ZAMAN GULMAR SHUWAGABANNI DA 'YAN SIYASA

ZAMAN GULMAR SHUWAGABANNI DA 'YAN SIYASA


Tambaya
Assalãmu Alaykum, Yaa Shaykh, menene hukuncin magana akan shugabanni da 'yan siyasa? Shi ma gulma ne ko akwai banbanci idan mutumin yana da nauyin yiwa al'umma shugabanci da hidima? Jazakumullahu Khayran


Amsa
Wa'alaykumussalam, 
To dan'uwa Allah da manzonsa sun haramta cin naman mutane, sannan malamai suna cewa : gulmar shuwagabanni da malamai ta fi tsananin haramci , saboda cin naman shuwagabanni zai jawo ayi musu tarzoma, kamar yadda cin naman malami zai jawo a raina ilimi, saidai akwai wuraren da ya halatta a ci naman mutane saboda maslaha, kamar idan aka zalunci mutum to ya halatta idan zai kai kara ya bayyana zaluncin da aka yi masa, haka nan idan ya ga wani sharri yana so a taimaka masa wajan gusar da shi to ya halatta ya fadi sunan mai laifin, kamar yadda kuma ya hallata ayi gulmar mutumin da ya shahara da aikata sabo da fasikanci, don a guji sharrinsa. Duba Azkar : 489 da kuma Majmu'ul fataawa 28\221 .

A bisa abin da ya gabata za mu fahimci cewa : duk kasar da ake kafa shugaba ta hanyar zabe, to ya hallata mutane su tattauna matsalolin shugaban da yake kai, domin tunanin kawo canji a zabe mai zuwa, musamman idan shugaban ya kasance azzalumi kuma fasiki mai yawan aikata sabo, saidai ya wajaba maganar ta su ta zama gwargwadon bukata.

Allah ne mafi sani.

Amsawa
Dr.JAMILU YUSUF ZAREWA
27-03-2015

Miftahul ilmi 
Facebook ⇨https://www.facebook.com/Miftahulilmi.ml

TELEGRAM ⇨https://t.me/Miftahulilm2

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)