"YANA MAI DA NEMAN LADA"
"Wanda ya azumci Ramadhan yana mai imani da neman lada, an gafarta masa abinda ya gabata na zunuban sa" Bukhari.
Imam Khaɗɗabiy R. Yace: Faɗin sa "Don imani da neman lada ma'ana, Ya yi su da niyya da kuma himma shine ya yi azumin abisa gaskata wa (sabida Allah da Manzon sa suka ce ya yi), da kuma kwaɗayi (na lada) kuma zuciyan sa tana mai jin daɗin azumin, ba yana yin azumin a matsayin tilasci agareshi ba ko kuma yana mai ganin wahalan azumin ba ko kuma yana mai ganin tsayin wunin azumin ba (yana cewa kai azumin yau akwai wahala, kai azumin yau wuninsa tayi tsayi da makamantan irin wannan zantukan da suke nuna mita da hancini na mutum), sai dai ya zama yana mai ribatar tsayin wunin (da ibadah) saboda girman ladan dake cikinsa.
-Dariqus-salihin (84)
#Zaurenfisabilillah
Telegram: https://t.me/Fisabilillaaah