LAILATUL QADRI 3

🌺 *LAILATUL QADR 3* 🌺

ACIKIN WANE DARE AKAFI TSAMMANIN LAILATUL QADR?
 
🔷 Jumhurin malamai sun tafi akan cewa lailatul qadr tana nan acikin wadannan darurruka goma na karshen wannan wata masu albarka, to amma sunyi sabani akan cewa acikin wane darene akafi tsammanin wannan dare acikin wadannan darurruka. 
   ðŸ”¸ An hakaito daga Hassanul basri da malik cewa lailatul qadr ana Neman ta ne acikin duka darurruka goman ne na karshen watan, witirinsa dama wanda ba witirinba. Sukace saboda hadisin da manzon Allah yake cewa "ku nemeta a taran karshen da suka rage da kuma bakwai din karshen da kuma biyar din karshe da suka rage", wannan hadisin idan mun daukeshi akan cikar wata kwana 30, to duka kwanakin bazasu fada cikin witiriba, idan kuma mun barshi akan duk yadda wata takasance ne to ai wannan gaibune bazamu saniba kafin watan ta kareba. Dan haka idan watan ta kasance cikakkiya to dararen zasu kasance wadanda ba witiriba, idan kuma bai cikaba to zasu kasance witiri, saboda haka yana wajaba kara kokari wurin nemanta aduka darurrukan witirinsu da wanda ba witirinsuba.
🔹 Sauran mafiya yawan malaman kuma sun tafi akan anfi tsammanin wannan darene acikin witirin wadannan dararraki. 
   Sai kuma wadannan maluman sukayi sabani akan to wane witirin darene akafi tsammanin ta?? 
▪ Wasu sukace acikin daren ashirin da daya, wannan kuma shine zance shahararre awurin shafi'iya, saboda hadisin Abi saeed. (Mun ambaceshi abaya).
Sannan kuma an ruwaito daga Sahabi Ibnu masud da Aliyu Allah ya kara musu yarda sunce "Ana Neman lailatul qadr ne adaren ashirin da daya da daren ashirin da uku".
▪Wasu malaman kuma sukace anfi tsammanin ta adaren ashirin da uku, wannan kuma shine maganan mutanen madina, har mutanen madina na kiran wannan daren da *lailatul juhaniyyi* (wato Abdullah bin Unais Aljuhani, suna jingina wannan darene gareshi saboda manzon Allah ya umarceshi ta ya sallaceta).
   Sannan kuma yazo ahadisi manzon Allah yace "An nunamin cewa asafiyar wannan dare ta lailatul qadr zanyi sujjada (Sallar Asubah) acikin ruwa da tabo Sai kuma gashi manzon Allah ya koma gida daga Sallar Asubah ranan ashirin da uku agoshinsa akwai ruwa da tabo.
▪ Wasu kuma suna ganin anfi tsammanin ta adaren ashirin da bakwai, wannan shine zancen mutanen kufa, kuma shine ra'ayin Sahabi Ubayyu bin ka'ab har ya kasance yana rantsuwa akan cewa itace daren lailatul qadr.
 Qanan bin Abdillah yace na tambayi zirru gameda lailatul qadr sai yace "Umar bin khaddab, huzaifatul yamani da kuma Anas dukansu sahabban manzon Allah ne sun kasance basa kokonto akan cewa tana daren ashirin bakwai". 
Sannan suna kara hujja da hadisin Ibnu Abbas yake cewa wani mutum yazo wurin manzon Allah Ni dattijone Babba kuma banida lafiya tsayuwa yana bani wahala, dan haka ka umarceni da wani dare zan tsaya acikinsa wanda akesa ran itace lailatul qadr sai manzon Allah yace masa "ka tsaya adaren ashirin da bakwai". Dabrani 11836.

#zaurenfisabilillah
https://t.me/Fisabilillaaah

Post a Comment (0)