MATSAYIN ZAKKA A SHARI'ANCE 18


_*⚖️MATSAYIN ZAKKA A' SHARI'ANCE⚖️*_(18)

*_ZAKKAR GIDAJE DA ABUBUWAN HAWA:_*

 Ya kamata mu sani cewa gidaje da abubuwan hawa iri biyu ne: 

Akwai na amfanin kai,
su wadannan babu maganar Zakka a kan su.

Akwai kuma wadanda ake yin haya da su,
to su ne muke magana a kan su. Sun hada da motoci, da babura, da jiragai (na sama da na ruwa Dana kasa).

Injinan masana’antu da duk wata dukiya da ake samun amfani daga gare ta.

 Ra’ayin malamai ya kasu biyu, dangane da Zakkar irin wadannan dukiyoyi:
 Akwai masu cewa za a shigar da su ne cikin tsarin zakkar kayan sayarwa. Watau ma’ana, duk wanda yake da gidajen haya, ko motoci, ko babura, ko injin kamfani,
sai ya yi masa Kima,

 idan shekara ta cika ya hada da abin da yake hannunsa ya fitar da daya bisa arba’in.
Watau ‘rubu’in ushri’.

 Daga cikin masu wannan fahimtar akwai,
Ibn AKil na Hambaliyya, da Ibnul Kayyim da shi kansa Imam Ahmad.

 Maganar ba ta tsaya a mazahabar Hambaliyya ba, 
shi ma Imamu Malik fahintarsa ke nan. Kamar yadda ibnu Rushudi ya fada a cikin littafinsa ‘‘Bidayatul Mujtahid”
(Duba FiKhuz-Zakat juz’i na 1, sh:na 466 – 469).

 Akwai kuma masu cewa bai kamata a shigar da su cikin tsarin Zakka kayan sayarwa ba.
Saboda idan aka yi haka an daidaita kayan haya da kayan sayarwa, alhali kuwa ba daya su ke ba. 

Su kadarorin haya cin albarkar amfanin su ake yi. Su kuwa kayan sayarwa su kansu ake sayarwa a ci kudinsu.

Don haka, masu wannan fahintar sai suka ce, maimakon a fitar da Zakkar daga Kimar kadarorin sai kawai a fitar daga abin da aka samu daga gare su.

Game da wannan har yau, sai fahintar malaman mahzahabar Malikiyya ta kasu biyu:
masu cewa a fitar daga kudin kadarar, bayan sun shekara, da masu cewa a fitar daga amfanin da aka samu daga kadarar a take.

Amma fa kowannensu yana cewa ne a fitar da ‘rubu’in ushri’.
Watau a kasa arba’in a fitar da daya. Watau dai a bi tsarin Zakkar kudi.

 Ra’ayin na uku ya haifu a KarKashin wannan ra’ayi na biyu.

masu wannan ra’ayi sun goyi bayan a fitar da Zakkar daga amfanin kadarorin, sai dai ‘Ushuri’ za a fitar ko ‘rubu’in Ushuri’.
Watau daya daga kaso goma, ko daya daga ashirin.

Masu wannan ra’ayi sun hada da Dr. Yusuful Kardawi da malamansa:
Irin su Sheikh Muhammad Abu Zahra, Sheikh Abdul Wahab Khallaf, da Sheikh Abdur-Rahman Hasan, su suna ganin maimakon a fitar a kan tsarin Zakkar kudi ya fi kyau a fitar a tsarin Zakkar amfanin gona.

 Domin su ma amfani ne.
Watau an hada amfanin gona da amfanin kadarorin haya. Sai dai sun ce za a rage abin da ya kan ragu na Kimar su duk shekara.

(Duba FiKh Zakat juz’I na 1, sh: 470 – 482)

_*Zamuci gaba insha Allah!!*_
Rubutawa>>✍🏼
*Abubakar Salihu Kabara*

Gabatarwa_
_*ALHUSEIN ABBAN SUMAYYA*_

*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi

Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248
Post a Comment (0)