BABU ABINDA ZAI GYARA MU FACE ABINDA YA GYARA NA BAYANMU


*BABU ABUNDA ZE GYARAMU FACE ABUNDA YA GYARA NA BAYANMU*

Assalumu'alaikum, wassalatu wassalamu ala rasulillah

_Bayan haka abunda yasani yin wannan rubutu a daidai wannan dare na 25-09-1441 karfe 12:30 na dare, shine dazu ina zaune a wani waje se nakejin wasu mutane wadanda ba kananan yaraba suna wata fira sunata kama sunayen shugabanni sunata zaginsu suna aibantasu da kokarin suga sun nuna gazawar shugabanni harma suna yabon wasu malamai akan malaman sunyi wa,azozi akan shugabanni wanda shakka babu ni nasan cewa wannan wa'azin ba irin koyarwan Annabi (s.a.w) bane*****_


_`Yan uwa dan girman Allah mutashi muyi karatu domin wallahi wallahi a irin halayenmu ayau ni dakai wallahi tallahi ko sahabin Annabi yadawo duniya ace shine ze shugabancemu wallahi baze iya kawo wani canji ko gyara wanda Buhari ayau be kawoba wallahi ko sahabine yadawo inhar mune ze mulka toh wallahi babu abunda ze iya canzawa. Wani malami ma cewa yayi idan sahabi yadawo duniya a yanzu yaga irin yadda muka lalace toh nantake sahabin ze fadi ya mutu bakin cikinmu ya kasheshi*****_


_Abunda yasa nace ko sahabine yadawo baze iya gyara komaiba shine inka duba littafi Hiqbatun Minat tarikh acan cikin Qissar Sayyidina Aliyu yakawo wata ruwaya inda wani mutum yazo ya samu sayyidina Ali yace masa yakai Aliyu shin meyasane Sayyidina Abubakar da Umar sukayi mulki lafiya lau suka gama amma dakai da Sayyidina Usman sadda kukazo mulki se faman zubarda jini akeyi tunda kukazo mulki ake kashe mutane babu wani cigabanda kuka kawowa musulmai face zubarda jininsu. Se Aliyu yace masa abunda yasa su Abubakar da Umar sukayi mulki lafiya lau saboda su Abubakar da Umar mutanen kirkine kamar yadda ni da Usmanu mutanen kirkine to tunda mu wadanda ake mulka irin yanayinmu daya da masu mulkin shiyasa sukai mulkin lafiya lau suka gama. Amma nida Usmanu sadda mukazo mulki toh mu masu mulkin mune kawai mutanen kirki amma wadanda ake mulka irinkane mutanen banza shine yasa zunubanku sukasa mulkin namu yaki yin kyau****""_

_Kunji abunda sahabin Annabi yafada wato ashe duk yadda shugaba yakaida kirki dazama nagari toh inhar akace mutanenda ze mulka ba bagartattu bane toh za,a hanasu samun alheransa. Kuma kai kasan su wanene suke rayuwa a najeriya idan mutanen kirkine kafini sani inma na banzane duka kafini sani*****_

_Acikin littafin *KAMA TAKUNU YUWALLA ALAIKUM* yakawo ruwaya zuwaga Hasnul Basri yayinda wasu jama'a sukazo suka sameshi sukace Malam kune manya a garinnan amma kuna ganin irin zalunci wanda Hajjaju dan Yusuf yakeyi yana yanka mutane yana zubarda jininsu amma kun zura ido ba zakuyi addu'a ba Allah ya kawar dashi. Se Malam yace musu a irin wannan mugun halin naku ai Hajjaju shine yadace daku kuma sa'a kukayima aka barku dashi hajjajun amma in aka daukeshi toh banda Jaki ko Alade ni banga wanda yafi hajjaju dacewa da shugabantakuba*****_

_Saboda haka ashe idan talakawa suka lalace toh lalacewarsu yakansa a jarrabesu da miyagun shugabanni kokuma inma shugabannin mutanen kirkine toh lalacewar talakawan yakansa Allah ya haramtawa su talakawan samun duk wani alherin shugabannin*****_


_Amma yakamata mugane cewa shifa Allah bawai Ubangijin talakawa bane su kadai Aa harda shugabanni duka Allah shine ubangijinsu, toh Allah ya umarci shugabanni suyi adalci amma sunki suyi adalci. Sukuma talakawa Allah ya umarcesu suyiwa shugaba biyayya koda kuwa shugaban azzalumine Allah ya hukunta cewa ayiwa shugaba biyayya matukar yana sallah kada a zageshi kada aimasa tawaye Amma suma talakawan sunki suyi abunda Allah yace suyi. Kaga anan kenan anyi kunnen doki. Allah ya umarci shugabanni amma sunki subi umarnin Allah sannan suma talakawa suma Allah ya basu umarni amma sunki subi kaga kenan anyi kunnen doki wajen sabama Allah toh kuma talakawan bayan kin bin umarnin Allah toh sun zagi shugaba kuma sunyi gulmarsa kaga anan semuce talakawa sun hada lefuka guda biyu wanda se munje gaban Allah zamuji shin dama dokarsa masu mulki ta shafa kawai banda talakawa kokuwa Aa harda talakawan duk dokar ta shafa???_

_Tuni Malam Abubakar Gumi yagayamana mafita akan wannan halinda muke ciki inda yace Karatun Hadisi da Aiki dashi shine kawai zama lafiya ga musulmi. Toh tsakaninmu da Allah irin yadda muke cin dunduniyar junanmu muke yiwa juna hassada da ganin kyashi da aikata fasadi iri iri dan Allah a wanne hadisi muka samo wadannan? Irin yadda mata suke fita ayau babu kangado dan Allah a wanne hadisi muka samoshi?? Toh ku juya waccan maganar ta Malam Abubakar gumi kuji tunda yace karatun hadisi da aiki dashi. Toh rashin karanta hadisi da rashin aiki da hadisi shikuma mene kenan ga musulmi?????_

_Ibnu Taimiya sadda shugaban tatar ya fitini musulmai kuma shi Ibnu Taimiya yana ganin dole seyayiwa wannan shugaban wa'azi, shin tsakaninku da Allah mimbari yahau yana zagin shugaban kokuwa gaba da gaba yaje??? Yanzu kaida kake cilloma shugaba nasiha daga kan mimbari shin tsakaninka da Allah sunnar wane kakebi????_


_Idan kace bakada ikon ganin Buhari toh ai kanada ikon ganin Isa Ali fantami toh meyasa bazakaba shi Fantami sakonba ya isarwa Buharin??? Idan El-Rufa'i shine yaimaka wahalar gani ashe bazaka iya ganin Khamis Almisry ba? Meyasa su bazaka basu sakon su isarba sekace larurace tasa kayi watsi da hadisan Annabi wai da sunan kana gyara 6arna? Shib Haka Ahmad binu Hambal yayiwa shugabannin zamaninsa? Kokuwa kai taka sunnar ba irin tasu bane kokuwa Aa su su Ibnu Taimiya dasu Imam Ahmad sune basu fahimci sunnah ba kaine ayau ka fahimta???_


✍🏼
```Jameel A Kabo```
_*(ABU ZULAIHAT)*_
Post a Comment (0)