_*🌙MUSAN AZUMI A' SHARI'ANCE🌙*_(8)
SUNNONIN AZUMI DA LADUBBANSA,
Azumi yana da sunnoni da mustahabbai,
yana daga cikinsu:
1. Sahur:
shi mustahabbi ne a gamuwar malamai, wanda bai yi shi ba ba shi da lafi sai dai wanda ya yi sahur ya fi shi yawan lada. Domin Annabi (S.A.W) ya yi umarni da a yi shi.
Dalili kan haka:
عَنْ أَنَسٍ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ أَنَّ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ
قَالَ: "سَحَّرُوا فَإِنَّ فِي السُّحُورِ بَرَكَةٌ." (رواه البخارى ومسلم).
An karbo daga Anas dan Malik (R.A) ya ce,
Manzon Allah (S.A.W) ya ce:
“Ku yi sahur hakika, akwai albarka a cikin yin sahur.”
(Bukhari da Muslim ne suka rawaito).
2. Gaggauta yin buda baki da jinkirta sahur.
Hujja yazo acikin Hadisi:
لِقَوْلِ النِّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
"لاَ يَزَالُ النَّاسُ بِخَيْرٍ مَا عَجَّلُوا الْفِطْرَ وَأَخّرُوا السُّحُورَ." (رواه البخارى ومسلم)
Don fadin Annabi (S.A.W) da ya ce: “Mutane ba za su gushe suna cikin alheri ba,
muddin suna gaggauta buda baki kuma suna jinkirta sahur.”
(Bukhari da Muslim ne suka rawaito).
3. Yin buda baki da dabino: ga wanda yasamu dama:
لِقَوْلِهِ عَلَيْهِ الصَّلاَةُ وَالسَّلاَمُ: "إِذَا أَفْطَرَ أَحَدُكُمْ فَلْيَفْطِرُ عَلَى تَمْرٍ فَإِنَّهُ بَرَكَةً فَإِنْ لَمْ يَجِدْ تَمْرًا فَالْمَاءُ فَإِنَّهُ طَهُورٌ." (رواه أبو داود والترمذى)
Don fadin Manzon Allah (S.A.W) da ya ce:
“Idan dayanku zai yi buda baki ya yi buda baki da dabino,
idan bai samu dabino ba, ya yi da ruwa,
don tsarki ne ko tsarkakakke ne.”
(Abu Dawud da Tirmizi ne suka rawaito).
4. Addu’a yayin buda baki:
عَنْ عَبْدِ اللهِ ابْنِ عُمَرُو بْنِ الْعَاص:
أَنَّ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: "إِنَّ لِلصَّائِمِ عِنْدَ فِطْرِهِ دَعَوَةٌ مَا تُرَد." (رواه ابن ماجه).
An karbo daga Abdullahi dan Amru dan As (R.A)
ya ce Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Hakika, mai Azumi in ya yi addu’a lokacin buda baki ba a mayar da addu’ar (ana amsawa).”
(Dan Maja ne ya rawaito).
Annabi (S.A.W) ya kasance idan zai yi buda baki yana cewa:
*"اللَّهُمَّ لَكَ صُمْنَا وَعَلَى رِزْقِكَ أَفْطَرْنَا فَتَقَبَّلْ مِنَّا إِنَّكَ أَنْتَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ" (أبو داود)*
Ma’ana: “Ya Ubangiji dominKa muka yi Azumi, kuma da arzikinKa muke buda baki, ka karba daga gare mu, lallai Kai mai ji ne Masani.”
(Abu Dawuda ne ya rawaito).
Da wasu addu'o'in da dama.
5. Asuwaki: An so ga mai Azumi ya yi asuwaki lokacin azuminsa.
Saboda Manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana yin asuwaki lokacin da yake Azumi.
Hakanan yana daga ladubban Azumi a nisanci shaidar zur, karya, giba, rada, tashin hankali, da dai sauran ayyukan sabo.
_*Zamuci gaba insha Allah!!*_
Rubutawa>>✍🏼
*Abubakar Salihu Kabara*
Gabatarwa_
_*USAINI AMFANIMA BABAN AMEENA*_
*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi
Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248