MU SAN AZUMI A SHARI'ANCE 7


_*🌙MUSAN AZUMI A' SHARI'ANCE🌙*_(7)


RUKUNAN AZUMI
Amma rukunan Azumi guda biyu ne:
1. Niyya: 
Azumi ba ya yiwuwa idan babu niyya, 
لِقَوْلِهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: "إنما الأعمال بالنيات" (رواه البخاري ومسلم)

“Dukkanin ayyuka basa yiwuwa sai da niyya.” (Bukhari da Muslim).

Da mutum zai dauki niyyar Azumin watan Ramadan a daren da ake zaton ganin wata ya kwanta bacci da niyyar idan an ga wata zai yi Azumi, idan kuwa ba a gani ba, zai ci gaba da cin abincinsa, sai aka ga wata yana bacci. 

Da gari ya waye, sai ya tashi bai ci abinci ba, bai yi abin da yake bata Azumi ba, sai aka gaya masa jiya yana bacci an ga wata, to wajibi ne ya kame bakinsa, kuma bayan Salla ya rama Azumi daya.

لِقَوْلِهِ عَمَّرُ ابْنِ يَاسِرٍ رَضِيَ الله عَنْهُ: "مَنْ صَامَ الْيَوْمَ الَّذِى يُشَكُّ فِيهِ فَقَدْ عَصَى أَبَا الْقَاسِمُ."

2. Kamewa ga barin ci da sha
Rukuni na biyu daga cikin rukunan Azumi shi ne kamewa ga barin duk wani abinci ko abin sha ko jima’i.

لِقَوْلِهِ تَعَالَى: "وَكُلُوا وَاشْرَبُوا حَتَّى يَتَبَيَّنَ لَكُمُ الْخَيْطِ اْلأَبْيَضِ مِنَ الْخَيْطِ اْلأَسْوَدِ مِنَ الْفَجْرِ ثُمَّ أَتِمُّوا الصِّيَامَ إِلَى اللَّيْلِ." (سورة البقرة: آية 187)
Ma'ana:
“Ku ci ku sha har izuwa ku bambance tsakanin farin zare da bakin zare daga hasken alfijir, sannan ku cika Azumi izuwa dare.” (Suratul Bakara: aya ta 187).

_*Zamuci gaba insha Allah!!*_
Rubutawa>>✍🏼
*Abubakar Salihu Kabara*

Gabatarwa_
_*USAINI AMFANIMA BABAN AMEENA*_

*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi

Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248
Post a Comment (0)