TAMBAYA TA 53

*SHIN MURYAR MACE AL'AURA CE ?*

*Tambaya*

Assalamu alaikum yaa Douktour Allah yaa kyautata muku
Malam shin menene asalin maganar cewa murya mata baligai aura ce, sannan kuma mace za ta iya yin tambaya ki tura karatun alqurâni ta voicemail zuwa ga wani malami don ya duba mata?

*Amsa*

Wa alaikum assalam
A zance mafi inganci muryar mace ba al'aura ba ce, saboda mata da yawa suna yawan zuwa wajan Annabi (SAW) su yi masa tambayoyi a gaban Sahabbansa maza, kuma bai taba cewa su tashi ba don kar su ji muryarsu.
Sahabbai da Tabi'ai da yawa sun dau karatun hadisi daga wajan Nana Aisha ta bayan hijabi, tare da cewa ba Muharramarsu ba ce, in da ace muryar mace al'aura ce da hakan ba ta faru ba.

Halifofin Annabi (SAW) shiryayyu sun kasance suna magana da mata in bukatar hakan ta taso, har sun kan kaiwa wadanda ba Muharramansu ba ziyara, kamar yadda Abubakar da Umar (RA) suka kaiwa Ummu Aiman ziyara, saboda Manzon tsira ya kasance yana kai mata ziyara, kamar yadda Muslim ya rawaito.

A cikin aya ta 32 a suratul Ahzaab Allah ya hana matayan Annabi (SAW) karya murya yayin magana da maza, hakan sai ya nuna yin magana a yanayi madaidaici halal ne .
Don neman karin bayani duba: Alhawy alkabeer 9/648 da kuma Alfuru'u 5/157.

Allah ne mafi sani
*Dr. Jamilu Yusuf Zarewa*

25/04/2020

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248

Post a Comment (0)