Ga masu sha'awar Shiga Zauren *MIFTAHUL ILMI* WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248

Post a Comment (0)